Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar: Ba a Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya Ba

Tushen Magana:

A ranar 7 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da ya janyo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafin Twitter. Labarin ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kebe a mataimakin Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya DIG Moses Jitoboh dan shekaru 52 a gefe guda inda ya nada Usman Alkali Baba dan shekaru 57 a matsayin sabon Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya.

Labarin ya kara da cewa DIG Jitoboh yana gaba da Usman Alkali a matsayi kuma an nada Alkalin ne dan tabbatar da cewa Musulmi kuma dan arewacin Najeriya ne ya hau mukamin Sipeta Janar din.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa DIG Moses Jitoboh baya gaban DIG Usman Alkali a mukami.

Binciken CDD din ya kara gano cewa Usman Alkali Baba wadda yanzu shine sabon Sipeta Janar din Yan Sandan Najeriya ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar ra 1988 yayin DIG Jitoboh ya fara aikin dan sanda a 1994.

A kwanan baya ne DIG Jitoboh ya samu mukamin mataimakin Sipeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya.

Da yake maida martani kan batun, mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya ce labarin da ake yadawa cewa an yiwa DIG Jitoboh ritaya da aiki labari ne na karya.

Har wayau da yake yiwa CDD Karin bayani, mai magana da yawun hukumar kula da ayyukan yan sanda, Ikechukwu Ani yace har zuwa ranar 9 ga watan Afirilun da muke cikin DIG Jitoboh yana na baki aiki.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewa labarin da ake yadawa cewa DIG Moses Jitoboh yafi Usman Alkali wadda yanzu ya zama Sipeta Janar din Yan Sanda karya ne. Har wayau labarin da ke cewa Usman Alkali yana kasan DIG Jitoboh ne aka dakko shi aka nada shi mukamin Sipeta Janar karya ne.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa