Shin Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomole Ya Zabi PDP a Zaben Gwamnan Edo?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Angano wani hoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani dake ikirarin cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole ya kada kuri’arsa ga jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jahar Edo. Wani shafin Twitter mai suna  PDP Vanguard (@pdpvanguard) ya wallafa wata  magana kamar haka: “Tof ha! Oshiomole da kansa @GovernorObaseki ya zaba!”

 Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa hoton da ake yadawa din hoto ne da aka canza masa fasali ta hanyar yin anfani da na’urar zamani. Wadan su bidiyoyi da CDD ta nazarta game da yadda Adams Oshiomole yayi zaben sa sun gano cewa ya kada kuri’arsa ne a mazabarsa dake karamar hukumar sa ta Etsako kuma bai nuna kuri’ar tasa.

A wani bidiyo da jariadar The Punch ya nuna yadda Oshiomole yake tafiya zuwa a mazabarsa da kuma lokacing da yake jefa kuri’arsa a akawtin zabe.

Ana iya hango bayna kuri’ar tasa lokacin da ya jefa ta cikin akwatin zaben amma ba’a iya ganin bangaren day a dangwala hannunsa. Ba kamar yadda aka yayata cewa anga kuri’ar Oshiomolen kuma PDP ya zaba, abinda ya zaba din bai bayyana ba ballantana a iya gane abinda ya zaba. Hoton da ake yadawa da ya nuna  cewa Oshiomole ya zabi PDP hoto ne da aka canza fasalin sad an cimma wannan muradi. Bugu da kari, jami’in sa ido akan zaben na CDD yana runfar da Oshiomolen yayi zabe kuma ya tabbatar cewa hoton da ake yadawa din na karya ne!

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa