Shugaba Muhammadu Buhari Bai Mutu Ba!

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban shekara ta 2020, dubban masu anfani da shafin Twitter sun yada labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu. Labaran da maganganun da aka wallafa din an wallafa su ne a karkashi wani shagube mai taken #BuhariIsDead wadda nufin Buhari ya mutu, kuma wannan muhawara ta janyo maganganu da ba’asi masu yawan gaske a shafin na Twitter inda har sai da ya zama batun da yafi kowane batu jan hankali kuma na daya acikin abubuwan da akafi tofa albarkacin baki akansa.

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu tanatce sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ya gano cewa labarin cewa Shugaba Buhari ya mutu karya ne.

Jinkirin Shugaba Buhari na rashin yiwa yan kasa jawabi akan kari game da zanga-zangar #EndSARS ya taimaka wajen fadada jita-jitar cewa ya mutu.

Wata alama dake karyata mutuwar Shugaba Buharin itace yadda aka ganshi ya jagoranci zaman majalisar kasa a jiya Laraba, 21 ga watan Oktoban shekara ta 2020 kodayake baiyi tsokaci ba game da kisan da ake zargin jami’an tsaro sun yiwa masu zanga-zanga  Lekki Toll Gate dake garin Legas.

Har wayau Shugaba Buhari ya gana da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi da Hafsan Rundonin Tsaro na Kasa Janar Gabriel Olanisakin a fadar sat a Aso Rock dake Abuja a ranar Talata, 20 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Kawo lokacin rubuta wannan rahoto da misalign karfe 1:25 na ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban shekara ta 2020, mai taimakawa Buhari a bangaren kafafen sadarwa na zamani Bashir Ahmad yace Buharin yana jagorantar tattaunawa kan tsaron kasa a fadar sa ta Aso Rock dake Abuja.

Wadan ke halartar taron da Buhari ke jagoranta sun hada da Mataimaki Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ministan Tsaro, Sauran Shugabannin Rundunonin Tsaro Na Kasa da Babban Sifetan Yan Sanda.

Kammalawa:

Labarin da ake yawada cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu karya ne. Ko ayau saida akaga Shugaba Buharin ya jagoranci tattaunawa da ta shafi tsaron kasa a fadar sa ta Aso Rock dake babban birnin tarayya Abuja.

CDD tana jan hankalin jama’a game da kirkira dama yada labaran karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa