Shin Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugabannin Kananan Hukumomi Biyar Na Jahar Katsina Game Da Rashin Tsaro?

Tantancewar CDD: Ba Gaskiya Bane!

Tushen Magana:

A ranar Talata, 28 ga watan Yulin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sun gano wani hoto da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wassu shugabannin kananan hukumomi a jahar Katsina.

Hoton wanda aka yada a dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook ya bayyana cewa Buhari yayi ganawar musamman da shugabannin kananan hukumomin Jibia da Safana da Faskari da Sabuwa da Danmusa dangane da lalubo hanyoyin magance rashin tsaro da ya addabi yankunansu.

Hoton ya zayyana karara cewa manufar ganawar shine samo hanyar da zata warware tare da kawo karshen kashe-kashe dake faruwa a jahar Katsinan.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa ba kamar yadda hoton da kuma bayanin dake biye dashi suka zaiyana ba, Shugaba Muhammadu Buhari baiyi kowace ganawa da wassu shugabannin kananan hukumomin jahar Katsina ba. Mutane da aka gani acikin hoton tare da Shugaba Buhari ba shugabannin kananan hukumomin Sabuwa, Safana, Batsari, Faskari k Danmusa bane.

Mutanen da aka gani suna zaune da Shugaba Buhari shugabanni ne na wasssu kasahen Afirka a lokacin da suka kai ziyara kasar Mali a ranar 23 ga watan Yulin shekara ta 2020 dan sasanta rikicin kasar, kuma an dauki hoton ne a wannan rana.

Shugabannin kasashen Afrikan da suke cikin hoton sune: Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar kasashen Afirka ta yamma wato Shugaba Muhammadu Issoufou na jamhoriyar Nijar, da Ibrahim Keita na kasar Mali, sauran sune Shugaba Machy Sall na Senegal, da Nana Akufo-Addo na Ghana, da Alasanne Ouattara na Code d’Ivoire da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an dauki hoton ne lokacin da Shugaba Buhari yake ganawa da sauran shugabannin kasashen Afirka a kasar domin lalubo hanyoyin magance rikicin siyasa dake faruwa a kasar Mali.

Kammalawa:

Hoton da ake yadawa a dandalin Facebook dake cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wassu shugabannin kananan hukumomin jahar Katsina dangane da halin rashin tsaro dake faruwa a yankunansu ba gaskiya bane!

Hoton an dauke shine a kasar Mali a ranar 23 ga watan Yulin shekara ta 2020 kuma mutanen da Shugaba Buhari ke ganawa dasu acikin hoton wassu shugabannin kasashen Afirka ne.

CDD na jan hankali mutane da su guji yada labaran karya tare da daina yada wannan labari.

Leave a Comment

Your email address will not be published.