Skip to main content
Tag

Fact Check Hausa - Centre for Democracy & Development

Hoton Zanga-Zangar Kungiyar Lauyoyi ta Kasa NBA Mai Dauke Da Kalmar “Autotomy” Hoto Ne Na Bogi

By Fact Check

Tushen Magana:

Anga wani hoto da ake yadawa ta shafukan Twitter da WhatsApp da Facebook da ke cewa an rubuta kalmar Turanci ta “Autonomy” cikin kuskure inda aka rubuta ta a matsayin “Autotomy” lokacin da ‘ya’yan kungiyar lauyoyi ta kasa “NBA” reshen babban barnin tarayya Abuja ke zanga-zangar goyon bayan ‘yancin bangaren shari’a.

Lokacin zanga-zangar anga lauyoyin na dauke da wani allo mai rubutu a jikin sa, kuma a jikin rubutun anga kalmar “Autotomy” wadda aka rubuta da jan alkalami.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken CDD ta gudanar ya gano cewa allon da ke dauke da kalmar “Autotomy” allo ne na bogi wadda aka yi amfani da fasaha wajen jirkita ainihin abinda kungiyar lauyoyin ta rubuta.

CDD ta tuntubi shugaban kungiyar lauyoyin reshen babban birnin tarayya Abuja, Hauwa Shekarau wadda ta bayyana hoton da ake yadawa mai dauke da kalmar “Autotomy” a matsayin ba bogi wadda wasu suka canzawa fasali dan cimma wata manufa.

Hauwa Shekarau ta baiwa CDD kwafin hotunan zanga-zangar da suka wallafa da ke dauke da ainihin kalmar “Autonomy” da suka yi amfani da ita a jikin hoton.

Masu zanga-zangar, wadan da ma’aikatan kotuna ne da lauyoyi sunbi sauran takwarorin su a fadin kasa baki daya a ranar Litinin da ta gabata kuma hoton da suka yi amfani dashi na dauke da kalmar “Autonomy” a jerin rubutun abubuwan da suke nema.

Kammalawa:

Wani hoto da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani da ke nuna cewa ‘ya’yan kungiyar lauyoyi ta kasa sunyi kuskuren rubuta kalmar “Autonomy” inda akayi ikirarin cewa sun rubuta “Autotomy” hoto ne na bogi wadda akayi amfani da fasahar zamani dan canza masa fasali.

Ainihin majigin da mambobin kungiyar lauyoyin tayi amfani dashi lokacin zanga-zangar na dauke ne da kalmar “Autonomy” ba “Autotomy” ba kamar yadda ake yadawa a dandalin Facebook da Twitter da WhatsApp.

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Labaran Karya da CDD ta Gano Tare da Binciko Sahihancin Su a Mako na uku, Watan Afrilu, 2021

By Fact Check

Aikin mu a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) shine ganowa tare da binciko gaskiyar labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani dama kafafen yada labarai.

A makon nan, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na CDD sun bankado wasu labaran karya da aka wallafa tare da yada su a shafukan sada zumunta na zamani.

A wannan makon da muke bankwana dashi, CDD ta gano wani labari da aka wallafa akan wani matashi mai suna Salim Sani Zakariyya, a labarin da yada shafin Twitter am wallafa hoton Salim inda aka yi rubuta a jikin sa kuma aka bayyana shi a matsayin wani dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Karanta Yadda Labarin ya Kasance:

A ranar Litinin, 12 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarain na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani jawabi da wani mai amfani da shafin Twitter mai lakabin @UchePOkoye ya wallafa. Jawabin na dauke da hoton Salim Sani Zakariyya kuma anga wani rubutu a jikin hoton kamar haka: “Dan Boko Haram Da Ake Nema Ruwa-a-Jallo”.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Salim Sani Zakariyya bashi da alaka da kungiyar Boko Haram. Binciken ya kara gano cewa Salim Sani Zakariyya baya cikin jerin wadan da Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa a matsayin yan Boko Haram da take nema, wannan kuma kai tsaye yana karyata ikirarin da Mr. Uche yayi wa Salim din a jawabin day a wallafa a shafin sa na Twitter.

CDD ta tuntube shi, Salim Sani Zakariyya ya ce ya yi mamakin abinda Mr. Okoye ya yi masa dan kawai ya gargade shi kan yada labaran bogi. Domin karanta cikekken labarin, latsa nan

Wasu Rahotannin Bincike da CDD ta Gabatar a Cikin Makon da ya Gabata

Farmer-Herder Conflict in Northern Nigeria: Trends, Dynamics and Gender Perspectives

Deradicalizing Rehabilitating and Reintegrating: Building Peace in Nigeria’s North East

Labarin da aka gabatar akan CDD

Insecurity and Covid-19: Threats to electoral democracy in Africa

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafa su

 1. hukumar hisbah a jahar kano bata ci tarar daliban jamiar bayero n20000 ba
 2. tantancewar da cdd ta aiwatar ba a yiwa dig moses jitoboh ritaya ba
 3. bill gates bai ce maganin cutar korona zai canza kwayoyin halittar danadam ba
 4. joe biden bai umarci hukumar shigi da ficin amurka ta bada izinin aiki da zama ta yanar gizo ga yan najeirya ba
 5. gwamnatin tarayya ba ta saye manhajar whatsapp ba

sheikh sharif ibrahim saleh bai soki dakatar da abduljabbar nasiru kabara daga waazi a kano ba

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Labaran Karya da CDD ta Gano Tare da Binciko Sahihancin Su a Mako na Biyu, Watan Afrilu, 2021

By Fact Check

Aikin mu a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) shine ganowa tare da binciko gaskiyar labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani dama kafafen yada labarai. A makonni biyun da suka gabata, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na CDD sun bankado wasu labaran karya da aka wallafa tare da yada su a shafukan Facebook da Twitter da manhajar WhatsApp.

Labaran da CDD ta gano din sun hada da labarin bogi da aka yada cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama tare da cin tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna rayuwa a daki daya tarar  naira dubu ashirin kowanen su, da Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya da dai sauran su:

Hukumar Hisbah a Jahar Kano Bata Ci Tarar Daliban Jami’ar Bayero N20,000 Ba!

A ranar 6 ga watan Afirilun shekara ta 2021, wani ya bulla daga kafafen yada labarai na yanar gizo da yawa. Labarin ya ce Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su sakamakon kama su da laifin zama a daki daya duk da kasancewar sub a ma’aurata ba.  Majiyoyi sun hada da: Sahara ReportersTori.ngKanyiDailyNigerDeltaConnectNaijaNewsAllSchoolsForum.

Labarin ya ce: “Hukumar Hisbah a Jahar Kano ta Bukaci Daliban Jami’ar Bayero Maza da Mata Su Biya N20,000 Dan Yin Belin Kansu Bayan Aikata Laifin Zama a Daki Guda”

Labarin da ake yadawa cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna zama a daki daya naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su karya ne. Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Labarin da ke yayata cin tarar daliban labari ne na bogi. Domin karanta cikakkiyar laari latsa nan

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar: Ba a Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya Ba

Masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ranar 7 ga watan afrilu sun kuma gano wani labari da ya janyo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafin Twitter. Labarin ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kebe a mataimakin Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya DIG Moses Jitoboh dan shekaru 52 a gefe guda inda ya nada Usman Alkali Baba dan shekaru 57 a matsayin sabon Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya.

Labarin ya kara da cewa DIG Jitoboh yana gaba da Usman Alkali a matsayi kuma an nada Alkalin ne dan tabbatar da cewa Musulmi kuma dan arewacin Najeriya ne ya hau mukamin Sipeta Janar din.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa DIG Moses Jitoboh baya gaban DIG Usman Alkali a mukami.

Binciken CDD din ya kara gano cewa Usman Alkali Baba wadda yanzu shine sabon Sipeta Janar din Yan Sandan Najeriya ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar ra 1988 yayin DIG Jitoboh ya fara aikin dan sanda a 1994. A kwanan baya ne DIG Jitoboh ya samu mukamin mataimakin Sipeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya.

Da yake maida martani kan batun, mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya ce labarin da ake yadawa cewa an yiwa DIG Jitoboh ritaya da aiki labari ne na karya. Domin karin bayani latsa nan

Minista Sadarwa Bai Ce Rashin Yin Rijistar NIN Zai Janyo Daurin Shekaru 14 a Gidan Yari Ga Mutane Ba

Masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da tarin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani suka wallafa. Labarin ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargadi jama’a game da fuskantan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari idan suka gaza yin rijistar NIN.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Pantami ya furta hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da sashin yada labarai na fadar shugaban kasa ya shirya ranar Alhamis din da ta gabata.

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin.

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin. Domin karin bayani latsa nan

Shugaban Kamfanin Kera Ababen Hawa na Innoson Wato Innocent Chukwuma Bai Mutu Ba!

A ranar 4 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani shafin yanar gizo ya wallafa inda ya ce, shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wadda kuma shine shugaban kungiyoyin fararen hula na Najeriya, Innocent Chukwuma ya mutu.

Shafin yanar gizon ya bayyana cewar abokan Chukwuma ne suka ayyana rasuwar tasa bayan yayi fama da rashin lafuyar da ke alaka da sankarar jini.

Binciken CDD ya gano cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba kamar yadda shafin yanar gizon ya rawaito.

Har wayau, CDD ta gano cewa Chief Innocent Ifediaso Chukwuma bai taba kasancewa shugaban kungiyoyin fafaren hula na Najeriya ba, hasalima shi dan kasuwa ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an tafka kuskure wajen bayyana rasuwar daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafaren hula na Najeriya kuma Daraktan Ford Foundation West Africa, Innocent Chukwuma wadda ya mutu ranar 3 ga watan Afirilun shekara ta 2021. Domin Karin bayani latsa nan

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafa su

 1. bill gates bai ce maganin cutar korona zai canza kwayoyin halittar danadam ba
 2. joe biden bai umarci hukumar shigi da ficin amurka ta bada izinin aiki da zama ta yanar gizo ga yan najeirya ba
 3. gwamnatin tarayya ba ta saye manhajar whatsapp ba
 4. sheikh sharif ibrahim saleh bai soki dakatar da abduljabbar nasiru kabara daga waazi a kano ba

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Salim Sani Zakariyya Ba Dan Boko Haram Bane

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 12 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarain na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani jawabi da wani mai amfani da shafin Twitter mai lakabin @UchePOkoye ya wallafa. Jawabin na dauke da hoton Salim Sani Zakariyya kuma anga wani rubutu a jikin hoton kamar haka: “Dan Boko Haram Da Ake Nema Ruwa-a-Jallo”.

Wannan jawabi da shi Uche P. Okoye ya wallafa akan Salim Sani Zakariyya na danganta shi da Boko Haram ya biyo bayan gargadi ne da Salim din ya yi masa game da yada labaran karya jim kadan bayan shi Okoyen ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami yan cikin jerin yan ta’adda da Amurka ke nema.

Okoye ya wallafa labarin da aka yi ta yama-didi akansa da wata jaridar yanar gizo mai suna NewsWireNGR ta wallafa cewa Isa Ali Pantami na cikin yan ta’addan da kasar Amurka ke nema saboda alakar sa da wadda ya assasa kungiyar Boko Haram, marigayi Mohammed Yusuf.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Salim Sani Zakariyya bashi da alaka da kungiyar Boko Haram. Binciken ya kara gano cewa Salim Sani Zakariyya baya cikin jerin wadan da Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa a matsayin yan Boko Haram da take nema, wannan kuma kai tsaye yana karyata ikirarin da Mr. Uche yayi wa Salim din a jawabin day a wallafa a shafin sa na Twitter.

Zuzzurfan nazarin da CDD ta kara aiwatarwa ya gano cewa Mr.Okoye (@UchePOkoye) ya samu hoton Salim ne daga shafin Twitter na Salim din inda ya yi rubutu ajikin hoton day a zayyana shi Salim a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Da CDD ta tuntube shi, Salim Sani Zakariyya ya ce ya yi mamakin abinda Mr. Okoye ya yi masa dan kawai ya gargade shi kan yada labaran bogi.

Salim yace: “nayi mamaki yadda aka dauki hoto na kuma aka yi rubutu ajikin sa tare da bayyana ni a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, lallai wannan rashin adalci ne karara kuma abin takaici, abinda ya janyo haka shine gargadin da na yiwa shi Mr. Okoye game da yada labarin da bashi da tabbacin sa”

“Ganin cewa labarin da ya wallafa labari ne na bogi sai nayi tsokaci inda naja hankalin sa game da hakan amma kawai sai ya dauki hoto na rubuta cewa ni dan Boko Haram ne kuma ya yada a shafin sa”.

Kammalawa:

Wani hoto da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani da ke bayyana Salim Sani Zakaraiyya a matsayin dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo hoto ne na bogi.

Wanda ke cikin hoton, Salim Sani Zakariyya ba dan Boko Haram bane, hoton sa kawai aka dauka a shafin Twitter akayi rubutu bayan ya janyo hankalin wani mai amfani da shafin “Uche P. Okoye (@UchePOkoye) game da yada labaran bogi.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar: Ba a Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar 7 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da ya janyo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafin Twitter. Labarin ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kebe a mataimakin Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya DIG Moses Jitoboh dan shekaru 52 a gefe guda inda ya nada Usman Alkali Baba dan shekaru 57 a matsayin sabon Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya.

Labarin ya kara da cewa DIG Jitoboh yana gaba da Usman Alkali a matsayi kuma an nada Alkalin ne dan tabbatar da cewa Musulmi kuma dan arewacin Najeriya ne ya hau mukamin Sipeta Janar din.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa DIG Moses Jitoboh baya gaban DIG Usman Alkali a mukami.

Binciken CDD din ya kara gano cewa Usman Alkali Baba wadda yanzu shine sabon Sipeta Janar din Yan Sandan Najeriya ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar ra 1988 yayin DIG Jitoboh ya fara aikin dan sanda a 1994.

A kwanan baya ne DIG Jitoboh ya samu mukamin mataimakin Sipeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya.

Da yake maida martani kan batun, mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya ce labarin da ake yadawa cewa an yiwa DIG Jitoboh ritaya da aiki labari ne na karya.

Har wayau da yake yiwa CDD Karin bayani, mai magana da yawun hukumar kula da ayyukan yan sanda, Ikechukwu Ani yace har zuwa ranar 9 ga watan Afirilun da muke cikin DIG Jitoboh yana na baki aiki.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewa labarin da ake yadawa cewa DIG Moses Jitoboh yafi Usman Alkali wadda yanzu ya zama Sipeta Janar din Yan Sanda karya ne. Har wayau labarin da ke cewa Usman Alkali yana kasan DIG Jitoboh ne aka dakko shi aka nada shi mukamin Sipeta Janar karya ne.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Hukumar Hisbah a Jahar Kano Bata Ci Tarar Daliban Jami’ar Bayero N20,000 Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar 6 ga watan Afirilun shekara ta 2021, wani ya bulla daga kafafen yada labarai na yanar gizo da yawa. Labarin ya ce Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su sakamakon kama su da laifin zama a daki daya duk da kasancewar sub a ma’aurata ba.  Majiyoyi sun hada da: Sahara ReportersTori.ngKanyiDailyNigerDeltaConnectNaijaNewsAllSchoolsForum.

Labarin ya ce: “Hukumar Hisbah a Jahar Kano ta Bukaci Daliban Jami’ar Bayero Maza da Mata Su Biya N20,000 Dan Yin Belin Kansu Bayan Aikata Laifin Zama a Daki Guda”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan labarin cin tarar daliban da aka ce Hukumar Hisba a jahar Kano tayi karya ne. Tun farko majiyoyi da yawa rawaito cewa Hisbah ta damke daliban ne sakamakon zama a daki daya duk da kasancewar su ba ma’aurata ba, sakamakon haka a cewar labarin Hisbah taci tarar daliban naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su.

Da yake yiwa CDD bayani akan batun, mai magana da yawun Hukumar Hisbah ta Jahara Kano, Lawan Ibrahim Fagge ya bayyana labarin a matsayin na bogi, ya kara da cewa Hukumar Hisbah bata ci tarar kowa ba.

Fagge ya ce Hisbah ba kotu bace, dan haka bata cin tarar mutane.

Lawan Ibrahim Fagge ya kara da cewa: “wannan labari ne na karya, Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Jama’ar da ke rayuwa a inda daliban suke ne suka tuntubi Hukumar Hisbah game da yadda daliban Musulmai ke rayuwa a daki daya kuma ba ma’aurata bane, daga nan sai Hisbah ta gana da daliban tare da basu shawara game da rashin dacewar hakan”

“abinda Hisbah tayi shine ganawa dasu tare da yi musu nasiha da basu shawara amma kawai sai ga labari ya bulla cewa wai mun kama tare da cin tarar daliban, wannan karya ne. Babu tarar wadda muka ci”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna zama a daki daya naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su karya ne. Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Labarin da ke yayata cin tarar daliban labari ne na bogi.

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Minista Sadarwa Bai Ce Rashin Yin Rijistar NIN Zai Janyo Daurin Shekaru 14 a Gidan Yari Ga Mutane Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 2 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da tarin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani suka wallafa. Labarin ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargadi jama’a game da fuskantan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari idan suka gaza yin rijistar NIN.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Pantami ya furta hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da sashin yada labarai na fadar shugaban kasa ya shirya ranar Alhamis din da ta gabata.

Gaskiyar Al’amari:

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin.

CDD har wayau ta gano cewa Pantami ya ce mafiya yawan yan Najeriya basu mallaki lambar NIN ba said a batun rufe layukan waya ya taso.

A jawabin da Pantami ya gudanar a taron manema labarai da CDD ta samu kwafin sa daga shafin YouTube na Channels TV, Pantamin ya ce: “mallakar shedar dan kasa doka ce kuma dole akan kowa”.

Da yake kara bayani kan dokar da kuma yawan shekarun ta, Pantami ya ce aiwatar da wasu al’amura ba tare da mallakar lambar NIN ba saba doka ne.

Pantami ya ciga ba da cewa: “laifi ne mutum ya mallaki katin zabe idan bashi da lambar NIN bisa hurumin sashi na 27 na dokar NIMC. Laifi ne mutum ya bude asusun ajiya a banki ba tare da lambar NIN ba.

“Haka nan biyan haraji ba tare da wannan lamba ba laifi ne, laifi ne ma mutum ya karbi pancho ba tare da mallakar NIN ba. Cin gajiyar gwamnati ta kowace hanya ba tare da mallakar NIN ba laifi ne. Sashi na 29 ya ce duk wanda yayi da daga cikin wadannan al’amura da  sashi na 27 yayi magana akan su ba tare da mallakar katin shedar dan kasa na ba ya aikata laifin da ka iya janyo masa cin tara ko zama a gidan yari ko ma duk hukunci guda biyun, wannan hukunci kuma tsawon shekaru 14 ne”, inji Pantami.

Karin binciken CDD ya gano cewa wannan doka da Pantami yayi magana akanta an samar da ita ne tun shekara ta 2007 lokacin da aka kirkiri hukumar katin dan kasa NIMC. Bayan cece-kucen da maganar tasa ta janyo, Pantami yayi magana ta shafin sa na Twitter inda ya bukaci yan jarida da su fitar muryar sa suka nada tare da bayyana cewa basu rawaito abinda ya fada daidai ba.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ya gargadi yan kasa kan mallakar lambar NIN ko su fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 na cike da rudani kuma an jirkita shi.

Nazarin da CDD ta gudanar ya gano cewa Ministan yayi magana ne akan abinda hurumin doka ya fada game da lambar dan kasa da kuma tsawon shekarun da dokar ta kwashe tun bayan samar da ita.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shugaban Kamfanin Kera Ababen Hawa na Innoson Wato Innocent Chukwuma Bai Mutu Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar 4 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani shafin yanar gizo ya wallafa inda ya ce, shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wadda kuma shine shugaban kungiyoyin fararen hula na Najeriya, Innocent Chukwuma ya mutu.

Shafin yanar gizon ya bayyana cewar abokan Chukwuma ne suka ayyana rasuwar tasa bayan yayi fama da rashin lafuyar da ke alaka da sankarar jini.

Acikin wannan labari anyi amfani da hoton dan kasuwa Innocent Chukwuma da kambama labarin kamar yadda za a iya gani a wannan hoto na kasa.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken CDD ya gano cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba kamar yadda shafin yanar gizon ya rawaito.

Har wayau, CDD ta gano cewa Chief Innocent Ifediaso Chukwuma bai taba kasancewa shugaban kungiyoyin fafaren hula na Najeriya ba, hasalima shi dan kasuwa ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an tafka kuskure wajen bayyana rasuwar daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafaren hula na Najeriya kuma Daraktan Ford Foundation West Africa, Innocent Chukwuma wadda ya mutu ranar 3 ga watan Afirilun shekara ta 2021.

