Skip to main content
Tag

Fact Check Hausa - Centre for Democracy & Development

Labaran Karya da CDD ta Gano a Karshen Satin 21 ga Watan Febrairu Shekara na 2021

By Fact Check

Labarin bogi ko labarin karya labari ne da ba’a tantance shi ba. Yakan iya zama labari da aka buga wanda ba abi ka’idar da ya kamata a bi ba wajen wallafa labarin kuma a ka yada shi a kafafen yada labarai.

A wannan satin CDD ta gano wasu labarai dake yawo a kafafen yada labari wanda suka hada da tallafin daga gidauniyar Dangote da kuma wani shafi a manhajar twitter da ke alakanta kansa da ma’aikatar matasa da wasanni ta tarayya.

A ranar Talata, 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa Gidauniya Aliko Dangote na bada tallafi dan fara sana’o’i ga ‘yan Najeriya da suka cancanta.

Sakon yace: “Ku gaggauta dubawa dan sanin ko kun cancanta da samun tallafin kudi daga tsarin bada tallafi na Gidauniyar Dangote na shekara ta 2021”

Binciken da CDD ta gudanar game da ikirarin tallafi daga Gidauniyar Dangoten ya gano cewa sakon da ake yadawa din sakon karya ne.

Adireshin yanar gizon da aka bayar dan yi rijista, adireshi ne na bogi. Haka zalika, hoton da aka lika a jikin sakon babu shi a adireshin yanar gizon da aka bayar dan yin rijistar, hakan  wani sabon salo ne na jan hankali da yaudaran mutane tare da zambatar su. Kuna iya karanta cikakiyar bayani a nan

A ranar 17 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, ayarin wasu yan kishin kasa sun janyo hankalin masu tantance sahihancin labarai da bankado labaran bogi na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) game da wani shafin Twitter mai lakabin “Nigerian Youth Investment Fund” (NYIF_NGR) da ke ikirarin cewa shi wani tsari ne na bada tallafi ga sana’o’in matasa da gwamnatin tarayyara Najeriya ke goyon baya.

Masu lura da shafin sunyi kira ga wadan da ke bukatar tallafin fara sana’a su biya wasu kudade kafin samun tallafin.

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa ma’aikatar matasa da bunkasa harkokin wasannin ba ta umarci masu neman kowane irin tallafi su biya kudi ba, dan haka da’awar @NYIF_NGR cewa a biya kudi karya ne.

Tsarin tallafawa matasa da jari da ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni ta fito dashi ya kammala shirin somin-tabi a watan Yuli na shekarar da ta gabata inda mutane 239 suka amfana da N165,700,000.

Shafin gaskiya na Twitter da ke bada bayanai game da harkokin matasa na gwamnatin tarayya shine @NYIF_NG. Domin karanta cikkayar labarin latsa nan

Wasu daga ciki labaran bogi da CDD suka wallafa

Shin Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Yin Rijistar NIN Ta Hanyar Yanar Gizo?

Bill Gates Bai Ce Za’a “Sake Samun Wata Annoba Bayan Cutar Korona Ba”

Gwamnatin Jahar Kano Ba Ta Rushe Makarantar Sheikh Abduljabbar Ba!

Shin WHO Dakatar Da Najeriya Daga Neman Maganin Rigakafin Cutar Korona?

DOMIN SAUKE MUJALLAR MU, LATSA NAN

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Babu Wani Tsarin Bada Tallafi Daga Gidauniyar Dangote

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Talata, 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa Gidauniya Aliko Dangote na bada tallafi dan fara sana’o’i gay an Najeriya da suka cancanta.

Sakon yace: “Ku gaggauta dubawa dan sanin ko kun cancanta da samun tallafin kudi daga tsarin bada tallafi na Gidauniyar Dangote na shekara ta 2021”

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar game da ikirarin tallafi daga Gidauniyar Dangoten ya gani cewa sakon da ake yadawa din sakon karya ne.

Adireshin yanar gizon da aka bayar dan yi rijista adireshi ne na bogi.

Hoton da aka lika a jikin sakon babu shi a adireshin yanar gizon da aka bayar dan yin rijistar, hakan kuma wani sabon salo ne na jan hankali da yaudaran mutane tare da zambatar su.

Karin binciken da CDD ta gudanar game da hotunan da biye da sakon ya gano cewa hotuna ne da aka dauka lokacin da Ministar Jinkai da Bada Dauki ga Jama’a, Sadaiyya Farouk take bada tallafin kudi ga yan Najeriya a watannin baya.

Hotunan an dauke su ne a yankin Kwale da ke kewayen babban birinin tarayya Abuja yayin raba kudi dan rage radadin zaman gida da fatattakar cutar Korona a watan Afirilun 2020.

Yayin rijistar ana bukatar masu neman tallafin su bada bayanan asusun su na banki, da lambar BVN, wannan kuma wata hanya ce day an damfara ke amfani da ita dan zambatan jama’a.

Wani sabon salo da wannan sakon bogi ke dauke dashi shine dokoki da ka’idoji day an damfarar suka tsara.

Nazarin da CDD ta aiwatar a shafin Gidauniyar Aliko Dangote dama shafin yanar gizon kamfanin nasa sun gano cewa sakon yanar gizon da aka yada game da su ba gaskiya bane.

Kawo lokacin hada wannan rahoto tallafin da Gidauniyar Dangote ke bayar shine ga mata da matasa kuma bayanan da muka samu sun nuna cewa Gidauniyar ta kammal raba kusan miliyan dubu hudu a jahohi sha daya, kuma wannan rabo zai cigaba a sauran jahohin Najeriya.

Kammalawa:

Wani sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke cewa Gidauniyar Aliko Dangote na bada tallafin kudi ga yan Najeriya masu sa’a dan fara sana’o’i a shekara ta 2021 sako ne na bogi. Yan damfara kan tsara ire-iren wadan nan sakonni da nufin tattara bayanan mutane dan zambatan su a karshe.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shafin Twitter Na Bogi Da Ke Alakanta Kansa Da Ma’aikatar Matasa Da Wasanni Ta Tarayya

By Fact Check, Uncategorized

Tushen Magana:

A ranar 17 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, ayarin wasu yan kishin kasa sun janyo hankalin masu tantance sahihancin labarai da bankado labaran bogi na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) game da wani shafin Twitter mai lakabin “Nigerian Youth Investment Fund” (NYIF_NGR) da ke ikirarin cewa shi wani tsari ne na bada tallafi ga sana’o’in matasa da gwamnatin tarayyara Najeriya ke goyon baya.

Masu lura da shafin sunyi kira ga wadan da ke bukatar tallafin fara sana’a su biya wasu kudade kafin samun tallafin.

Gaskiyar Magana:

Shafin Twitter wadda ake kira @NYIF_NGR shafi ne na bogi kuma bashi da alaka da ma’aikatar matasa da harkokin wasanni.

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa ma’aikatar matasa da bunkasa harkokin wasannin ba ta umarci masu neman kowane irin tallafi su biya kudi ba, dan haka da’awar @NYIF_NGR cewa a biya kudi karya ne.

Tsarin tallafawa matasa da jari da ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni ta fito dashi ya kammala shirin somin-tabi a watan Yuli na shekarar da ta gabata inda mutane 239 suka amfana da N165,700,000.

Har wayau, CDD ta tuntubi mai taimakawa Ministan Matasa da Wasanni akan harkokin fasaha Areola Oluwakemi wanda ya bayyana cewa shafin Twitter din da ke neman mutane su biya kudi dan bas u tallafi shafi ne na bogi.

