Shin Shugaba Muhammadu Buhari Ya Umarci Rarara Ya Karbi Naira Dubu Dai-Dai a Hannun Yan Najeriya Dan Yimasa Waka?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 16 ga awatan Satumban shekara ta 2020, masu tanatnce sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani rahoton da aka nada cikin murya wanda kuma wani rediyo da bai bayyana sunansa ba ya yada inda akaji mai gabatar da labaran na bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci mawakin siyasan na Dauda Kahutu Rarara ya tattara naira dubu dai-dai daga hannun yan Najeirya dan yimasa waka. Acikin rahoton mai tsawon kusan minti 2 anji mutane na bayyana ra’ayoyin su game da tara kudaden.

Acikin rahoton anji mai gabatar da shirin tana cewa Buhari ya bayyana dalilin umartan Dauda Rarara ya tara kudin dan yimasa wakar shine rashin kudi da gwamnati ke fama dashi a wannan lokacin.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Shugaba Muahammadu Buahri bai umarci Rarara ya karbi koda naira daya daga yan Najeriya ba dan yimasa waka.

Da CDD ta tuntube shi game da batun, matemaki na musamman ga Shugaba Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya bayyana cewa Buhari bai umarci Rarara ya karbi ko kwabo daga kowa ba.

Bashir Ahmad ya kara da cewa: “wannan labari ba wani abu bane face karya tsagwaron ta. Buhari bashi da masaniya game da tara kudi da Rarara zaiyi dan yimasa waka, kuma shi kansa Rarara baici Buhari ya umarceshi ya karbi kudin kowa ba, dan mutane suyi watsi da wannan labari na bogi”.

Bashir ya cigaba da cewa: “a duk hirarrakin gidajen jaridu da Rarara yayi bayani karara akan dalilansa na neman magoya bayan Shugaba Buhari suyi karo-karo dan biyan kudin wakar da zai yiwa Buharin akan nasarorin da ya samu kuma babu inda ya danganta Shugaba Buhari da tattara kudaden”.

Kammalawa:

Rahoton da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Dauda Kahutu Rarara ya karbi naira dubu-dubu daga yan Najeriya dan yimasa waka karya ne!

Wannan rahoton da ake yadawa cikin murya labari ne na bogi dan haka CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi dashi tare da daina yadashi.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa