Shin Status Din Da WhatsApp Ya Saka Wani Salon Kutse Ne Ga Masu Amfani Da Manhajar?

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne.

Tushen Magana:

A ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigada (CDD) sun gano wata murya da aka nada kuma aka yadata a manhajar WhatsApp da ke gargadin dukkan mutane masu amfani da manhajar ta WhatsApp da su guji latsa status din WhatsAppp din ya saka.

Muryar tace wani balarabe ne ya kirkiri “status” din kuma duk wanda ya latsa dan kallon hoton da aka saka to lallai balaraben zai samu damar shiga rumbun hotunan wayar sa.

Wannan murya ta kara da cewa duk wanda ya latsa wannan status da WhatsApp ya saka to za’a yada dukkan hotunan batsa da ke wayar sa ga sauran jama’a.

Wannan sako ya bukaci duk wanda ya saurare shi ya yadashi ga sauran jama’a.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar akan wannan batu ya gane cewa sakon da aka nada cikin murya ake yadashi din sako ne na karya.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa manhajar WhatsApp tana da wani tsari na hana bibiya ko sarrafa abubuwan da mutum ke aiwatarwa a manhajar da ya shafi nadan murya ko wasu abubuwa da mutum ya ajiye a manhajar.

Mai magana da yawun manhajar ta WhatsApp ya bayyana cewa akwai labaran bogi da rudani da yawa da ake yadawa game da sauye-sauyen da suka gudanar a baya-bayannan.

Kanfanin WhatsApp din yace yana so ne ya sanar da mutane tsare-tsaren sa na bada kariya da kiyaye sirrin masu amfani dashi shiyasa ya sanar dasu ta hanyar status din. WhatsApp ya kara da cewa yana so ne mutane suji kai tsaye daga gare shi, shiyasa yayi amfani da hanyar status inda kowane mai amfani da manhajar zai gani kai tsaye.

Kammalawa:

Binciken CDD ya gano cewa kallon “status” din kamfanin WhatsApp baya nufin samu damar shiga rumbun hotunan masu amfani da manhajar ta WhatsApp, labarin da ake yadawa cewa idan mutum ya kalli status din WhatsApp to za’a samu damar shiga rumbun adana hotunan sa labari ne na bogi.

Kamfanin WhatsApp yayi amfani da tsarin “status” ne dan sanar da masu amfani dashi wassu batutuwa game da manhajar.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa