Shin Shugaba Buhari Ya Sallami Abba Kyari Daga Aiki?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Maganar:

Jita-jiatr da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari  ya sallami Abba Kyari daga aiki saboda kamuwa da yayi da Cutar Corona ko COVID-19  karya ne. Mai taimakawa Shugaba Buharin ta bangaren yada labarai a kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya tabbatar da rashin sahihancin labarin a shafin san a Twitter a ranar 31 ga watan Maris din 2020 inda yace Abba Kyari yana cigaba da zama a mukaminsa na shugaban mai’aikata ga Shugaba Buharin.

Kammalawa:

Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) suna kira ga jama’a suyi watsi da wannan labari na bogi. Labari ne marar tushe kuma kirkirarre.

#AdenaYadaLabaranKarya

#AgujiYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.