Kodayake sunayen su nada kamanceceniya amma mutane ne guda biyu mabanbanta. Shi Innocent Chukwuma darakta ne na Ford Foundation West Africa haka nan daya daga cikin jagororin kungiyoyin fararen hula na Najeriya yayin da Chief Innocent Ifediaso Chukwuma ya ke shugaban kamfanin kera ababen hawa da a turance ake kira Vehicle Manufacturing Company Limited.

Kammalawa:

CDD na tabbabatr da cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba. Labarin da wani shafin yanar gizo ya wallafa da ke bayyana rasuwar tasa labari ne mai cike da rudani tare da jirkita fahimta.

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Mujallar Karshen Mako Ta CDD

By Fact Check

A makon karshe na watan Maris din shekara ta 2021, kamar sauran makonnin da suka gabata, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun zurfafa bincike da gano labaran karya da aka wallafa a shafuka daban-daban na sada zumunta, wannan bincike ya kai CDD da gano labaran karya da suka shafi bada izinin zama da daukar yan Najeriya aiki a kasar Amurka. Wani labarin karyar da CDD ta gano shine wadda akace wai shahararren attajirin nan na kasar Amurka wato Bill Gates ya ce maganin cutar Korona yana jirkita kwayoyin halittar dan’adam.

Wani abin jin dadi shine CDD tabi diddigin wadannan labarai kuma ta gano cewa dukkannin su labarai ne na karya. Ku karanta wannan tantancewa da CDD ta aiwatar kan wadannan labarai:

Shugaba Joe Biden Bai Umarci Hukumar Shigi da Ficin Amurka Ta Bada Izinin Aiki Da Zama Ta Yanar Gizo Ga Yan Najeirya Ba

Akwai wata sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da suka hada da manhajar WhatsApp da ke cewa Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya bada umarnin daukar yan Najeriya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardar izinin zama a kasar ta Amurka.

Sanarwar wadda aka yi ikirarin cewa wani bangare na takardar da aka rabawa manema labarai ance ta fito ne daga ofishin da ke kula da yan kasar Amurka da harkokin shigi da fici kuma Shugaba Biden ya sanyawa dokar dake bada izini dan daukar yan Najeirya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardun izinin zaman kasar Amurka

A cewar wannan sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani an mika kwafin wannan takardar sanarwa ga ofishin jekadancin Najeriya da ke Amura kuma ranar da za a rufe neman daukar aikin tare da bada izinin zama a kasar ta Amurka ga yan Najeirya itace 30 ga watan Afirilu, 2021.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan shafin yanar gizo na ofishin kula da yan kasar Amurka da shigi da fici U.S Citizenship and Immigration Services ya gano cewa babu wata sanarwa da ta fito daga wannan ofishi.

Wata alama da ke bayyana cewa sanarwar ta bogi itace sanarwar tana kunshe da kura-kuari masu yawan gaske haka nan babu wata hujjar cewa Shugaban Amurka Joe Biden ya saka hannu domin bada izini dan daukan yan Najeriya ta hanyar yanar gizo ko wani izinin zama ga yan Najeriya din a wannan lokaci.

Har wayau ofishin jekadancin Amurka da ke Najeriya ya yi watsi da sanarwar ta cikin wani bayani da ya wallafa a amintaccen shafin sa na Twitter (@USinNigeria). Ofishin ya bayyana cewa sanarwar sanarwa ce ta bogi da aka tsara dan damfarar jama’a. Karanta cikekken labarin anan

Bill Gates Bai Ce Maganin Cutar Korona Zai Canza Kwayoyin Halittar Dan’adam Ba

Wani rahoto da Principia Scieitific suka wallafa a watan Disamban shekara ta 2020 yayi ikirarin cewa anga babban attajirin nan na kasar Amurka, wato Bill Gates acikin wani faifan bidiyo yana cewa maganin cutar Korona zai sauya kwayoyin halittar dan na did-din-din. Bidiyon wadda aka wallafa shi an kalleshi sau dubbai haka nan an sake wallafa shi a shafin YouTube.

Gaskiyar Al’amari:

Labarin da ke ikirarin cewa Bill Gates ya ce maganin cutar Korona zai jirkita kwayoyin halittar dan’adam karya ne.

Nazarin da aka gudanar kan bidiyon ya gano cewa bidiyon da Principia Scientific din suka wallafa an jirkita shi kuma yanzu haka jirkitaccen ne yake yaduwa a tsakankanin yan Najeriya.

Mazanarta da bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano sahihin bidiyon da Bill Gates din yake magana game da magunguna kuma an wallafa wannan bidiyon a shafin Bill Gates din mai suna Gates Notes dama dandalin san a YouTube wadda aka yiwa lakabi da  YouTube channel. Binciken CDD din ya gano cewa bidiyon Bill Gates din na asali ya mai tsawon minti biyu da dakika ashirin da tara ya fuskanci sauye-sauye da gyaer-gyare dan jirkita bayanin asalin da ke cikin sa da manufar sauya ma’anar sa.

Binciken CDD din har wayau ya gano cewa bidiyon da ake yadawa din mai tsawon 1:37 an yanko shine daga bidiyon asalin mai tsawon 1:50. Samu Karin bayani anan

Bill Gates Bai Ce Maganin Cutar Korona Zai Canza Kwayoyin Halittar Dan’adam Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

Wani rahoto da Principia Scieitific suka wallafa a watan Disamban shekara ta 2020 yayi ikirarin cewa anga babban attajirin nan na kasar Amurka, wato Bill Gates acikin wani faifan bidiyo yana cewa maganin cutar Korona zai sauya kwayoyin halittar dan na did-din-din. Bidiyon wadda aka wallafa shi an kalleshi sau dubbai haka nan an sake wallafa shi a shafin YouTube.

Gaskiyar Al’amari:

Labarin da ke ikirarin cewa Bill Gates ya ce maganin cutar Korona zai jirkita kwayoyin halittar dan’adam karya ne.

Nazarin da aka gudanar kan bidiyon ya gano cewa bidiyon da Principia Scientific din suka wallafa an jirkita shi kuma yanzu haka jirkitaccen ne yake yaduwa a tsakankanin yan Najeriya.

Mazanarta da bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano sahihin bidiyon da Bill Gates din yake magana game da magunguna kuma an wallafa wannan bidiyon a shafin Bill Gates din mai suna Gates Notes dama dandalin san a YouTube wadda aka yiwa lakabi da  YouTube channel. Binciken CDD din ya gano cewa bidiyon Bill Gates din na asali ya mai tsawon minti biyu da dakika ashirin da tara ya fuskanci sauye-sauye da gyaer-gyare dan jirkita bayanin asalin da ke cikin sa da manufar sauya ma’anar sa.

Binciken CDD din har wayau ya gano cewa bidiyon da ake yadawa din mai tsawon 1:37 an yanko shine daga bidiyon asalin mai tsawon 1:50.

Maganin Cutar Korona na RNA

Tun bayan fara samar da maganin cutar Korona, Cibiyar Takaita Yaduwar Cututtuka da Magance Su ta (CDC) tayi watsi da cece-kucen da akeyi kan cewa maganin cutar Korona yana sauya fasalin kwayoyin halittar dan’adam. Acikin wani bayani da ta wallafa a shafin ta yanar gizo “maganin cutar Korona mRNA ba zai iya sauya kwayoyin halittar dan’adam ta kowace hanya ba.”

