Shin Yar Jaridar Nan Kiki Mordi Ta Wallafa Wata Game Da Zubar Da Cikin Da Gano Cewa Namiji Za’a Haifa a Shafin Ta Na Twitter?

Gaskiyar Magana: Karya Ne

Tushen Magana:

Wani hoton wata magana da aka ce sananniyar yar jaridar nan Kiki Mordi ce ta wallafa ta karade kafafen sada zumunta na zamani a satin da ya gabata.

Maganar wadda akace a shafin Twitter aka wallafa tace Mordi tace, babu matsala taimakawa wadda ta shirya zubar da ciki har idan ta gane cewa namiji zata Haifa.

Maganar tace: “ni naïf son ya’ mace da da’ namiji kuma ina ra’ayin cewa ina damar zubar da ciki idan dai namiji zan haifa”

Wannan magana an yada ta sosai kuma mutane sunyi matukar Allah-wadai da abinda akace yar jaridar ta fada.

Gaskiyar Magana:

Bincike da nazari na kwakwaf da CDD ta aiwatar ya gano cewa maganar da aka danganta ta Mordin magance ta bogi kuma ba ita bace tayi maganar.

CDD tayi magana da Mordi inda ta karyata batun. Kuma binciken CDD game da batun ya gane babu wannan magana a jerin abubuwan da ta wallafa. Sakon wanda akace ta wallafa shi ranar 27 ga watan Nuwanba, 2020 baya cikin abubuwan da ta wallafa.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa da ake danganta shi da Kiki Mordi inda akace tace a zubda cikin da aka gane cewa namiji za’a haifa karya ne. Mordi bata wallafa wannan magana ko sako ba.

CDD na karfafawa jama’a gwiwa game da tantance game da tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa