Shin Gwamnatin Tarayya Ta Bada Biliyan Dari Ga Kungiyar Miyetti Allah Da Nufin Magance Kashe-Kashe Da Garkuwa Da Mutane?

Gaskiyar Magana: Karya Ne! Tushen Magana: A ranar Ladi, 24 ga watan Janairun shekara ta 2021, an yada wani bidiyo a shafin Twitter wadda ya janyo cece-kuce da tofa albarkacin baki daga mutane da yawa, bidiyon yayi zargin cewa gwamnatin tarayya bada kudi har naira miliyan dubu dari ga kungiyar Fulani makiyaya ta “Miyetti Allah” …