CDC ta yi bayanin cewa magungunan Pfizer-BioNTech da Moderna an samar da su ne daga sinadaran mRNA. “wadanan magunguna suna horar da sinadaran jikin mutum yadda za su samar ma’adanan baiwa jiki kwari dan su iya maida martanin kare jiki. Maganin mRNA ba zai iya shiga cikin kwayoyin sinadaran jiki ba wadda kuma a nan ne kwayoyin halittar dan’adam suke. Wannan yana nuna cewa maganin cutar Korona na mRNA bashi da zarafin yin hulda da kwayoyin halittar dan’adam ta kowace hanya. Hasali ma mRNA yana aiki ne garkuwar jikin dan’adam dank are jikin daga barazana da ka iya tasowa.

Wani sabon nazari da ya shafi garkuwar jiki da Frontiers suka gudanar ya gano cewa maganin mRNAs bashi da sinadaran da ka iya jirkita kwayoyin halittar dan’adam.

Kammalawa:

Wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da ke ikirarin cewa attajirin nan dan kasar Amurka, wato Bill Gates yace maganin cutar Korona zai jirkita kwayoyin halittar dan’adam bidiyo ne da aka sauyawa fasali, attajirin bai fadi haka ba.

Haka nan binciken kimiyya ya tabbatar da cewa maganin cutar Korona na mRNA baya jirkita kwayoyin halittar dan’adam.

CDD na karfafawa mutane gwiwa game da bincika sahihancin labarai kafin yada su a kowane lokaci

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Joe Biden Bai Umarci Hukumar Shigi da Ficin Amurka Ta Bada Izinin Aiki Da Zama Ta Yanar Gizo Ga Yan Najeirya Ba

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Akwai wata sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da suka hada da manhajar WhatsApp da ke cewa Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya bada umarnin daukar yan Najeriya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardar izinin zama a kasar ta Amurka.

Sanarwar wadda aka yi ikirarin cewa wani bangare na takardar da aka rabawa manema labarai ance ta fito ne daga ofishin da ke kula da yan kasar Amurka da harkokin shigi da fici kuma Shugaba Biden ya sanyawa dokar dake bada izini dan daukar yan Najeirya aiki ta hanyar yanar gizo tare da basu takardun izinin zaman kasar Amurka

A cewar wannan sanarwa da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani an mika kwafin wannan takardar sanarwa ga ofishin jekadancin Najeriya da ke Amura kuma ranar da za a rufe neman daukar aikin tare da bada izinin zama a kasar ta Amurka ga yan Najeirya itace 30 ga watan Afirilu, 2021.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan shafin yanar gizo na ofishin kula da yan kasar Amurka da shigi da fici U.S Citizenship and Immigration Services ya gano cewa babu wata sanarwa da ta fito daga wannan ofishi.

Wata alama da ke bayyana cewa sanarwar ta bogi itace sanarwar tana kunshe da kura-kuari masu yawan gaske haka nan babu wata hujjar cewa Shugaban Amurka Joe Biden ya saka hannu domin bada izini dan daukan yan Najeriya ta hanyar yanar gizo ko wani izinin zama ga yan Najeriya din a wannan lokaci.

Har wayau ofishin jekadancin Amurka da ke Najeriya ya yi watsi da sanarwar ta cikin wani bayani da ya wallafa a amintaccen shafin sa na Twitter (@USinNigeria). Ofishin ya bayyana cewa sanarwar sanarwa ce ta bogi da aka tsara dan damfarar jama’a.

Bayanin ofishin jekadancin Amurkan ya kara da cewa: “Ayi hankali da aikin yan damfara! Mazambata da yan damfara na yada wata sanarwar bogi da ke ikirarin bada sabon izinin zama da yin aiki a Kasar Amurka ga yan Najeriya da ke tsakanin shekaru 40 zuwa 55. Wannan tsohuwar sanarwa ce ta bogi wadda aka canzawa fasali, ku kula da kyau kada a zambace ku!”-inji bayanin da ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Tun bayan kama aiki, sabon Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu kan dokoki da dama da suka shafi harkokin shigi da fici na tsohon Shugaba Donald Trump.

Yana da kyau a sani cewa babu daya daga cikin dokokin da Shugaba Biden ya sanyawa hannu da ta shafi daukar yan Najeriya aiki ta hanyar yanar gizo ko basu izinin zama a Amurka.

Kammalawa:

Shugaban kasar Amurka Joe Biden bai bada umarnin bada izinin zama dan yin aiki a Amurka ta hanyar yanar gizo ba. Wata sanarwa da ake yadawa ta kafafen sada zumunta na zamani da ke ikirarin haka sanarwa ce ta bogi.

CDD na tabbatar da cewa wannan sanarwa wasu yan damfara ne suka tsara ta dan zambatan yan Najeriya, dan haka jama’a suyi watsi da ita.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Gwamnatin Tarayya Na Bada Tallafin N30,000 a Zango Na Biyu Na Bullar Cutar Korona?

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Karya Ne

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 18 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai dan gano sahihancin sun a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani da ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Labarin na cewa yanzu haka gwamnatin tarayya na bada tallafin N30,000 ga jama’a a matsayin tallafi rage radadin da cutar Korona ta haifar a wannan zagaye na biyu da cutar ke kunno kai.

A cewar labarin, za a rika baiwa yan Najeriya naira dubu talatin kowane sati dan cigaba da rayuwa acikin wannan zango na biyu na cutar ta Korona.

Wani bangare na labarin yace: “ku gaggauta dan samun tallafin cigaba da rayuwa na N30,000. Acikin dakiku kadan za ku cika fom din neman wannan tallafi. Ku hanzarta kada ku rasa wannan dama”. An samar da wani adireshin yanar gizo da aka ce shine za a latsa dan cika fom din.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin sun a CDD suka gudanar ya gano cewa ikirarin da labarin yayi cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin naira dubu talatin duk sati ga jama’a karya ne.

Binciken har wayau ya gano cewa adireshin yanar gizon da aka bayar acikin labarin adireshi ne na bogi da ke yiwa tarko. Yan damfara ne suka tsara labarin dan zambatan jama’a. idan mutum ya latsa adireshin zai yadda aka wallafa wasu hotuna da nufin daukar hankali da kokarin gaskatawa mutane batun tallafin wadda kuma karya ne.

Bayan kusan kamala bada bayanai acikin shafin, za a bukaci mutum ya dakata ya sanar da akalla wasu mutanen goma kafin ya cigaba, wannan kuma wata alama ce day an damfara ke amfani da ita yaudarar jama’a.

Karin binciken na CDD ya gano cewa, sahihiyar majiyar da ke bada bayanai kan tallafin gwamnatin tarayya kan cutar Korona a karo na biyu itace survivalfund.gov.ng, a wannan shafi ne kadai mutane za su samu gamsassun bayani kan tallafin rage radadin cutar Korona a zagaye na biyu.

Kammalawa:

Wani labari da sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin naira dubu talatin duk sati ga yan Najeriya a matsayin daukin zagayen cutar Korona karo na biyu karya ne.

Adireshin yanar gizon da aka samar ajikin sakon adireshi ne na bogi kuma yan damfara ne suka samar dashi dan zambatan jama’a.

CDD na kira ga jama’a da suyi watsi da labarin tare da daina yadashi.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Ranar 15 ga Watan Maris, 2021 Mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala Ya Rasu?

By Fact Check

Gaskiyar Al’amari: Akwai Rudani Cikin Labarin

Tushen Magana:

A ranar 15 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bin didddigin labarai dan gano sahihancin su Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da majiyoyi da Punch da ABN suka wallafa, majiyoyin sunyi ikirarin cew Farfesa Chukwuma Okonjo, wato mahaifin daraktar hukumar cinikayya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ya rasu.

Haka nan rahotanni sun bayyana cewa wata sanarwa da Dr. Ngozi ta fitar a madadin iyalanta  ta bayyana cewa baban ta, wadda shine mai ya rike sarautar Obi na Ogwashi-Uku na baya-bayannan a jahar Delta ya mutu ranar 15 ga watan Maris, 2021.

Sanarwar ta kara da cewa Farfesa Okonjo ya mutu yana mai shekara 91 a garin Legas jim kadan da dawowar sa daga kasashen Amurka da Ghana.

A screenshot from the published report on ABN

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin mutuwar Farfesa Chuwkuma Okonjo a ranar 15 ga Maris, 2021 din yana cike da rudani.

Tsohon basarake wadda ya rike mukamin Obi na Ogwashi Ukwu a jahar Delta ya mutu ne ranar 13 ga watan Satumban 2019 yana dan shekaru 91 a garin Legas.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa sanarwar mutuwar marigayi Farfesa Okonjo wadda mai taimakawa Dr. Okonjo-Iwela ta fannin hulda da jama’a da yada labarai, Paul C. Nwabiukwu ya sanyawa hannu a ranar 13 ga watan Satumban 2019 ta tabbatar da cewa mahaifin Iwealan ya mutu ne shekaru biyu da suka gabata, ba cikin shekarar 2021 ba.

CDD ta gano cewa lokacin da mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ya rasu ba a nada mukamin daraktar hukumar cinikayya ta duniya ba.

Kammalawa:

Binciken CDD ya gano cewa labarin da kafafen yada labarai suka rawaito cewa Farfesa Chukwuma Okonjo, wato mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ya mutu ranar 15 ga Maris din 2021 yana cike da rudani.

Mahaifin Dr. Ngozin ya mutu ne ranar 13 ga watan Satumban 2019 ba ranar 15 ga watan Maris din 2021 ba kamar yadda majiyoyi da dama suka rawaito.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin Wani Kansila a Jahar Kano Ya Nada Mutane 18 a Matasyin Masu Taimaka Masa?

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Eh, Gaskiya Ne.

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 12 ga watant Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da mai amfani da shafin Twitter mai lakabin @UncleAnass ya wallafa wani tsokaci day a bayyana cewa wani zababben kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka a bangarori daban-daban. Tsokacin ya ce Kansilan ya nada mai taimaka masa a bangaren al’amuran addini da siyasa da kungiyoyin sakai da bada dauki, dama sakatare na musamman ga Kansilan.

Tsokacin wanda @UncleAnass ya wallafa shi ya ce: “abinda dariya: wani Kansila a Kano ya nada mataikama 18 da suka hada da mai taimaka masa a wasu kebabbun al’amura, da mai taimaka masa ta bangaren addini da siyasa, da harkokin sakai, da bada dauki, da mataimaki a bangaren kafafen sada zumunta na zamani”

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar game da maganar cewa wani Kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka masa ya gano cewa gaskiya Kansila ya nada mutanen 18 a matsayin mataimaka a gare shi.

Kansilan, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda ke wakiltar mazabar Guringawa a karamar hukumar Kumbutso da ke kewayen birnin Kano , a jahar Kano ya tabbatar wa CDD nadin mutane 18 din a matsayin mataimaka a gare shi.

A wata sanarwa da ya fitar kuma CDD ta samu kwafin ta ranar 11 ga watan Maris din shekara ta 2021, Hon. Muslihu ya zayyano sunayen mutane da bangarorin da za su taimaka masan.

Da yake karin bayani wa CDD akan batun, Hon. Muslihu ya ce kodayake babu hurumin nada mataimaka ga ofishin kansila acikin tsarin mulki, amma yayi nadin tunda tsarin mulkin bai hana ba duk da kuwa bai ce ayi ba, kuma za a rantsar da mataimakan nasa nan gaba.

Muslihu ya ce: “to, banyi wannan nadi dan janyo hankalin jama’a kaina ba ko dan kokarin zama daban acikin yan uwana kansiloli ba, nayi haka ne kawai dan haskawa al’umma cewa ana iya amfani da kujerar siyasa dan aiwatar da ayyuka bisa ka’ida da kamanci ko da kuwa babu hurumin acikin kundin tsarin mulki”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa wani kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka masa a bangarori daban-daban gaskiya ne.

Kansilan, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda ke wakiltar mazabar Guringawa da ke karamar hukumar Kumbotso da ke kewayen birinin Kano ya tabbatar wa CDD nadin mutane 18 din.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Bai Soki Dakatar Da Abduljabbar Nasiru Kabara Daga Wa’azi a Kano Ba!

By Fact Check

A ranar Alhamis, 4 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata murya mai tsawon minti 9 da dakika 27 da aka nada kuma ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Acikin muryar anyi dogon sharhi tare da sukar dakatar Malam Abdujjabar Nasiru Kabara daga gabatar al’amuran wa’azi a jahar Kano sakamakon cece-kuce da maganganun sa suka janyo. Wata gabatarwa da ake yadawa da muryar tace Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ya yi wannan jawabi.

Acikin muryar anjiyo wani mutum na cewa: “bisa ga bayanan da muke dasu gwamnatin Kano ta rufe inda Abduljabbar ke gudanar da al’amuran wa’azi, wannan ya faru ne bayan taron dangi da malaman Darika, Sunna da sauran mazhabobi suka yi masa”

Mai sharhin ya ci gaba da cewa: “hanyar da malaman suka bi abinda dariya da kunyata kai ne, kuma dukkan mai hankali zai fahimci hakan tare da gane irin rashin adalci da aka yi masa saboda an gyara maganganu da ya yi din”

Gaskiyar Al’amura:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa muryar da ake yadawa ta manhajar WhatsApp din ba ta Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussain ba ce. Hasalima Sheikh bai yi magana akan batun dakatar Abduljabbar ba balle ya soki al’amarin.

Da CDD ta tuntubi da ga Sheikh Shariff Saleh, wato Engr. Almuntasir Ibrahim Saleh Alhaussain ya bayyana cewa muryar da ake yadawa din ba ta mahaifin sa ba ce.

Almustasir ya kara da cewa mahaifin sa bai yi tsokaci kan batun dakatar da Abduljabbar din ba,

Almuntasir y ace: “lallai na saurari muryar da ake yadawa sosai ta manhajar WhatsApp, kuma ina bada tabbacin cewa muryar ko sakon da take dauke dashi baya bayyana ra’ayin Maulana Sheikh Ibrahim Saleh Alhussain ta kowace hanya”.

Kammalawa:

Wata murya da ake yadawa ta manhajar WhatsApp inda aka jiyo wani mutum yana sukan dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara daga gabatar da wa’azi a jahar Kano tare da ikirarin cewa murya ce ta Sheikh Sharif Ibrahim Saleh murya ce ta bogi. Binciken CDD ya gano cewa ba muryar Shehin Malamin ba ce.

Bayanan da CDD ta tattara sakamakon bincken da ta gudanar akan batun sun nuna cewa Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhsussain bai yi magana kan batun ba.

CDD na kira ga jama’a da suyi watsi da muryar tare da daina yadata.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Gwamnatin Tarayya Ba Ta Saye Manhajar WhatsApp Ba

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar 10 ga watan Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin sun a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sako da aka wallafa a shafin Facebook da ke ikirarin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta saye manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajen turawa da karbar sakonni.

Sakon da aka wallafa din ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta saye manhajar ne akan kimanin kudi biliyan uku (kodayake ba a bayyana biliyan ukun na nau’in wane kudi bane).

Sakon ya kara da cewa masu amfani da manhajar su gaggauta barin amfani da ita dan komawa yin amfani “Signal App” saboda a cewar sakon gwamnatin Najeriya za ta ci gaba das aka ido akan abinda mutane ke yi a manhajar ta WhatsApp.

Wani bangare na sakon yace: “Za a rika bin diddigin abinda kake yi! Daina amfani da WhatsApp yanzu-yanzu! Fara yin amfani da Signal App yanzu! Signal App baya bada damar sa ido akan abinda kakeyi”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin Najeriya ba ta saye manhajar WhwatsAppm din ba kamara yadda akayi ikirari.

Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa sakon da wanda wani mai lura da wani shafin Facebook mai suna “Best of Mazi Nnamdi Kanu”  ya wallafa shi dandalin Facebook din ya riga ya aiyana shi a matsayin labarin bogi.

Shafin Facebook a martanin da ya mayar game da sakon bogin da aka wallafa din yace tuni wasu masu tantance sahihancin bayanai masu zaman kansu sun tantance shi kuma sun gano cewa karya ne.

Wani karin binciken da zurfafa ya gano cewa, kamfanin sada zumunta da muhawarar na Facebook a martanin day a mayarwa kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana sakon a matsayin na karya.

Ba zai yiwu Facebook su sayar da kamfanin da ta samar dashi akan zabar kudi dala biliyan goma sha tara da digo uku ($19.3 billion), da ke da mallakar hannun jari da kudin su yakai dala biliyan sha biyu ($12 billion), abu ne da bazai yiwu ba ace an sayar dashi akan naira biliyan uku (3BN)  kacal ga gwamnatin Najeriya.

Yana da kyau a sani cewa a halin yanzu idan za a sayar da WhatsApp zai kai tsabar kudi dala biliyan dari biyar ($500 billion), dan haka babu ta yadda za a sayar dashi a naira biliyan uku kacal.

Alamu na nuna cewa wanda ya wallafa sakon ka iya zama masoyi ga Nnamdi Kanu, mai fafutukar neman kirikiro kasar Biafra wadda magoya bayan suka kware wajen yada labaran karya.

Kammalawa:

Bayan gudanar da zuzzurfan bincike, CDD na tabbatar da cewa gwamnatin Najeirya ba ta saye manhajar WhatsApp ba kamar yadda wani sakon da aka yada a wasu shafukan sada zumunta na zamani ya bayyana.

CDD na jan hankalin jama’a game da yin nazari da tantance sahihancin sakonni da labarai kafin yada su ga sauran jama’a.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Labaran Karya da CDD ta Gano a Makon Farko na Watan Maris Shekara ta 2021

By Fact Check

A wannan satin, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ta bankado tare da binciko gaskiyar wasu labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter da manhajar WhatsApp. Ga labaran nan kamar yadda wannan mujalla ta mu ta wallafa su:

Hoton Da aka Ga Shanu Na Cin Timatir a Gefen Hanya Ba a Najeriya aka Dauke Shi Ba!

Wata mai amfani da dandalin Facebook mai suna Amanda Chisom ta wallafa wani hoto da ya nuna wasu shanu na cin tumatir mai tarin yawan gaske da ke jibge a gefen hanya. Hoton ya alamta cewa an dauke shi ne a arewacin Najeriya kuma shanun na cin tumatir din ne sakamakon dakatar da kai kayan abinci kudancin kasar najeriya.

Bincike da masu tabbatar da sahihanci labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ya gano cewa, tarin tumatir din da aka gani shanu suna ci a gefen hanya ba a Najeriya aka dauke shi ba. Hasali ma, Funny, wani shafin yanar gizo da ke kasar India ne ya fara wallafa hoton ranar 30 ga watan Yulin shekara ta 2017. Domin karanta cikekken labarin, latsa nan

Shin Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Titin Zuwa Filin Jirgin Saman Abuja Ranar 4 Ga Maris, 2021?

A ranar 5 ga watan Maris, shekara ta 2021 wadan su kafafen sada zumunta na zamani sun wallafa wani bidiyo tare da yin ikirarin cewa matasan Najeriya sun toshe titin zuwa filin jirgin sama da ke garin Abuja, daidai gadar Dantata, sun kuma dakatar zirga-zirgar jiragen sama tare da tsayar da al’amura cak a garin na Abuja. Bidiyon an kara yada shi a manhajar WhatsApp da taken: zanga-zangar Lekki Toll Gate na maimaita kanta a garin Abuja.

Binciken da CDD ta gudanar, ya gano cewa bidiyon da aka yadawa din, watan sa biyar da dauka. Hasalima an dauki bidiyon ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 2020 lokacin gudanar da zanga-zangar #EndSARS da ke hankoron kawo karshen ikirarin cin zarafin mutane da yan sanda keyi a Najeriya..

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa, lallai anyi zanga-zanga a garin Abuja a ranar 4 ga watan Maris din shekara ta 2021 wadda wasu mutane da ke neman Shugaba Buhari yayi murabus suka aiwatar. Domin karanta cikekken labarin, latsa nan.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568.

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafawa

 1. ba a kori fulani a jahar kano ba
 2. babu wani tsarin bada tallafi daga gidauniyar dangote
 3. shin who ta sauya matsayin ta game da killace kai da bada tazara
 4. bill gates bai ce zaa sake samun wata annoba bayan cutar korona ba

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Labaran Karya da CDD ta Gano a Makon Karshe na Watan Fabrairun Shekara ta 2021

By Fact Check

Hakika illolin labaran karya ko labaran bogo a fili suke. Labaran karya na iya haifar da rudani da tashin hankali dama jefa mutane cikin zulumi. Da alama masu kirkira da yada labaran bogi na cin kare su ba babbaka musamman a kafafen sada zumunta na zamani, ta yadda suke yada wadan nan labarai ta fuskoki daban-daban. Yada ire-iren wadan nan labarai na bogi musamman a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter, YouTube, Instagram dama WhatsApp a bune mai sauki amma mai cike da illoli ko matsaloli. Kokarin kare faruwar matsalolin da labaran karya za su iya haifarwa yasa Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ke bin diddigin labarai dan gano gaskiyar su da nufin fahimtar da al’umma. Wannan mujalla za ta gabatar muku da wasu labaran da CDD ta bankado.

A wannan satin, cibiyar demokradiyya da cigaba ta bankado tare da binciko gaskiyar wasu labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook da manhajar WhatsApp. Ga labaran nan kamar yadda wannan mujalla ta mu ta wallafa su:

Ba a Kori Fulani a Jahar Kano Ba!

A ranar Laraba, 24 ga watan Fabrairun shekara ta 2021,masu bincike na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani bidiyo da ake yadawa a manhajar WhatsApp. Bidiyon na ikirarin cewa jama’ar jahar Kano sun umarci al’ummar Fulani da subar jahar ta Kano dama arewacin Najeriya baki daya.

Dubiya da CDD ta yi, an gano cewa wannan labari ne na bogi. Hasali ma bidiyon an dauke shi ne lokacin wata hatsaniya da ta faru a garin Billiri da ke jahar Gombe. Hatsaniyar ta barke ne tsakanin wasu kabilu sakamakon takaddama game da nadin basaraken gargajiya da ake yiwa lakabi da “Mai Tangale” bayan rasuwar wadda ke kan mukamin. Latsa nan dan karanta cikekken labarin.

Shin WHO Ta Sauya Matsayin Ta Game Da Killace Kai da Bada Tazara?

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

A ranar alhamis, 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba, sun gano labari da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sauya matsayin ta game da ka’idojin kare kai daga kamuwa da cutar Korona.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin da ake yadawa game da WHO cewa mutanen da suka kamu da cutar Korona basa bukatar killace kansu karya ne.

Hukumar WHO bata ce mutanen da ke dauke da cutar Korona basa bukatar killace kansu ba. Wannan labarin hasalima an taba yadashi a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2020 inda mutane da dama sukayi ta cece-kuce akansa. Domin karanta cikekken labarin latsa nan

Babu Wani Tsarin Bada Tallafi Daga Gidauniyar Dangote

Wani sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke cewa Gidauniyar Aliko Dangote na bada tallafin kudi ga yan Najeriya masu sa’a dan fara sana’o’i a shekara ta 2021 sako ne na bogi. Yan damfara kan tsara ire-iren wadan nan sakonni da nufin tattara bayanan mutane dan zambatan su a karshe.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi. Domin karanta cikekken binciken da CDD ya gano, latsa nan.

Gwamnatin Jahar Kano Ba Ta Rushe Makarantar Sheikh Abduljabbar Ba!

Labarin da kafafen da yada labarai da yawa suka wallafa cewa gwamnatin jahar Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar karya ne. Ziyarar da CDD takai wurin da akayi rusau din da karin binciken da ta gudanar ya gano babu abinda ya samu makaranta ko masallacin malamin.

CDD na tabbatar da cewa wannan labari ne na bogi dan haka jama’a suyi watsi dashi.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568. Samu karin  bayani anan.

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafawa

 1. babu wani tsarin bada tallafi daga gidauniyar dangote
 2. shafin twitter na bogi da ke alakanta kansa da maaikatar matasa da wasanni ta tarayya
 3. shin gwamnatin tarayya ta amince da yin rijistar nin ta hanyar yanar gizo
 4. gwamnatin jahar kano ba ta rushe makarantar sheikh abduljabbar ba

Domin sauke mujallar mu, latsa nan

Ba a Kori Fulani a Jahar Kano Ba!

By Fact Check

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 24 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani bidiyo da ake yadawa a manhajar WhatsApp, masu yada bidiyon sunyi ikirarin cewa na, jama’ar jahar Kano sun umarci al’ummar Fulani da subar jahar ta Kano dama arewacin Najeriya baki daya.

A jikin bidiyon anga wani rubutu da ke cewa: “Hausawa sun umarci Fulani da su tattara na- su-ya-na-su subar yankin arewacin Najeriya yayin da suka lalata wani Masallaci mallakar Fulanin. Da’awar Shehu Usmanu Danfodio mai tsawon tarihin shekaru 220 ne ta ke aiki yanzu. A cikin bidiyon da ke dauke da wannan magana anga wassu tarin mutane dauke da makamai na shiga cikin wani masallaci tare da lalata abubuwan da ke cikin masallacin.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa bidiyon da ake yadawa din ba a Kano aka nade shi ba. Hakanan ikirarin da akayi cewa Hausa a Kano sun uamrci Fulani da subar garin dama arewacin kasar karya ne.

Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa, bidiyon an dauke shi ne lokacin wata hatsaniya da ta faru a garin Billiri da ke jahar Gombe.

Hatsaniyar ta barke ne tsakanin wasu kabilu sakamakon takaddama game da nadin basaraken gargajiya da ake yiwa lakabi da “Mai Tangale” bayan rasuwar wadda ke kan mukamin, wato marigayi Dr Abdu Buba Maisharu a watan Janairun shekara ta 2021.

Bayan barkewar tarzoma a garin Billirin, Gwamnan Jahar Gomben, Muhammadu Inuwa Yahaya ya dauki aniyar ganowa tare da hukunta wadan da ke da hannu wajen ingiza afkuwar rikicin.

A cewar gwamnan, tashin hankalin ya janyo salwantar ruyuka da dokiya da tasan ma miliyoyin naira.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa jama’ar jahar Kano sun umarci Fulani da su fice daga jahar karya ne. Bidiyon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin korar Fulani daga Kanon dama arewacin Najeriya bidiyo ne da aka dauke lokacin wata hatsaniya da ta barke a garin Billiri na jahar Gombe.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantamce muku sahihancin su ta hanyar turo sakon WhatsApp ko gajeren sako akan lamba +2349062910568 ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Shin WHO Ta Sauya Matsayin Ta Game Da Killace Kai da Bada Tazara?

By Fact Check

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano labari da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sauya matsayin ta game da ka’idojin kare ka daga kamuwa da cutar Korona.

Labarin yace WHO ta ce masu dauke cutar Korona basa bukatar su killace kansu saboda cutar baza ta yadu daga jikin wani mutum zuwa wani ba.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin da ake yadawa cewa WHO mutanen da suka kamu da cutar Korona basa bukatar killace kansu karya ne. Karin binciken CDD din ya gano cewa wannan labari na bogi ba sabo bane, hasalima an taba yadashi a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2020 inda mutane da dama sukayi ta cece-kuce akansa.

CDD har wayau ta kara gano cewa WHO a cikin wani jadawali da ta fitar ta ci gaba da karfafawa mutanen da makusantan su suka kamu da cutar Korona da su bi ka’idojin kare kai kamar su bada tazara yayin mu’amala, das aka takunkumi, da wanke hannaye da ruwa mai gudana da sabulu mai kashe kwayoyin cuta da ido baya iya gani.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewa sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta canja matsayin ta game matakan kare kai daga kamuwa da cutar Korona karya ne. Hukumar bata ce mutanen da ke dauke da cutar Korona basa bukatar killace kansu ba.

CDD na jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu tantance sahihancin su ba.