Shugaba Buhari Bai Nada Wanda Zai Maye Gurbin Marigayi Abba Kyari Ba

Tushe Magana:

Wani labari da wata jarida da ake wallafawa a yanar gizo mai suna National Daily Newspaper ta wallafa wani labari  a ranar Asabat, 18 ga watan Afirilun shekara ta 2020 a shafin ta na yanar gizo dama shafin ta na Facebook inda ta zayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Ambasada Babagana Kingibe a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar sa. Labarin ya cigaba da cewa, kasancewar sa wanda ya rike mukamin Abba Kyarin na wucin gadi tun lokacin da marigayi Abba Kyarin yake jinya, Shugaba Buhari ya tabbatarwa da Babagana Kingibe mukamin sabon shugaban ma’aiktan fadar shugaban kasar.

Wannan jarida tayi wa Kingibe fatan alkhairi bisa sabon mukamin inda tace: “muna tayaka murna Babagana Kingibe, Allah yayi maka jagora amin”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gudanar ya gano cewa wannan labari ne na bogi. Kawo lokacin hada wannan rahoton a ranar 19 ga watan Afirilun shekara ta 2020 babu daya daga cikin fadar shugaban kasa ko mashawartan sa bangaren yada labarai da suka sanar nadin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar. Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa labarin da jaridar National Daily din ta wallafa ya gaza bada cikekken bayani game da inda ta samu labarin ko wanda ya sanar nadin Kingiben ko kuma majiyar da jaridar ta dogara da ita ta wallafa labarin. Har wayau acikin labarin, jaridar tayi alkawarin kawo cikekken bayani ga masu karanta labarin amma har lokacin hada wannan rahoto hakan bai faru ba.

Kammalawa:

Shugaba Muhammadu Buhari bai nada sabon shugaban ma’aikatan fadar sa ba. Labarin da ake yadawa cewa an nada Anbasada Babagana Kingibe bai tabbata ba. Ana shawartan mutane da suyi watsi da wannan labarin. CDD na jan hankalin mutane da su guji kirkira ko yada labaran karya. A rika tantance labari kafin wallafawa ko yadashi.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.