Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

Wani Takaitaccen Video Da Akayi Ta Yadawa a Shafin Sada Zumunta Na Twitter Da Ake Cigaba Da Yadawa a Shafukan WhatsApp da Facebook Yace Jirgin Saman Pasinja Na Air Peace Ya Dakko Wani Pasinja Mai Dauke Da Cutar Coronavirus Zuwa Kano Daga Lagos.

Kamar Yadda Wannan Video Ya Bayyana, Jim Kadan  Da Tsayawar Jirgin, Matukin Jirgin Yaki Bude Jirgin Dan Pasinjan Da Ya Dakko Daga Lagos Su Sauka Saboda Fargabar Da Yake Da Ita Game Da Mai Dauke Da Kwayar Cutar Coronavirus.

CDD Tayi Binciken Kwakwaf Dan Tantance Gaskiyar Wannan Jita-Jita Kuma Ta Gano Cewa Jim Kadan Da Tashin Jirgin a Lagos Wani Pasinja Mai Shekaru Goma Sha Bakwai Wanda Kuma Hawan Sa Jirgi Na Farko Kenan Yayi Amai.

Binciken CDD Ya Gano Cewa Ayarin Kwararrun Likitoci Sun Gwada Wannan Saurayi Da Yayi Amai A Lokacin Tashin Jirgin. Likitocin Filin Jirgin Sama Sun Bayyana Cewa Matashin Yayi Aman Ne Sakamakon Jijjiga Da Tsoro Yake Haifar Da Ita Da Ake Kira Motion Sicknesss A Turance. Binciken Likitocin Ya Kara Tabbatar Da Cewa Matshin Baya Dauke Da Alamomin Cutar Coronavirus.

Tuni Jirgin Ya Sauka Kuma Pasinjoji Suka Tafi Inda Zasu Je. Har Wayau Binciken CDD ya tabbatar Da Cewa Matashin Baya Dauke Da Cutar Coronavirus.

Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.