Shin Wani Kansila a Jahar Kano Ya Nada Mutane 18 a Matasyin Masu Taimaka Masa?

Gaskiyar Magana: Eh, Gaskiya Ne.

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 12 ga watant Maris din shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da mai amfani da shafin Twitter mai lakabin @UncleAnass ya wallafa wani tsokaci day a bayyana cewa wani zababben kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka a bangarori daban-daban. Tsokacin ya ce Kansilan ya nada mai taimaka masa a bangaren al’amuran addini da siyasa da kungiyoyin sakai da bada dauki, dama sakatare na musamman ga Kansilan.

Tsokacin wanda @UncleAnass ya wallafa shi ya ce: “abinda dariya: wani Kansila a Kano ya nada mataikama 18 da suka hada da mai taimaka masa a wasu kebabbun al’amura, da mai taimaka masa ta bangaren addini da siyasa, da harkokin sakai, da bada dauki, da mataimaki a bangaren kafafen sada zumunta na zamani”

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar game da maganar cewa wani Kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka masa ya gano cewa gaskiya Kansila ya nada mutanen 18 a matsayin mataimaka a gare shi.

Kansilan, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda ke wakiltar mazabar Guringawa a karamar hukumar Kumbutso da ke kewayen birnin Kano , a jahar Kano ya tabbatar wa CDD nadin mutane 18 din a matsayin mataimaka a gare shi.

A wata sanarwa da ya fitar kuma CDD ta samu kwafin ta ranar 11 ga watan Maris din shekara ta 2021, Hon. Muslihu ya zayyano sunayen mutane da bangarorin da za su taimaka masan.

Da yake karin bayani wa CDD akan batun, Hon. Muslihu ya ce kodayake babu hurumin nada mataimaka ga ofishin kansila acikin tsarin mulki, amma yayi nadin tunda tsarin mulkin bai hana ba duk da kuwa bai ce ayi ba, kuma za a rantsar da mataimakan nasa nan gaba.

Muslihu ya ce: “to, banyi wannan nadi dan janyo hankalin jama’a kaina ba ko dan kokarin zama daban acikin yan uwana kansiloli ba, nayi haka ne kawai dan haskawa al’umma cewa ana iya amfani da kujerar siyasa dan aiwatar da ayyuka bisa ka’ida da kamanci ko da kuwa babu hurumin acikin kundin tsarin mulki”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa wani kansila a jahar Kano ya nada mutane 18 a matsayin masu taimaka masa a bangarori daban-daban gaskiya ne.

Kansilan, Hon. Muslihu Yusuf Ali wanda ke wakiltar mazabar Guringawa da ke karamar hukumar Kumbotso da ke kewayen birinin Kano ya tabbatar wa CDD nadin mutane 18 din.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu da gano muku gaskiyar su. Za ku iya turo gajeren sako (SMS) ta manhajar WhastApp akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa