Shin Shugaba Buhari Ya Kori Hafsoshin Rundunonin Tsaron Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 29 ga watan Mayun shekara ta 2020, jaridar Daily Mail Online ta wallafa wani labari dake cewa Shuagab Muhammadu Buhari ya kori hafsoshin rundoninin tsaron kasar nan sakamakon almundahanar da ta shafi kudade.

Labarin ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya salami manyan jami’an tsaron ne bayan aka gabatar korafi akansu day a shafi aikata cin hanci da rashawa.

Labarin harwayau ya kara da cewa tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari ya rufe almundahanar da hafsoshin tsaron suka tafka.

Wani shafin yanar gizo mai suna Will a wani labari da ya wallafa shima ya yace Shugaba Buhari ya amince da korar manya shugabannin rundunonin tsaron ne bayan cin hanci da rashawar da suka tafka ta fito fili makonni bayan rasuwar Malam Abba Kyari.

Kamar yadda shafin yanar gizo na Will din ya zayyana, marigayi Abba Kyari a lokacin rayuwar sa akodayaushe yana boye cin hanci da rashawar da hafsoshin tsaron ke tafakawa.

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD batun korar hafsoshin rundunonin tsaron ya samo asali ne daga jita-jitar da ake yadawa a sassa daban-daban na kasar nan.

CDD har wayau ta gano cewa Shugaba Buhari baiyi kowane irin furuci ba game da hafsoshin rundunonin tsaron wadanda suka kama aiki tun shekata ta 2015.

Wani bincike da CDD din ta aiwatar ya gano cewa shugaban rundunar sojan kasan Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai yaje Maiduguri a Jahar Borno a ranar Asabar, 30 ga watan Mayun shekara ta 2020 dan ganin yadda kirkira dama gyara ababan sufuri da akanyi anfani dasu a lokacin yaki da wassu injiniyoyi ke aiwatar wa.

Har wayau, Sifeta Janar din yan sandan Najeriya Mohammaed Adamu a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin shekara ta 2020 da yake maida martani game da kisan Matashiya Vera Uwaila ya tabbatar wad a yan Najeriya cewa za’a zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gabatar dasu a gaban kuliya.

Leave a Comment

Your email address will not be published.