Shin Wassu Kwararru a Najeriya Sun Gano Maganin Cutar Corona?

Gaskiyar Magana: Hakan Bai Tabbata Ba!

Tushen Magana:

A satin da ya gabata majiyoyi da yawa musamman a yanar gizo sun wallafa wani labari dake cewa wassu masana kimiyya a Najeriya sun gano maganin cutar Corona.

Daya daga cikin wadannan majiyoyin mai suna Nigerian Guardian ta wallafa wani labari mai taken: “masana kimiyya a jami’o’in Najeriya sun samo maganin cutar Corona”.

Wannan labari an wallafa shi sosai acikin Najeriya kai harda ma wassu kafofin yada labarai na kasahen ketare.

Gaskiya Magana:

Kawo yanzu babu masani ko gungun masana a Najeriya da suka kai gano maganin cutar Corona. Kodayake, a ranar 19 ga watan Yunin shekara ta 2020, kungiyar masana da manazarta kimiyya a Najeriya a karkashin bincike akan cutar ta Corona wanda Dr Oladipo Kolawole na jami’ar Adeleke, Ede dake jahar Osun sun bayyana cewa suna da wani magani da suke tunanin za’a iya anfani dashi dan magance Corona. Sun bayyana hakan ne a lokacin da suke yiwa yan jarida bayani game da batun.

Manema labarai da yawa sunyi riga malam masallaci wajen bayyana cewa wadannan gungun masana sun gano maganin cutar Corona duk kuwa da yake basu fadi hakan ba, abinda kawai suka fada shine cewa suna da wani magani da suke tunanin zai iya magance Corona.

Kolawole, wani kwararren likita ne kuma ya bayyana cewa suna tukuru dan samo maganin cutar Corona a fadin nahiyar Afirka. Ya kara da cewa a halin yanzu suna da wassu sinadarai da suka aminta cewa zasu iya tai akawa wajen magance cutar amma za’a gudanar binciken kwakwaf dan tantance su.

A wani rahoto da aka wallafa a ranar 23 ga watan Yunin shekara ta 2020 Farfesa Olubukola Oyawoye wanda shine shugaban sashin nazarin kimiyya na jami’ar Adeleke University ya gaywa  BBC Pidgin cewa ikirarin da akeyi cewa masani kimiyya na jami’a sun samo maganin cutar Corona bah aka bane.

Oyawoye ya kara da cewa abinda taron manema labaran da akayi ya bayyana shine ana cigaba da gudanar da bincike game da neman maganin.

Har wayau a wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta wallafa awatan Yunin shekara ta 2020 COVID-19 candidate vaccines landscape, hukumar lafiyar tace kawo yanzu akwai magunguna guda 129 a fadin duniya baki daya da suke matakin tantancewar kwakwaf bisa matakin binciken magani kuma wannan adadi baya dauke da maganin da ayarin likitocin jami’a Adeleken.

Yaddan Ake Samar da Magani

Samar da magani abune da ya ta’allaka da bin wassu matakai da kuma gwaje-gwaje wadanda ake aiwatar dasu a matakai daba-daban saboda tantance inganci da illolin da suke dasu ga dan’adam dan dakile illolin in akwaisu. A wani kaulin yakan dauki shekaru kafin akai ga samar da magani saboda masana da masu bincike kan sadaukar da lokaci dan fahimtan abubuwa da yawa.

A wani martani da tayi, hukumar lafiya ta duniya World Health Organisation (WHO) a watan Afirilun wannan shekara tace samar da magani da ka iya magance cututtuka yakan dauki lokaci mai tsawo kafin a samar dashi, an iya samar da maganin da ka iya tasiri ga annoba da ka iya faruwa kuma samar da irin wannan magani zai taimaka musamman ga annobar da ake fama da ita.

WHO tace “adaidai wannan lokaci abin a yaba ne irin matakan dakatar da yaduwar cutar Corona da al’ummomi daban-daban ke dauka da aiwatarwa da suka shafi bada kariya ga dukkan mutane da sauran jama’a masu rauni acikin al’umma. Wannan abune mai kyau yayin da yunkurin samar waraka ga cutar ke cigaba”.

Kammalawa:

Ayarin masu bincike akan cutar Corona na Jami’ar Adeleke basu kaiga samo maganin cutar Corona ba, matsayar da suka cimma itace sun samu wani sinadari da za’a iya anfani dashi akan cutar amma wanna ya ta’allaka da tantancewar binciken lafiya.

CDD tana jan hankalin mutane dasu rika karanta gundarin labari dan gano abinda ya kunsa ba kawai a tsaya daga abinda jigon labarin ya fada ba.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.