Oluwakemi ya kara da cewa: “wanda suka mallaki shafin kuma suke gudanar dashi na damfarar matasan Najeriya ne kawai”

Kammalawa:

Shafin Twitter wadda ake kira @NYIF_NGR shafi ne na bogi kuma bashi da alaka da ma’aikatar matasa da harkokin wasanni.

Shafin gaskiya na Twitter da ke bada bayanai game da harkokin matasa na gwamnatin tarayya shine @NYIF_NG.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Yin Rijistar NIN Ta Hanyar Yanar Gizo?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar bunakasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) wani jawabi da wani shafin yanar gizo ya wallafa da ke cewa gwamnatin tarayya ta amince da yin rijistar lambar bayanan mutum da a turance ake kira “National Identity Number (NIN)” ta hanyar yanar gizo.

Karin bayani da shafin yanar gizon ya samar sunyi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakin ne sakamakon wa’adin da aka baiwa dukkan masu layin waya suyi rijistar su kafin ranar 1 ga wtaan Afirilu ko kuma a dakatar da layin nasu daga yin amfani.

Shafin yanar gizon ya kara da cewa adadin yan Najeriya 117,836 ne suka yi rijistar kuma suka samu aka hada musu lambar NIN din su da layukan wayyoyin su.

Gaskiyar Magana:

Binciken CDD ya gano cewa shafin yanar gizo shafi ne da aka kirkire shi dan tattara bayanan jama’a kuma bashi takarda shaidar SSL, wanda kuma alama ce da ke nuna rashin amincin sa.

Har wayau hukumar yiwa yan kasa katin kasancewa yan kasa ta barranta kanta da wannan shiri a wani tsokaci da tayi ta shainta na Twitter (@nimc_ng).

Hukumar da ke yin katin dan kasar NIMC ta ce shafin yanar gizon na yan damfara ne, dan haka bashi da alaka da ita.

NIMC ta gargadi jama’a dan su guji wasa ko bada bayanan su ga duk wadan da basu aminta da su bad an gujewa fadawa hannun bata-gari.

Kammalwa:

Wani bayani da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya ta amince da rijistar “NIN” ta hanyar yanar gizo karya ne, dan haka jama’a a kiyaye.

Shafin yanar gizon da ke ikirarin cewa ana rijistar NIN din ta hanyar yanar gizo shafi ne na bogi.

CDD na jan hankalin jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Bill Gates Bai Ce Za’a “Sake Samun Wata Annoba Bayan Cutar Korona Ba”

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: An Jirkita Labarin.

Tushen Magana:

A ranar Talata, 9 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani jigon labari zauren YouTube mallakin MSNBC ya wallafa wadda kuma aka yada shi a zaurukan WhatsApp tare da janyo cece-kuce sakamakon tattaunawa mai yawa da mutane suka yi akansa. Jigon labarin ikirarin cewa Bill Gates yace: “wata annoba na nan tafe bayan cutar Korona”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa Bill Gates bai ce za wata annoba na nan tafe ba, amma abinda yayi shine gargadi ga dokacin duniya cewa ta shirya saboda fuskantar wata annoba.

Bill Gates yana magana ne yayin martanin sa game da annobar da ake ciki inda yace:

“sai mun dauki matakai guda biyu a lokaci guda, kawo karshen wannan annoba taka-maimai ta hanyar samar da magani mai yawa da zai ishi dukkan duniya, sannan mu tabbatar da cewa mun shirya dan za a sake samun wata annobar”

Amma jigon labarin da MSNBC suka wallafa sai ya nuna cewa Bill Gates ya bayyana cewa za a sake samun wata annoba ne ana gama cutar Korona.

Kodayake sanannen abu ne cewa ana iya fuskantar wata annobaa kodayaushe, amma ba’a san cewa ko ana fita daga wannan annoba ta Korona bane, kuma Bill Gates a bayanan sa bai zaiyana haka ba.

Mr. Gates yana daya daga cikin mutane kadan da ke hankoro da rajin ganin an samu maganin cutar Korona. Matsayin sa akan nemo maganin cutar Korona ya haifar da cece-kuce ta fuskoki daban-daban a duniya da suka hada malaman addini. Angina cece-kuce da yawa da maganganu marasa tushe akan Mr. Gates da suka da abinda wasu ke cewa yana da manufar rage adadin mutanen duniya.

Kammalawa:

Jigon labarin da MSNBC suka wallafa yana dauke da rikitarwa tare da rudani.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai kan gabatar da rahotanni da labarai yadda suka fito daga inda aka samo su ba tare da jirkita sakon da suke dauke dashi ba.

CDD har wayau na jan kafafen yada labarai da su guji jina jigon labari mai dauke da rudani dan jan hankalin jama’a. Akwai bukatar mutane kuma su rika karanta gundarin labari ba kawai jigon sa ba.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Gwamnatin Jahar Kano Ba Ta Rushe Makarantar Sheikh Abduljabbar Ba!

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da BBC Hausa sunka wallafa cewa gwamnatin Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Wasu kafafen yada labarai da yawa tare da tashoshin kallo na dandalin YouTube duk wallafa wannan labari. Majiyoyin sun hada da: Express Radio Kano, Legit Hausa, Kadaura 24, tashoshin YouTube da suka buga labarin sun hada da: 9ja Hausa TV, Action Hausa TV, Alheri Royal TV, Kundin Labarai TV, Komai Da Ruwan Ka TV 1

Labarin yayi ikirarin cewa daukar hukuncin rushe makarantar malamin ya biyo bayan hana shi wa’azi da gwamnatin tayi ne sakamakon cece-kucen da maganganu sa suka janyo a tsakanin Musulmai tare da yin maganganu na batanci ga Musulunci.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa gwamnatin jahar Kano ba ta rushe makarantar malamin ba kamar yadda labarai da dama da kafafen yada labarai suka wallafa suka bayyana.

Ziyarar gani da ido da wakilin CDD yakai inda makaranta da gidan malamin suke ta gano cewa babu abinda ya samu maranta ko masallacin malamin. Dan haka labarin cewa an rushe makarantar malamin karya ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano gine-ginen da aka rushen din suna tazarar akalla mita dari biyu da makaranta da masallacin malamin.

Gine-ginen da aka rushen din sun kunshi gidaje ne da sauran muhallai da mutane daban-daban suka gina wanda a cewar hukumar kula da tsara gine-gine ta jahar Kano (KNUPDA) tace ba a yisu akan ka’ida ba.

Anga yan sanda cikin shiri a motoci na zagaye da gidan malamin yayin da yara ke ci gaba da wasa cikin baraguzan rusau din da aka yi a filin da ke da tazara daga gidan malamin.

Da yake magana da wakilin CDD, darakta mai kula tsara birane na hukumar KNUPDA, Rilwanu Baita y ace labarin cewa an rushe makarantar Abduljabbar labari ne bogi.

Baita ya kara da cewa KNUPDA ba ta rushe makaranta ko wata kadara ta malamin ba, hasalima abinda ya faru shine rushe gine-gine da aka yisu ba bisa ka’ida ba a wani waje da ake kira Filin Mushe.

Baita yace: “KNUPDA ta gano wasu gine-gine da wasu mutane suka yi a Filin Mushe da ke karamar hukumar Gwale, dan haka sai ta aikawa wadan da suka yi gargadin karya ka’ida da suka yi tun watannin baya amma sai suka yi watsi da sanarwar, saboda haka KNUPDA ta rushe su sakamakon saba ka’ida da kuma kunnen uwar shegu da sanarwar da aka baiwa mutane cewa su dakatar da gine-gine”

“duk mutane da suka yi gine-gine a wannan waje basu takardun izini, kuma doka ta bamu ikon ruguje duk wani gini da aka yishi ba bisa ka’ida ba”

“ina kara jaddada cewa ba makaranta KNUPDA ta rushe ba face gine-gine da aka yisu cikin rashin izini”

Kammalawa:

Labarin da kafafen da yada labarai da yawa suka wallafa cewa gwamnatin jahar Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar karya ne.

Ziyarar da CDD takai wurin da akayi rusau din da karin binciken da ta gudanar ya gano babu abinda ya samu makaranta ko masallacin malamin.

CDD na tabbatar da cewa wannan labari ne na bogi dan haka jama’a suyi watsi dashi.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin WHO Dakatar Da Najeriya Daga Neman Maganin Rigakafin Cutar Korona?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tuhen Magana:

A ranar 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2021 jardar Punch ta wallafa wani labari a shafin ta na yanar gizo mai taken: “hukumar lafiya WHO ta dakatar da Najeriya da sauran wasu kasashe takwas daga yunkurin sun a nemo maganin cutar Korona”

Labarin yayi ikirarin cewa wani bangare na WHO da aka yiwa lakabi da COVAX ya dakatar da Najeriya da wasu kasashe daga neman maganin cutar Korona daga neman maganin daga kamfanin hada magunguna da Pfizer.

Labarin yace Najeirya ta gaza cika ka’idojin samun maganin wanda suka hada da tabbatar samar muhallin ajiye maganin a ma’aunin yanayi na “70 degrees Celsius”.

Gaskiyar Magana:

Labarin da jaridar Punch ta wallafa wanda yayi ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta dakatar da Najeriya da sauran wasu kasashe takwas daga neman maganin cutar Korona karya ne.

Wakilin WHO a Najeriya Dr. W. Kazadi Mulombo, yace “WHO ta aminta da maganin Covax kuma ba zata dakatar da kowace kasa ko mamba daga samun maganin da aka aminta dashi ba”, wakilin ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter mai lakabin @WMulombo.

Mulombo ya bukaci manema labarai da kafafen yada labarai na Najeriya da sauran kasashen duniya da guji yada labaran bogi da suka shafi cutar Korona.

A wani taron manema labarai da WHO da hukumar lafiya matakin farko suka shirya, Dr. Kazadio ya ce hukumar lafiya ta WHO bata dakatar da kowace kasa a nahiyar Afirka daga neman maganin cutar Korona ta hanyar COVAX, hasali ma WHO na goyon bayan dukkan kasashen dan nemo maganin cutar cikin gaggawa”.

Ya kara da cewa, banda maganin “AstraZeneca”, akwai wani karancin maganin cutar da kamfanin Pfizer ke samarwar ta hanyar COVAX.

“Kaow ranar 18 ga watan Janairun da muke ciki, akwai bukata daga kasashe 13 , hakanan wani kwamiti mai wakilcin ma’aikatu da hukumomi da yawa ya yi nazari akan bukatun maganin guda tara wadda acikin su akwai Najeriya, kamfanin Pfizer zai aika maganin gare su sannu a hankali”, inji Mulombo.

Har wayau, nazarin da CDD ta gudanar game da taron manema labaran da Dr Matshidiso Moeti ya jagoranta wanda kuma taron ne jaridar Punch da sauran kafafen yada labarai suka dogara dashi waje cewa an dagatar da Najeriya daga neman maganin cutar Korona din ya gano cewa WHO bata dakatar da Najeriya ba.

Dr Matshidiso Moeti ta kara da cewa: “nan bada dadewa ba za a fara rukunin farko na maganin rigakafin cutar nahiyar Afirka. Akalla digon maganain rigakafin cutar miliyan 90 ne na Oxford/AstraZeneca za a kawo wa nahiyar ta Afirka zuwa karshen wannan wata na Fabrairu kodayake wannan ya danganta ne da jadawalin da WHO ta bayar dan yin rigakafin gaggawa. Ana ci gaba da yin nazari akan haka kuma sakamakon nazarin zai bayyana nan bada dadewa ba”.

Takardar taron manema labaran ta bayyana cewa kwayar maganin guda 320,000 ne za a raba su ga kasashen Afirka guda hudu bisa ga yawan mace-macen kananan yara da ake dasu yanzu da kuma samuwar yanayin “70 degrees Celsius” a wadannan kasashe.

Kasashen sune: Cape Verde, Rwanda, South Africa da Tunisia.

Wani karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa tsarin jadawalin raba maganin ya nuna cewa Najeriya ta shirya tsaf dan karbar kwayoyin maganin rigakafin da yawun su yakai 16,000,000.

Kammalawa:

Labarin da jaridar Punch ta wallafa a shafin tan a farko cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta dakatar da Najeriya daga neman maganin rigakafin cutar Korona karya ne.

Binciken CDD ya gano cewa Najeriya har yanzu cikin jerin kasashen da za a aikawa maganin cutar rigakafin cutar ta Korona.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Sipetan Yan Sandan Najeriya Ya Mika Ragamar Hukumar Yan Sanda Ga Mai Rikon Kwarya?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 2 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani zauren yanar gizo mai suna OperaNews ya wallafa inda yace Sipetan Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu mika ragamar mulki ga sabon sipetan yan sanda da zai maye gurbin sa.

Labarin yace Sipeta Adamu ya cika shekaru 35 da kama aikin gwamnati dan ya mika ragamar hukumar yan sanda ga mataimakin sa mai kula da harkokin yau da kullum mai suna Sanusi Lemo.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa kawo ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekara ta 2021 Mohammed Adamu shine Sipetan Yan Sandan Najeriya. Labarin da ke cewa ya mika ragamar shugabanci ga mataimakin sa ba gaskiya bane.

Da yake maida martani ga labarin, mai magana da yawun yan sandan Najeriya Frank Mba a wata hiar da yayi da jaridar Nation ranar 2 ga wata Fabrairu yace rahoton da ke yawo cewa sipetan yan sanda Mohammed Adamu ya mika shugabanci ga DIG Lemo ba gaskiya bane, dan haka jama’a suyi watsi da labarin. Kawo lokacin hada wannan rahoto ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, Shugaba Muhammadu Buhari bai ayyana wanda zai jagoranci hukumar yan sandan dan maye gurbin Mohammed Adamu ba.

Kammalawa:

Jita-jitar da ake yadawa cewa Sipetan Yan Sandan Najeriya Mohammaed Adamu ya mika jagorancin ma’iakatar yan sanda ga wanda zai rike ma’aikatar na wucin gadi ba gaskiya bane.

Kawon lokacin hada wannan rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, Mohammed Adamu ne ke ci gaba da zama Sipetan Yan Sandan Najeriya.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Status Din Da WhatsApp Ya Saka Wani Salon Kutse Ne Ga Masu Amfani Da Manhajar?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne.

Tushen Magana:

A ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigada (CDD) sun gano wata murya da aka nada kuma aka yadata a manhajar WhatsApp da ke gargadin dukkan mutane masu amfani da manhajar ta WhatsApp da su guji latsa status din WhatsAppp din ya saka.

Muryar tace wani balarabe ne ya kirkiri “status” din kuma duk wanda ya latsa dan kallon hoton da aka saka to lallai balaraben zai samu damar shiga rumbun hotunan wayar sa.

Wannan murya ta kara da cewa duk wanda ya latsa wannan status da WhatsApp ya saka to za’a yada dukkan hotunan batsa da ke wayar sa ga sauran jama’a.

Wannan sako ya bukaci duk wanda ya saurare shi ya yadashi ga sauran jama’a.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan wannan batu ya gane cewa sakon da aka nada cikin murya ake yadashi din sako ne na karya.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa manhajar WhatsApp tana da wani tsari na hana bibiya ko sarrafa abubuwan da mutum ke aiwatarwa a manhajar da ya shafi nadan murya ko wasu abubuwa da mutum ya ajiye a manhajar.

