Skip to main content

Shin Zargin Shugaba Buhari Game Da Rahotannin BBC da CNN Akan Zanga-Zangar #EndSARS Gaskiya Ne?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 9 ga watan Disamban shekara ta 2020, shafin Twitter na Shugaba Muhammadu Buhari wato @MBuhari ya wallafa wani jawabi inda yace rahoton da kafafen yada labarai na kasashen ketare suka yada game da zanga-zangar #EndSARS ba rahoto ne day a karkata zuwa wani bangare tare da barin wani bangare.

Jawabin da ake zargin shafin shugaban kasan ya wallafa yace gidajen talabijin na CNN da BBC suka yada din ya kauda kai daga kisan yan sanda da akayi lokacin zanga-zangar, da ofisoshin yan sanda da gidajen yarin da aka mamaye, dama kadarorin da aka barnata.

Kawo lokacin hada wannan rahoto, an kara wallafa maganar shugaban kasan sau 6700 yayin da wassu kafafe da yawa suka cewa maganar ta burgesu.

Mai magana da yawun shugaban kasan Malam Garba Shehu ya bayyana cewa jawabin da akace shugaban kasan ne ya wallafa karya ne. Garba Shehu yayi wannan bayani ne ranar 11 ga watan Disamba, 2020, kwana biyu bayan jawabin ya fita.

Gaskiyar Magana:

Labarin da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya soki salon rahoton gidajen talabijin na BBC da CNN game da zanga-zangar #EndSARS karya ne.

Wani bincike da CDD ta gudanar ya gano cewa zargin da ake yi cewa gidajen talabijin din kasashen ketare sun fifita wani bangare suka kuma bar wani bangare a rahoton su game da #EndSARS ya gano cewa karya ne.

Sashin turancin buroka na BBC ya gabatar da rahoton kona ofishin yan sanda na Orile da wassu bata gari sukayi a ranar 20 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Photo credit: Rosemary Ajayi. Twitter: @RMAjayi

Kwana biyu bayan haka BBC sun bada labarin harin da aka kaiwa gidajen yarin Ikoyi da Warri

Gidan talabijin na CNN shima ya gabatar rahoton kai hari ga gidajen yarin, ga rahoton cikin adireshin yanar gizon.

A ranar 22 ga watan Oktoba, 2020 BBC sun gabatar da rahoto mai fadi game da batun.

A ranar 23 ga watan Oktoban shekara ta 2020 BBC ta gabatar da rahoto kan martanin Shugaba Buhari game da zanga-zangar #EndSARS din

A wata hira da aka yada sosai, gwamnan Legas Babjide Sanwo-Olu ya gayawa ma’aikaciyar CNN Becky Anderson cewa yana da kwarin gwiwar cewa za’a samu garan-bawul game da aikin yan sanda sakamakon zanga-zanga.

Kammalawa:

Zargin da ya fito daga shafin Twitter na Shugaba Muhammadu Buhari cewa gidajen talabijin na CNN da BBC basu bada kulawa ga kisan yan sanda, da kona ofisoshin yan sanda dama gidajen yari da aka bude karya ne!

CDD na jan hankalin jama’a da akodayaushe su tantance sahihancin labarai kafin yada su.