Shugaban Kamfanin Kera Ababen Hawa na Innoson Wato Innocent Chukwuma Bai Mutu Ba

Tushen Magana:

A ranar 4 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani shafin yanar gizo ya wallafa inda ya ce, shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wadda kuma shine shugaban kungiyoyin fararen hula na Najeriya, Innocent Chukwuma ya mutu.

Shafin yanar gizon ya bayyana cewar abokan Chukwuma ne suka ayyana rasuwar tasa bayan yayi fama da rashin lafuyar da ke alaka da sankarar jini.

Acikin wannan labari anyi amfani da hoton dan kasuwa Innocent Chukwuma da kambama labarin kamar yadda za a iya gani a wannan hoto na kasa.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken CDD ya gano cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba kamar yadda shafin yanar gizon ya rawaito.

Har wayau, CDD ta gano cewa Chief Innocent Ifediaso Chukwuma bai taba kasancewa shugaban kungiyoyin fafaren hula na Najeriya ba, hasalima shi dan kasuwa ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an tafka kuskure wajen bayyana rasuwar daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafaren hula na Najeriya kuma Daraktan Ford Foundation West Africa, Innocent Chukwuma wadda ya mutu ranar 3 ga watan Afirilun shekara ta 2021.

Kodayake sunayen su nada kamanceceniya amma mutane ne guda biyu mabanbanta. Shi Innocent Chukwuma darakta ne na Ford Foundation West Africa haka nan daya daga cikin jagororin kungiyoyin fararen hula na Najeriya yayin da Chief Innocent Ifediaso Chukwuma ya ke shugaban kamfanin kera ababen hawa da a turance ake kira Vehicle Manufacturing Company Limited.

Kammalawa:

CDD na tabbabatr da cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba. Labarin da wani shafin yanar gizo ya wallafa da ke bayyana rasuwar tasa labari ne mai cike da rudani tare da jirkita fahimta.

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa