Shin Za’a Iya Anfani Da Katin Jebu Dan Yin Zabe a Zaben Gwamna Dake Tafe a Jahar Edo?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 18 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba sunga rahotanni da yawa da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zamani dama wassu jaridu da suka hada da The Nigerian Post da akace jam’iyyar PDP tayi zargin cewa jam’iyyar APC a jahar Edo tana samar da katin zabe na bogi ga ya’yanta dan yin zabe a zaben gwamnan dake tafe a jahar.

Jigon labarin da aka wallafa yace: “Zaben Gwamna a Jahar Edo: APC na buga katin zabe na bogi, inji jam’iyyar PDP”. Labarin yace jam’iyyar PDP tace APC ta yanke shawarar buga katunan zaben ne saboda ta gano cewa bazata iya lashen zaben gwamnan da za’a gudanar a jahar Edon.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa hukumar zabe ta kasa INEC ne kawau take da hurumin buga katin zabe na dindindin da ake anfani dashi dan kada kuri’a a Najeriya a halin yanzu. INEC tasha yin bayani akan cewa itace kawai keda damar buga katin zabe kuma katin na yanzu yana dauke da wassu alamomin tsaro da aka tsarasu dan su dace da runfa da akwatin da mutum zaiyi zabe. Kari akan bayanan da INEC ta gabatar baya shine yanzu katin zabe sai na’urar kada kuri’a ta tantance shi, wanda ke nuna cewa babu wani da zai iya buga katin zabe na bogi.

Yana da kyau mutane su tuna cewa wannan ba shine karon farko ba da irin wadannan zarge-zargen ke fitowa, kafin zaben shekara ta 2019 ansamu irin wannan zargin day a fito daga yan siyasa, a wancan lokacin, kwamishina a hukumar zaben mai kula da wayar da kai da hulda jama’a, Barr. Festus Okoye yayi bayani yayin da yake mayar da martani game da jita-jitar samar da katunan zaben na bogi inda yace kawai yan siyasa nayin irin wadannan maganganun ne da nufin tirsasawa hukumar zaben ayyana muhimman bayanan ta game na’urar kada kuri’a da a turance ake kira “smart card reader”.

Kamar yadda Ka’idojin Hukumar Zabe suka zayyana,  Na’urar Tantance Masu Zabe ana anfani da ita ne dan tantance masu kada kuri’a dan tabbatar da cewa hoton dan yatsan mai dauke da katin ya dace bayanan da na’urar ke dauke dashi. Hujjoji sun tabbata da cewa yin anfani da na’urar tantance masu zabe da nu’ura ya kara inganta sahihancin aiwatar da zabe a Najeriya.

Katin zabe na din-din-din da ake anfani dashi yanzu wani bazai iya anfani da na wani ba kuma INEC ce kawai ke iya bayar dashi. Zaben gwamna da za’a gudanar a jahar Edo dake cigaba da karotawa za’ayi anfani das hi wannan katin na din-din-din.

Labarai da aka wallafa a kafafen yada labarai da yawa inda jam’iyyar PDP tayi zargin cewa za’ayi anfani da katunan zabe na bogi dan yin magudi a zaben jahar Edo karya ne.

Kammalawa:

Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) tana tabbatar da cewa duk wani katin zaben da ba hukumar zabe ta kasa INEC ce ta bayar dashi ba, baza’a iya yin zabe dashi ba, saboda haka zargen da PDP keyi cewa anbuga katunan zabe na bogi dan yin magudin zabe a jahar Edo karya ne. Katin zabe da INEC ta bayar ne kawai za’a iya gudanar da zabe dashi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.