Shin Rundunar Yan Sanda Ta Jahar Legas Ta Kara Kama Naira Marley?

Gaskiyar Magana: Eh Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani labari da wani zauaren yanar gizo suka wallafa, labarin ya bayyana cewa shahararren mawakin na Azeez Fashola wanda akafi sani da suna Naira Marley ya sake shiga komar yan sanda a jahar Legas.

Labarin wanda ya karade shafukan sada zumunta na zamani yace: “labari da dumu dumin sa: yan sanda sun sake kama Naira Marley”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa rundanar yan sanda a jahar Legas ta sake garkemewa tare da gabatar da Naira Marley da shida manajansa Seyi Awouga a gaban wata kotun tafi da gidan ka mai sauraron laifuka na musamman ta jahar Legas.

Wata sanarwa da ta fito daga rundunar yan sandan jahar Legas ta bayyana cewa ankama Naira Marley da manajansa ne bisa laifin karya dokar sufuri da tafiye-tafiye tsakanin jihohi lokacin da aka saka doka akan hakan dan magance cutar Korona.

Binciken CDD din ya gano cewa wadan da ake zargin sun amsa laifin su inda kotun taci tarar su naira dubu dari-dari kowannen su.

Marly dashi da manajansa sunbar jahar Legas zuwa Abuja a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2020 inda kuma suka dawo a ranar.

Sunyi tafiyar ne ta filin jirgin saman Murtala Muhemmed dake Legas inda suka halarci wani taron waka a unguwar Jabi dake Abuja, taron da suka halarta din ya janyo garkame wajen mai suna Jabi Lake Mall.

Rundunar yan sanda ta dauki Naira Marley zuwa Abuja ta jirgin sama a ranar 7 ga watan Agustan shekara ta 2020 dan fuskantar zarge-zargen da ake masa da suka kai hudu.

Naira Marley ya amsa laifukan sa sannan mai shari’a Idayat Akanni taci tararsa tsabar kudi naira dubu dari biyu (N200,000).

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa rundunar yan sandan jahar Legas ta kama Naira Marley gaskiya ne.

Mawakin wanda aka kama tare da manajansa yana fuskantar laifin karya dokokin zirga-zirga da Shugaban kasa ya kafa domin dakile cutar Corona.

CDD tana jan hankalin jama’a das u rika karanta gundarin labari dan fahimtar abinda ya kunsa. Zaurukan yanar gizo suna da dabi’a wallafa labarai masu cece-kuce dan hankalin mutane atre da jawowa kansu yawan masu ziyartan shafukan su.

Summary

Tantancewar Da CDD Ta Aiawatar

Shin Rundunar Yan Sanda Ta Jahar Legas Ta Kara Kama Naira Marley?

Gaskiyar Magana: Eh Gaskiya Ne!

Labarin da ake yadawa cewa rundunar yan sandan jahar Legas ta kama Naira Marley gaskiya ne.

Mawakin wanda aka kama tare da manajansa yana fuskantar laifin karya dokokin zirga-zirga da Shugaban kasa ya kafa domin dakile cutar Corona.

CDD tana jan hankalin jama’a das u rika karanta gundarin labari dan fahimtar abinda ya kunsa. Zaurukan yanar gizo suna da dabi’a wallafa labarai masu cece-kuce dan hankalin mutane atre da jawowa kansu yawan masu ziyartan shafukan su.

Ku kiramu akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.