Mai magana da yawun manhajar ta WhatsApp ya bayyana cewa akwai labaran bogi da rudani da yawa da ake yadawa game da sauye-sauyen da suka gudanar a baya-bayannan.

Kanfanin WhatsApp din yace yana so ne ya sanar da mutane tsare-tsaren sa na bada kariya da kiyaye sirrin masu amfani dashi shiyasa ya sanar dasu ta hanyar status din. WhatsApp ya kara da cewa yana so ne mutane suji kai tsaye daga gare shi, shiyasa yayi amfani da hanyar status inda kowane mai amfani da manhajar zai gani kai tsaye.

Kammalawa:

Binciken CDD ya gano cewa kallon “status” din kamfanin WhatsApp baya nufin samu damar shiga rumbun hotunan masu amfani da manhajar ta WhatsApp, labarin da ake yadawa cewa idan mutum ya kalli status din WhatsApp to za’a samu damar shiga rumbun adana hotunan sa labari ne na bogi.

Kamfanin WhatsApp yayi amfani da tsarin “status” ne dan sanar da masu amfani dashi wassu batutuwa game da manhajar.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin An Samu Rudani a Garin Legos Sakamakon Raba Rigakafin Cutar Korona?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano gaskiyar su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata murya mai tsawon dakika 51 da aka nada cikin harshen Hausa kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Muryar na cewa an samu hargitsi a garin Lagos inda mutane ke ta guduwa daga gidajen su, wasu ma na fadowa daga saman beni a yunkurin su na gujewa rigakafin cutar Korona da a cewar wannan murya ake rabawa a garin na Legas.

Wani sashi na sakon yace: “ana ci gaba da samun turmutsitsi a Legas sakamakon raba rigakafin cutar Korona”

“Turawa ne suka kirkiri rigakafin kuma lokacin da aka gwada shi akan mutane 1000 a kasar Birtaniya, 600 daga cikin wannan adadi sun mutu, wannan shine dalilin da yasa suke so su gwada akan bakaken fata. Allah ya kare mu”, inji wannan murya ta namiji da aka nada kuma ake yada ta ta manhajar WhatsApp.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar game da maganar cewa mutane na gujewa rigakafin cutar Korona a jahar Legas ya gano cewa karya ne.

Hujjojin da CDD ta tattara sakamakon binciken da ta gudanar sun bayyana cewa har yanzu ba’a shigo da rigakafin cutar Korona kasar Najeriya ba, dan haka batun fara raba shi ko mutane a Legas na guje masa karya ne.

Har wayau, CDD ta gano cewa babu wani yanayi da ya shafi gujewa jami’an lafiya a jahar Legas saboda raba maganin cutar Korona da suke yi.

Jaridar AfricaNews ta rawaito babban daraktan hukumar lafiya a matakin farko na Najeriya, Dr. Faisal Shuaib na cewa za’a shigo da rigakafin cutar Korona guda 100,000 Najeriya a zangon farko a watan Fabrairun shekara ta 2021 wadda kanfanin sarrafa magani na Pfizer zai samar.

Dr. Shuaib ya kara da cewa: “za mu shigo da rigakafin cutar Korona wadda kanafanin Pfizer ya samar wadda ke bukatar sarrafawa a ma’aunin Celsius 70”.

Kammalawa:

Wata murya mai tsawon dakika 51 da aka nada kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa mutane na gujewa rigakafin cutar Korona a garin Legas karya ne. Kawo lokacin hada wannan rahoto a ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2021 ba’a kawo rigakafin cutar Korona Najeriya ba balle ma ace mutane na guje masa a Legas sakamakon rabashi gare su. Wannan labari ne na bogi.

Al’amura na ci gaba da wakana lafiya kalau a Legas kuma mutane basu gujewa jami’an lafiya ba kamar yadda wannan sakon WhatsApp ya bayyana.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Babu Wani Tsarin Bada Data Da N10,000 Kyauta Ga Masu Amfani Da Wayar Salula!

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Damfara Ce

Tushen Magana:

A ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da sakonni da gano gaskiyar su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Sakon na cewa hukumar yin katin dan kasa tana bada tsarin shiga yanar gizo kyauta ga dukkan wadan da suka tantance lambobin wayoyin su.

Sakon mai lakabin “NINVerification” yayi ikirarin cewa hukumar yin katin dan kasa zata bada kyautar data da yawan ta yakai “5G” ga dukkan masu amfani da layin waya da suka wuce tsawon watanni uku suna amfani dashi.

Wani bangare na sakon yace: “ku duba idan kuna daga cikin wadan da zasu ci garabasar kyautar “5G” na data. Wannan tsari ne na kyautatawa ga dukkan wadan da sukayi amfani da layin wayar su har na tsawon watanni uku. Ga tsawon lokacin da za’a dauka ana bada garabasar: 30-01-2021 2021-2-29 “

Acikin wannan sako akwai wani adireshi na yanar gizo da aka bayar ga masu neman garabasar dan ziyarta su nuna sha’awar su.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa ikirarin bada garabasar data har ta “5G” din karya ne. kawai wasu mazambata ne ke tsara ire-iren wadannan sakonni dan cutar jama’a, amma babu wani tsari daga hukumar yin katin dan kasa na bada data kyauta ga masu amfani da layin wayar salula.

Binciken CDD har wayau ya bankado irin yadda aka tsara rufta jama’a ta hanyar bukatar su da su bayanan su a matakai uku tare da neman su kara yada wannan sako a zaurukan WhatsApp dan sauran mutane su gani.

Idan mutum ya fara bada bayanan sa za’a kara yi masa alkawarin naira dubu goma (N10,000) tare da bashi data mai yawan “5G”.

Wadannan mayaudara sun wallafa wasu bayanai na bogi da ke nuna yadda wasu mutane suka gwada tsarin kuma suka samu gamsuwa.

CDD ta kara gano wani gargadi da hukumar yin katin yan kasa ta wallafa a shafin tan a yanar gizo inda tace mutane suyi hankali wajen yarda da labaran bogi game da ta.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa cewa hukumar da ke yin katin dan kasa NIMC na bada data har “5G” da N10,000 ga masu amfani da wayar salula karya ne. Wadan su bata-gari ne suka kirkiri sakon kuma suke yadashi dan damfaran jama’a, dan haka a kula.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Gwamnatin Tarayya Ta Bada Biliyan Dari Ga Kungiyar Miyetti Allah Da Nufin Magance Kashe-Kashe Da Garkuwa Da Mutane?

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 24 ga watan Janairun shekara ta 2021, an yada wani bidiyo a shafin Twitter wadda ya janyo cece-kuce da tofa albarkacin baki daga mutane da yawa, bidiyon yayi zargin cewa gwamnatin tarayya bada kudi har naira miliyan dubu dari ga kungiyar Fulani makiyaya ta “Miyetti Allah” dan tsayar matsalar kasha-kashe das ace-sacen mutane da ke faruwa a fadin kasar nan.

Bidiyon wanda rahoto ne da gidan talabijin na Roots TV ya gabatar, mawallafin wata mujalla da ake bugawa a harshen Turanci mai suna “Ovation Magazine” Dele Momodu ya wallafi a shafin sa na Twitter a safiyar ranar Ladin da ta gabata.

Wani mai amfani da shafin Twitter wadda ke da tarin magoya baya, Kelvin Odanz (@MrOdanz) ya sake wallafa wannan bidiyon inda yayi masa take kamar haka: “gwamnatin Najeriya ta bada naira miliyan dubu dari ga makiyaya domin su daina aikata muggan laifuka. Naira miliyan dubu dari ga kungiyar da tayi garkuwa da mutane, ta kashe tare da tagayyara rayuwa. Lallai wannan al’amari yayi kyau”

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu bin diddigin labarai da bayanai dan gano sahihancin su na CDD suka gabatar ya gano cewa bidiyon da Dele Momodu da Mr. Kevin suka wallafa ba bidiyo ne na kwanan nan ba. Hasalima binciken ya gano cewa tun farko gidan talabijin na “Roots TV” ne ya fara wallafi a shafin san a YouTube a ranar 14 ga watan Mayun shekara ta 2019.

Fadar shugaban kasa a lokuta daban-daban ta karyata zargin cewa ta bada naira miliyan dubu dari ga kungiyar Fulani makiyaya dan tsayar da matsalar garkuwa da mutane dake faruwa a kasar nan. Wannan ba shine karon farko da ake yada wannan bidiyo da wannan zargi ba.

A ranar 10 ga watan Mayun shekara ta 2019, an yada irin wannan jita-jita da zargi a kafafen sada zumunta na zamani dama saura kafafen yada labarai da aka sani, wannan al’amari ya janyo a wancan lokaci gwamnatin tarayya ta hannun mai Magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu yayi bayani a gidan talabijin na Channels ranar 10 ga Mayu, 2019 inda ya karyata batu.

Shima da yake amsa tambayoyin manema labarai game da batun a watan Mayun shekara ta 2019, babban sipetan yan sanda na kasa, Mohammed Adamuyace gwamnatin tarayya bata baiwa makiyaya ko kungiyar su naira miliyan dubu dari ba. Rahaton da “Roots TV” wanda shine gidan talabijin din da ya wallafa labarin tun farko ya janyo cece-kucen za’a iya samun sa a dandalin YouTube

A martanin da ta mayar, kungiyar “Miyetti Allah” tace hakika ta neman gwamnatin tarayya ta bata naira miliyan dubu dari a shekarun baya amma ba a karkashin wannan gwamnati mai ci yanzu ta Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Sakataren kungiyar “Miyetti Allah”, Saleh Alhassan ya gayawa jaridar Punch a watan Mayun shekara ta 2019 cewa naira miliyan dubu dari din da kungiyar tasu ta nema ba wai da kowace manufa bane face dan ginawa makiyaya wuraren kiwo dan saukaka musu al’amuran su na kiwo.

Alhassan yace: “lallai wannan zargi na biyan naira biliyan dari ga kungiyar makiyaya mummunan zargi ne. Shin dama gwamnati na bada haka sakaka? Sun taba biyan kudi kamar haka. Ai maganar neman wannan kudi ta naira miliyan dubu dari ta kasance a teburin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan tun shekara ta 2014 a lokacin da yake neman warware rikicin makiyaya da manoma”.

Saleh ya kara da cewa wani bangare na wadaddan kudade gwamnanin jihohi sunyi amfani dashi a karkashin kwamitin da tsohon gwamnan jahar Benue Gabriel Suswam ya jagoranta, “ko a haka ma bana jin kaso mai yawa na kudin ya kai ga makiyaya”

Dalilan da suka janyo aka sake dawo da bidiyon a wannan lokaci

Yanzu ana ci gaba da cacar baka ta hanyar kafafen yada labarai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnan jahar Ondo wanda ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga Fulani su bar jahar ta Ondo. Gwamnan Ondo ya bada wa’adin kwanaki bakwai din ne ga Fulani subar wuraren kiwo da ke dazukan jahar Ondon dan magance matsalar garkuwa da mutane da tayi kamari da kuma ake zargin Fulanin da aikatawa kuma suna buya a cikin dazukan.

Yadda Maganar Miliyan Dubu Dari ta Samo Asali

A shekara ta 2014, gwamnatin tarayya karkashin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta kafa wani kwamiti akan wuraren kiwo a karkashin shugabancin tsohon gwamnan jahar Benue Gabriel Suswam.

Kwamitin ya bada shawarar cewa babban bankin kasa na CBN ya samar da wasu kudade dan taimakawa wajen kirkirar kananan wuraren kiwo na zamani a duk fadin kasa baki daya.

Suswam a lokaci da yake yiwa yan jaridar fadar shugaban kasa bayani a ranar 26 ga watan Oktoban shekara ta 2014 bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta kasa ya bayyana shirin gwamnatin tarayyar.

Haka nan, a watan Satumban shekara ta 2019, gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari ta kara karkade shirin tsohuwar gwamnatin lokacin da rikici tsakanin manoma da makiyaya yayi kamari a arewa ta tsakiya, wannan ya zo ne a lokacin gwamnatin ta karbi tsari na kyautata kiwo na kasa. Wannan shiri na gwamantin tarayya Gwamnan Ebonyi ne, David Umahi ya sanar shi ne ya sanar dashi jim kadan da kamala taron kasa akan tattalin arzikin kasa wanda ya gudana a Abuja.

A cewar Umahi a karkashin tsarin, gwamnatin tarayya za ta samar naira miliyan dubu dari wanda shine kaso 80  yayin da gwamnaotcin jahohi za su bada wurare ko kasa  da yanayi dama sauran kaso 20 dan aiwatar  tsarin da ake yiwa lakabi da “Ruga”.

Wannan shiri na gwamnatin tarayya ya gamu da tazgaro inda ya fuskanci mummunar tsana da kiyayya daga yan Najeriya a kafafen sada zumunta na zamani, wannan ya janyo daga baya gwamnatin ta dakatar da shirin.

Kammalawa:

Wani bidiyo da ake wallafawa tare da yadawa a kafafen sada zumunta na zamani inda ake zargin cewa gwamnatin tarayya ta bada naira miliyan dubu dari ga kungiyar makiyaya ta “Miyetti Allah” bidiyo na karya haka nan yana cike da rudani. Binciken CDD ya gano cewa bidiyon an dauke shi ne shekaru biyu da suka gabata, wannan kuma ya saba da ikirarin da masu wallafawa da yada shi ke yi cewa sabon bidyo ne.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Gwamnatin Tarayya Na Raba Tallafin N10,500 Duk Sati Ga Yan Najeriya?

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 20 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da bayanan da ake dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sunyi kichibis da wani sako da aka kirkira kuma ake yada shit a manhajar WhatsApp. Sakon nan cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin naira dubu goma da dari biyar (N10,500) a matsayin tallafi ga yan Najeriya a kowane mako .

Sakon wanda aka yima sa lakabin: “tallafin rage radadin cutar Korona a zango cutar na biyu”,  ya bukaci jama’a da su nemi tallafin wanda a cewar sakon cika fom neman baya daukar lokaci mai tsawo.

Wannan adireshi na yanar gizo da ke neman wanda ke da sha’awar tallafin su nema yace hadakar kungiyoyiin sakai masu zaman kansu da ke bada tallafi wajen yakar cutar Korona (CA-COVID) ne ka bada tallafin. A shafin an wallafi sakonnin bogi na wassu mutane da aka bayyana su a matsayin wadan da sukaci gajiyar tallafin suna tofa albarkacin bakin su.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa babu wani tsarin tallafi da gwamnatin tarayya ke bayarwa na N10,500 ga yan Najeriya duk sati. Binciken har wayau ya bankado cewa yan danfara ne suka kirkiri adireshin yanar gizo tare da kirkiran sakon dan yaudaran jama’a.

Hotunan da za’a gani a shafin yayin da mutum ya ziyarci ce shi sun hada wadannan da za’a iya gani a sama, kuma binciken da CDD ta gudanar wadda ya shafi nazarin hotunan ta hanyar fasaha ya gano cewa an dauke su ne yayin raba kudaden tallafin Korona a yankin Kwale dake gundumar babban birnin tarayya Abuja a watan Afirilun shekara ta 2020.

Karin binciken da CDD din ta gudanar wadda ya hada ziyartan shafukan sada zumunta na hadakar kungiyoyi da masa’antu masu zaman kansu da ke taimakawa yunkurin gwamnati na yakar cutar Korona ya cewa hadakar bata da wani shiri na bada tallafin N10,500 ga yan Najeriya.

Kammalawa:

Wani sako da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin N10,500 ga yan Najeriya duk sati karya ne. Sakon wani tarko ne da yan damfara suka tsara dan cutar jama’a, dan haka CDD na jan hankali mutane da su gujewa amincewa ko yada sakon.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku a kansu dan tantance muku ta wannan lamba: +2349062910568 ko ta shafin Twitter: @CDDWestAfrica/@CDDWestAfrica_H

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Kwamitin Gwamnatin Tarayya Kan Yakar Cutar Korona Bai Fitar Da Sanarwa Game Da Saka Dokar Kulle Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2021 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa a manhajar WhatsApp, sakon na cewa kwamitin kar takwana na gwamnatin tarayya aka cutar Korona ya fitar da sakon game da sake kakaba dokar kulle  a fadin kasa.

Sakon y ace: “nan ba da dadewa ba, watakila ma a karshen makonnan za’a saka dokar kulle ta tsawon sati biyu”, karshen ya nuna wadda ya sa hannu wato: “Dr. Sani Aliyu” tare da ayyana shi a matsayin “shugaban kwamintin yaki da cutar Korona na gwamnatin tarayya”.

Gaskiyar Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na CDD sun gano cewa ba kamar yadda sakon da aka yada din ya zayyana ba, Dr. Sani Aliyu ba shine shugaban kwamitin yaki da cutar Korona na gwmanatin tarayya ba, shugaban shine Boss Mustapha wadda kuma shine sakataren gwamnatin tarayya.

Har wayau, CDD ta samu wani bidiyo mai tsawon dakika 51 da kwamitin kar takwana kan cutar Korona na gwamnatin tarayya ya sake, acikin bidiyon, shugaban tsare-tsare na kwamitin, Dr. Sani Aliyu ya bayyana sakon da ake yadawa game da saka dokar kullen a matsayin labarin bogi yayin day a gargadi jama’a da su guji yarda sakon bogin da ake yadawa din.

Dr. Sani Aliyu kara da cewa, kwamitin gwamnatin tarayyar ya da sahihan hanyoyin da yake bi wajen yada bayani, ba yadda za’a kwamitin ya yada muhimmin sako da manhajar WhatsApp.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewar jita-jitar da ake yadawa cewa kwamitin gwamnatin tarayya kan yakar cutar Korona ya fitar da sanarwa game kakaba dokar kulle karya ne. Wani bidiyo mai tsawon dakika 51 da mai kula da tsare-tsaren kwamitin, Dr. Sani Aliyu yayi magana acikin sa hujja ce akan haka. Sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp game da dokar kullen sako ne na bogi.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Kananan Yara Sun Kada Kuri’a a Zaben Kananan Hukumomi Da Ya Gudana a Jahar Kano

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 16 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigada (CDD) sun gano tarin hotuna da bidiyoyi da ke nuna kananan yara suna kada kuri’a a lokacin da ake gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar a fadin jahar Kano.

Hotunan da ma bidiyoyin an yada su sosai a shafukan Twitter da Facebook, kuma acikin su anga yara wadan da bisa doka shekarun su basu kai na kada kuri’a suna dangwala hannayen su a kuri’u yayin da jami’an zabe kalmashewa tare da jefa ta acikin akwatin zabe.

Bidiyoyin sun janyo cece-kuce da tofin alatsine daga yan Najeriya a kafafen sada zumunta na zamani.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar dangane da hotuna da bidiyoyin ya gano cewa an bar yara sun kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da kansilolin na jahar Kano na shekara ta 2021.

Karin binciken da ya shafi fasaha da CDD din ta gudanar ya gano cewa bidiyoyi da hotunan an dauke su ne a zaben shekara ta 2021 din ya suka nuna yara kanana suna kada kuri’a a wurare daban-daban.

Daya daga cikin hotunan da yara suka kada kuri’un an dauke shi ne a karamar hukumar Kabo yayin da wani bidiyon da shima yake nuna nuna yara na kada kuri’a tare da tallafin wassu jami’an zabe aka nade shi a Shahuci da ke karamar hukumar birni dake cikin birnin Kano (Kano Municipal Council).

Bayan nazari da bincike, CDD na tabbatar da cewa kada kuri’un da yara suka yi dama yin zabe sau da yawa da wassu manya aka gani suna yi ya faru ne a gaban jami’an zabe na hukumar zabe ta jahar Kano, hasali ma anga jami’an hukumar zabe ta jahar Kano (KANSIEC) din suna taimakawa yaran da manya masu zabe fiye da sau daya.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa akwai hotunan zaben shekara ta 2018 da aka gudanar na kananan hukumomi a jahar Kano din da wassu mutane suka sake yada su tare da bayyana su a matsayin hotunan zaben shekara ta 2021.

Wannan hoto da ke kasa da wani shafin Twitter mai suna @Ayemojubar hoto ne da aka dauke shi lokacin zaben kananan hukumomi na shekara ta 2018 a jahar Kano.

Kammalawa:

Wadan su daga cikin hotuna da bidiyoyin da suka nuna yara kanana suna kada kuri’a lokacin zaben kananan hukumomi na shekara ta 2021 a jahar Kano hotuna na ne gaske, al’amarin ya faru. Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an bar yara kanana sun kada kuri’a tare da barin sauran wassu mutanen su kada kuri’a sau da daya.

Binciken CDD ya gano cewa masu anfani da kafafen sada zumunta na zamani sun yada hotunan kananan yara na kada kuri’a wadan da aka dauka a zaben day a gabata na shekara ta 2018 lokacin wannan zabe na shekara ta 2021.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Ba a Nahiyar Afirka Kawai Ake Raba Rigakafin Cutar Corona Mai Suna “Remdesivir” Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

Tun watan Satunban shekara ta 2020 majiyoyi da masu anfani da kafafen sadarwa na zamani suka yi ta wallafa hoton kwalin wani magani mai suna “Cipremi” wanda ake yiwa lakabi da allurar “Remdesivir”.

Hoton kwalin maganin yana dauke da wani bayani da ke cewa maganin cutar Corona da za a yi gwajin sa akan mutanen nahiyar Afirka kawai, wannan batu ya sake zama sabo inda mutane ke ci gaba da wallafa irin wannan sako musamman a yan makonnin baya-bayannan.

Masu anfani da kafafen sada zumunta na zamani da dama suna bayyana cewa anaso ayi anfani da maganin ne akan jama’ar nahiyar Afirka da mummunar manufa kuma wannan shine dalilin da yasa ake son gwada shi a nahiyar Afirka. Wani ami anfani da kafar sada zumunta na zamani mai suna Ozolua. O. Giwa-Amu ya wallafa inda tsohon Ministan Zirga-Zirgar Jiragen Sama Femi Fani-Kayode ya kara wallafa labarin. Tsokacin da mutane suka yi game da “Remdesivir” din sun bayyana shi a matsayin magani.

Gaskiyar Al’amari:

Remdesivir ba maganin cutar Corona ba ne. Bayanan da kamfanin Gilead Sciences Inc ya samar a shafin sa na yanar gizo wanda shine ya kirkiri “Remdesivir” nuna cewa “Remdesivir” wani sinadari ake gudanar da bincike akan sa da manufar magance cutar Corona ajikin yara yan kasa da shekara 12 da kuma suke da nauyin 3.5kg ko kasa da 40kg.

Da suke maida martani a shafin Twitter game da batun, Cipla South Africa sunce “ana anfani da “Remdesivir” dan kula da lafiyar wadan da cutar Corona ta yiwa illa sosai amma bawai magance Corona yake yi ba. Akwai doka mai tsauri game samuwar sa Cipla basu samu lasisi ko izinin samarwa da raba shi ba” ana iya samu karin bayani gama da wannan sinadari a wannan shafi Voluntary Licensing Agreements for Remdesivir

Bisa ga tsarin dokokin yarjejeniyar wanzuwar sinadarin wadda ya Cipla ke ciki, an yarda ayi musayan fasahar kanfanin Gilead kan kirkirar Remdesivir dan gaggauta samuwar sa cikin karamin lokaci.

Me Yasa Aka Zabi Nahiyar Afirka Kawai?

Kanfanin Gilead ya kara da cewa: “wadan da ke izinin samar da maganin suma suna da wani matakin farashi da suka samar”, a cewar wani jawabi da Reuters suka wallafa.

Har wayau jawabin ya ci gaba da cewa lasisin zai ci gaba da samun sassauci har sai hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta aiyana karshen annobar cutar Corona

ko kuma sai lokacin da aka samu wani magani bayan Remdesivir da aka amince  ayi anfani dashi dan kula ko magancewa ko kare mutane daga cutar Corona”

Yarjejeniyoyin da aka cimma sun bada damar kai maganin zuwa kasashen irin su: Vietnam, Ukraine, Thailand, Zambia, Togo, South Africa, North Korea da Cuba a jerin kasashe 127 da za’ayi anfani da maganin wanda mafiya yawan su na Afirka ne.

Masu tantance sahihancin labarai sun tuntubi Farfesa Morenike Ukpong ta tsangayar Nazarin Lafiyar Hakorin Yara na Sashin Karatun Lafiya na Jami’ar Obafemi Awolowo inda tace lamarin ba wani bakon abu bane, hasalima ana kiran sa banbanta farashi wajen saida kayayyaki kuma kasashe na iya daidatawa game da farashin musamman a lokacin da ake matakin samar da maganin.

“kanfanoni da yarda su samar da magani cikin farashi mai rahusa bawai dan samar da magani marar inganci ba, a’a, sai dai kawai dan suma suna so su bada taku gudummawar musamman a kasashe matalauta. Sukan yi hakanne da magance kwararar cututtukan zuwa sauran kasashe masu karfin tattalin arziki”, a cewaFarfesa Morenike.

Karerayin da ake yadawa cewa ba’a yarda ayi anfani da maganin a nahiyar Turai ba karya ne. Hasalima Tarayyar Turai ta shiga cikin yarjejeniyar Euro miliyan sittin da uku (€63 million) da kanfanin Gilead Science a watan Julin 2020 dan samar da maganin mai suna “Remdesivir”  dokacin kasashe 27 da ke nahiyar ta Turai. Stella Kyriakides, kwamishina mai kula da fannin abinci da lafiya ta bayyana cewa za’a samar da maganin ga marasa lafiya kimanin 30,000 da ke cikin mawuyacin hali bayan kamuwa da cutar ta Corona. Kwamishinar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai ranar 9 ga watan Yulin shekara ta 2020.

Kammalawa:

Labarin da ake yadwa cewa sinadari mai suna “Cipremi” da ake yiwa lakabi da allurar “Remdesivir” maganin cutar Corona ne da aka samar dan yin gwajin sa akan mutanen nahiyar Afirka karya ne. Sinadarin ba maganin cutar Corona ba ne, kawai an samar dashi ne dan taimaka wa masu dauke da cuta mai yaduwa wadda kuma ake anfani dashi akan wadan da cutar Corona ta galabaita.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Farfesa Ebere Onwudiwe Ba Ya Cikin Bidiyon Ake Watsa Dalar Amurka

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 11 ga watan Janairun shekara ta 2021 suka gano wani bidiyon inda mutane sanye da fararen kaya suke shagalin biki, a wajen wannan shagalin biki anata kari da watsi da dalar Amurka.

Bidiyon wanda aka yadashi sosai a manhajar WhatsApp anyi ikirarin cewa bidiyo ne da aka dauke yayi bikin nadin sarautar Farfesa Ebere Onwudiwe a ,matsayin Mba 1 na Isunjaba wanda ya gudana a watan Disamban shekara ta 2020. Farfesa Onwudiew ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Corona a ranar 9 ga watan Janairun shekara ta 2021 ku a kafin rasuwar sa babban shehin malami ne mai nazartan harkokin siyasa a Jami’ar Wliberforce dake Ohio a Amurka, sannan Onwudiew babban manazarci ne a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD).

Gaskiyar Magana:

Binciken da nazari da CDD ta gudanar da shafi fasaha ya gano cewa bidiyon ya kunshi mambobin wata kungiya ce mai suna Asian Tigers wanda mafiya yawan su jahar Anambra na da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Mambobin kungiyar Asian Tigers din sun halarci taron nadin sarautar gargajiya ne a Agulu da ke jahar ta Anambra. Nazarin CDD har wayau ya gano cewa bidiyoyin na mambobin kungiyar Asian Tigers din ne kuma wani masoyin wannan kungiya mai suna Ufo Solomon ya wallafa bidiyon a shafin sa na Facebook. Haka nan wani mai suna Okafor Ukay dake ikirarin cewa shi dan kungiyar ne dake zaune a kasar Qatar shima ya wallafa bidiyon a watan Janairun shekara ta 2020, wato shekara ta daya cif da ta gabata.

Bayan nazarin da suka gabatar, masu bin diddigin labarai na CDD suna tabbatar da cewa Farfesa Onwudiwe ba mamba ne na kungiyar Asian Tigers din ba dan haka basu halarci nadin nasa ba.

CDD ta tuntubi Mr. Ray Ekpu, wanda makusanci ga Farfesa Onwudiwe wanda yaje nadin nasa yace Farfesan ba mamban wannan kungiya bace. Tun a baya Mr. Ekpu ya sanar da jaridar Premuim Times rasuwar Farfesan.

Mr. Ekpu yana daya daga cikin wadan da suka kafa mujallar Newswatch ya bayyana cewa bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta zamanin da ke cewa Farfesa Onwudiwe yana ciki bidiyo ne na karya. A cewar Mr. Ekpu anyi bikin nadin sarautar cikin takaitaccen yanayi kuma Farfesa Pat Utomi yana daya daga cikin mahalarta taron.

Kammalawa:

Wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani inda da akaga wassu mutane sanye da fararen kaya suna watsa dalar Amurka kuma akace bidiyon nadin sarautar Farfesa Onwudiwe bidiyo ne na karya.

CDD na jan hankalin jama’a da su guji yada labaran da basu tantance sahihancin su ba. Kuna iya turo wa CDD labaran da kuke da shakku a kansu dan tantance sahihancin su.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Ayi Hankali Da Shafin Yanar Gizon Bogi Da Ake Yadawa Game Da Tallafin N500,000 Na CBN

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 13 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da aka wallafa kuma ake yadawa a manhajar WhatsApp, sakon na ikirarin cewa gwamnatin tarayya bisa hadin gwiwar babban bankin kasa na CBN zasu fara bada tallafin naira dubu dari biyar (N500,000) ga dukkan matasan Najeriya.

