Warware Labarin Bogi Da CDD ta Aiwatar na daga 8 Yuni zuwa 14 Ga Watan Yuni Shekara na 2020

Shahararren Dan Wasan Kwaikwayo Olu Jacobs Bai Mutu Ba

Tushen Magana:

A ranar 10 ga watan Yunin shekara ta 2020 majiyoyi da yawa na yanar gizo sun bada labarin cewa shahararren dan wasan kwaikwayo nan na Nollywood mai suna Olu Jacobs ya rasu bayan gajeriayar rashin lafiya. Labaran yaja hanakalin mutane matuka gaya a dandalin Facebook da Twitter a wannan rana.

Har wayau wani shafin yanar gizo ya wallafa labarin da aka yadashi sosai a dandalin Facebook.

Gaskiya Magana:

Dan was an kwaikwayon, Olu Jacobs yananan a raye. Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa jita-jitar mutuwar dan was an ta samo asali ne daga shafin Nairaland ta wani labari da suka wallafa wanda suka goge daga baya.

Dan was an kwaikwayon mai shekaru 78 wanda ya taka rawa a finafinan kasar nan dama na kasashen duniya yana auren Joke Silva ne.

A lokacin da take karyata labarin, Joke tace mijinta yana nan a raye inda ta kara da cewa, “abin ya dagawa iyalan Olu Jacobs hankali wannan yasa dole muyi magana”. Domin Karin bayani latsa nan  https://www.cddwestafrica.org/shahararren-dan-wasan-kwaikwayo-olu-jacobs-bai-mutu-ba/

Shin Gwamnatin Tarayya Tana Bada Tallafin Naira 30,000 Ga Yan Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 14 ga watan Yunin shekara ta 2020 Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD ta gano wani sakon da ake yadawa a manhajar WhatsApp dake ikirarin cewa gwamnatin tarayya raba tallafin naira dubu talatin (N30,000) ga dukkan yan Najeriya a matsayin agajin rage radadin annobar cutar Corona.

Sakon yayi ikirarin cewa naira dubu talatin din tallafi ne dan ragewa yan Najeriya radadin annobar da cutar Corona ta haifar kuma mutane zasu tallafin kudin ne daga lokacin da suka cika wani fom da aka samar a yanar gizo.

Gaskiyar Magana:

Kamar ire-iren wadannan hanyoyin da yan danfara yaudaran mutane cewa gwamnati zata bada tallafi da suka gudana a baya, wannan ma daya ne daga cikin dinbi labarun bogi da yan danfara ke yadawa dan cutar mutane.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa wadanda suka kirkiri sakon sunyi ne da nufin tara bayanai masu muhimmanci kamar su lambar asusun ajiya na banki da sauran bayanai dan zambatan jama’a. Domin Karin bayani latsa nan https://www.cddwestafrica.org/shin-gwamnatin-tarayya-tana-bada-tallafin-naira-30000-ga-yan-najeriya/

Leave a Comment

Your email address will not be published.