Shin Shugaba Buhari Ne Yafi Kowane Shugaban Kasa Yawan Mabiya a Shafin Twitter a Nahiyar Afrika?

Tantancewar CDD: Ba Gaskiya Bane

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 22 ga watan Yulin shekara ta 2020, kanfanin dallancin labarai na kasa (News Agency of Nigeria-NAN) ya rawaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban da yafi yawan mabiya a shafin Twitter a jerin shugabannin Afrika.

Rahoton NAN din ya bada misali da binciken “Twiplmacy Study 2020” wanda majiyoyin sadarwa na yanar gizo dama jaridu irinsu Vanguard News, PMNews Online, Newswireng da Pulse Nigeria da All Africa sukayi anfani dashi.

Gaskiyar Magana:

Kamar yadda binciken kwakwaf ya gano wanda kuma Twitter ke anfani dashi (Twiplamacy) wajen tantance masu yawan mabiya ya zayyana cewa shugaban kasar Masar wato Abdelfattah Elsisi (@AlsisiOfficial) shine shugaban da yafi yawan mabiya a shafin na Twitter a jerin shugabannin Afirka. Yana da mabiya 4,133,263 yayin da Shugaba Buhari (@MBuhari) ke da mabiya 3,121,169

Rahoton Twiplamcy din ya zayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shine shugaban da yafi yawan mabiya a Twitter a yammacin Afrika amma ba’a fadin Afirka baki daya ba. Rahoton Twiplomacy din da NAN tayi anfani dashi ya zayyana bayanan sa karara.

A screenshot of a cell phone
Description automatically generated

Wani bangare na bincike twiplomacy di yace: “Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya shine shugaban da yafi kowane shugaba dake kudancin Sahara a nafiyar Afirka yawan mabiya a shafin Twitter, Buhari yana saman Paul Kagame, shugaban kasar Rwanda da mabiya 1,910,159”.

Akwai kasashe 46 a kudancin Sahara daga cikin kasashe 54 dake nahiyar Afirka. Kasashen Masar, Libiya, Maroko, Somalia, Sudan, Algeria, Djibouti da Tunisia basa cikin jerin kasashen dake kudancin Sahara.

Kudancin Sahara a nahiyar Afirka yana nufin kasashen da kudu da Sahara.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Shugaba Muhammadu Buhari shine shugaban da yafi kowane shugaban kasa a nahiyar Afirka yawan mabiya a Twitter ba gaskiya bane.

Shugaban kasar Masar wato Abdelfattah Elsisi (@AlsisiOfficial) shine yafi kowane shugaban kasa a nahiyar Afirka yawan mabiya a shafin Twitter, yawan mabiyan sa yakai 4,133,263 kawo karfe goma na safiyar ranar 23 ga watan Yulin shekara ta 2020.

CDD tana karfafawa yan jarida dasu rungumi dabi’ar yin binciken kwakwaf akan labari kafin wallafa shi.

Leave a Comment

Your email address will not be published.