Sakon har wayau ya ce an ware kudaden dan baiwa matasan Najeriya wannan tallafin ta hanyar wani tsari na tallafawa matasa dan gudanar da sana’o’i kuma wadan da suke bukatar samun tallafin sais u ziyarci wannan adireshi na yanar gizo: https://bit.ly/CBN–Youth-Grant da cika fom din neman tallafin. A cewar sakon za’a rufe neman samun tallafin a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2021.

Gaskiyar Magana

Binciken da CDD ta gano cewa babu wani tsari na bada tallafin N500,000 ga dukkan matasan Najeriya da gwamnatin tarayya ko babban bankin kasa ya shirya. Adireshin yanar gizon da ake yadawa na bogi.

CDD ta gano cewa wassu mazanbata ne suka kwaikwayi shirin gwamnatin tarayya wanda ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni na samar da aikin yi da sana’o’i ga matasa ta hanyar kirkirar guraben aiyuka rabin miliyan (500,000) tsakanin shekara ta 2020 da 2023.

Adireshin yanar gizo na gaske da gwamnatin tarayya ke gudanar da tsarin samar da ayyukan yi da tallafin sana’o’i shine: FMYSD, haka nan adireshin babban bankin kasa shine: CBN.

Karin binciken da CDD ta aiawatar ya gano cewa yan danfara suna anfani da ire-iren wadannan salo dan zanbatan mutane. Sau da yawa yan danfarar sukan bukaci mutane da su gaya wassu mutanen game da irin wannan tallafin, sukan yi hakan ne da samun mutane da zasu yi rijista kuma su bada bayanan su wadan da da sune za’a anfani wajen zanbatan su.

Da CDD ta tuntube ta, mai taikamawa ministan matasa da bunkasa wasanni, Areola Oluwakemi ta bayyana cewa sakon WhatsApp din aka yadawa sako ne na bogi.

Oluwakemi ta bukaci yan Najeriya da su ziyarci shafin ma’aikatar matasa da wassanin dan samun gamsassun bayanai: https://youthandsport.gov.ng/

Ta kara da cewa: “mutane su rika ziyartan amintaccen shafi tare da bin ka’idojin da aka samar da kaucewa fadawa hannun yan danfara”

Kammalawa:

Wani adireshin yanar gizo da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke cewa gwamnatin tarayya da babban bankin kasa CBN na bada tallafin N500,000 ga matasan Najeriya adireshi ne na bogi dan haka jama’a a kula!

Domin samun gamsashshen bayani game da tsarin tallafin ma’aikatar matasa da wasannin zaku iya ziyartan wannan sahihin shafi:  Ministry of Youth and Sport Development dama na babban bankin kasa CBN website.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai da sakonni kafin yada su ga sauran jama’a.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku da akansu dan tantance muku su ta hanyar wannan lambar: +2349062910568 ko a shafin Twitter: @CDDWestAfrica/@CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Cutar COVID19 Ba Ta Hallaka Mambobin Cocin ECWA 200 Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 11 ga watan Janaiarun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da TrueTellsNigeria” suka wallafa inda suka ce mambobin cocin ECWA dari biyu (200) sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona

Labarin wanda har wayau wani zauren yanar gizo Akpraise ya wallafa da jigon labari kamar haka: sananniyar cocin Najeriya na cikin jimami bayan mutuwar mambabin ta 200 sakamakon harbuwa da cutar Corona

A cewar labarin, sanarwar mutuwar mambobin cocin ECWA din ta fito ne daga shugaban cocin Reverend Stephne Baba a lokacin binne daya daga cikin mambobin cocin, Yakubu Kadiya da ya gudana a Kent Academy Academy Miango, karamar hukumar Bassa, jahar Filato.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin mutuwar mambobin cocin ECWA 200 karya ne. Da CDD ta tuntube shi game da batun, mai magana da yawun cocin ECWA din wadda ke da hedikwata a Jos, babban birinin jahar Filato, Reverend Romanus Ebenwokodi ya bayyana labarin baya kunshe da koami face tsagwaron karya.

Ya kara da cewa an jirgita bayanin shugaban cocin ne da nufin ruda mutane. Kakakin cocin ya kara da cewa, abinda shugaban cocin ya fada shine, matsin tattalin arzikin da cutar Corona ta haifar ya shafi masu aikin yada manufar cocin su 200.

Bayanan kakakin cocin sun kara bayyana cikin wata sanarwa da cocin ya fitar inda yace cutar Corona bata hallaka mambobin cocin 200 ba kamar yadda zaurukan yanar gizo suka rawaito.

Sanarwar da cocin ya fitar bayyana karara cewa annobar cutar Corona ta shafi yadda cocin ke gudanar da aika-aikacen yada manufar cocin ECWA din.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa mambobin cocin ECWA guda dari biyu (200) sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona karya ne. Kakakin cocin ya bayyana cewa jawabin da shugaban cocin yayi ne zaurukan yanar suka jirgita inda suka fadi abinda bashi ne abinda ya fada ba.

A kodayaushe ku tabbata kun tantance sahihancin labarai ko sakonni kafin yada su ga sauran jama’a.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

A Kula Da Kyau! Ba Hukumar NIMC Ce Ta Samar Da Manhajar Da Ke Hada Bayanan Layin Waya Da Lambar NIN Ba

By Fact Check, Uncategorized

Tushen Magana:

Akwai wata manhaja da ake anfani da ita a wayar salula dake ikirarin cewa zata hada katin dan kasar mutum da kuma bayanan da ke kan layin wayar sa, wannan manhaja yanzu haka tana samun tagomashi a dandalin yanar gizo.

Wadan da suka kirkiri wannan manhaja sunyi ikirarin cewa manhajar zata warware matsalolin da mutane ke fuskanta wajen hada bayanan dake kan layin wayar su da na katin dan kasa, kuma mutane na iya yin rijistar lambar su ta NIN har ma da na layin waya, ana ma iya anfani da manhajar a cewar wadan da suka kirkire ta wajen samun bayani game da NIN.

Har wayau, makirkiran manhajar sunce tana saukaka yin rijistar layukan waya na MTN da Glo da 9Moblie ad Airtel dama hada bayanan wadannan layukan da lambar NIN.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa manhajar da ke ikirarin hada bayanan layin waya da lamabar NIN din ba ta fito daga hukumar yiwa yan kasa katin shaida ba, hasali ma hukumar tayi gargadi ga jama’a game da manhajar.

A wani tsokaci da tayi ta shafin tan a Twitter (@nimc_ng), hukumar ta barranta kanta da manhajar inda tace yan danfara ne suka kirkiri ta dan tattara lambar NIN dama BVN din su.

“ba hukumar NIMC ko gwamnatin tarayya bace ta kirkiri manhajar. Wassu yan danfara ne suka kirikire ta dan biyan bukatun kansu dama zaluntan mutane ta hanyar samun muhimman bayanan su irinsu NIN da BVN”, a cewar NIMC.

Karin binciken CDD ya gano an tsara manhajar ta yadda zata debo bayanai daga kan wayoyin mutane.

Kammalawa:

Wata manhaja da aka kirikire ta kuma akayi ikirarin cewa za’a iya anfani da ita wajen hada bayanan layin waya da lambar NIN bata fito daga hukumar da ke yiwa jama’a katin dan kasa ba wato NIMC. Yanzu haka manhajar tana runbun ajiyar manhajoji na Google.

Dan haka CDD na jan hankalin jama’a da su kula da kyau kada su fada hannun bata gari ko yan danfara yayin yunkurin su hana bayanan layin wayar su da lambar NIN.

A kodayaushe ku tabbata kun tantance sahihancin labarai ko sakonni kafin yada su ga sauran jama’a.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa