Shin WHO Ta Sauya Matsayin Ta Game Da Killace Kai da Bada Tazara?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano labari da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sauya matsayin ta game da ka’idojin kare ka daga kamuwa da cutar Korona.

Labarin yace WHO ta ce masu dauke cutar Korona basa bukatar su killace kansu saboda cutar baza ta yadu daga jikin wani mutum zuwa wani ba.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin da ake yadawa cewa WHO mutanen da suka kamu da cutar Korona basa bukatar killace kansu karya ne. Karin binciken CDD din ya gano cewa wannan labari na bogi ba sabo bane, hasalima an taba yadashi a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2020 inda mutane da dama sukayi ta cece-kuce akansa.

CDD har wayau ta kara gano cewa WHO a cikin wani jadawali da ta fitar ta ci gaba da karfafawa mutanen da makusantan su suka kamu da cutar Korona da su bi ka’idojin kare kai kamar su bada tazara yayin mu’amala, das aka takunkumi, da wanke hannaye da ruwa mai gudana da sabulu mai kashe kwayoyin cuta da ido baya iya gani.

Kammalawa:

CDD na tabbatar da cewa sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta canja matsayin ta game matakan kare kai daga kamuwa da cutar Korona karya ne. Hukumar bata ce mutanen da ke dauke da cutar Korona basa bukatar killace kansu ba.

CDD na jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu tantance sahihancin su ba.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantamce muku sahihancin su ta hanyar turo sakon WhatsApp ko gajeren sako akan lamba +2349062910568 ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa