Shin NCDC Tana Bada Tallafin Kudi Ga Yan Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi 17 ga watan Mayun shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC) tana shirye-shiryen rabawa yan Najeriya tallafin kudi adaidai lokacin da ake cigaba da yakar cutar Corona.

Kamar yadda sakon ya bayyana, tallafin kudin za’a rabashi ne sakamakon umarnin da gwamnatin tarayya ta baiwa babban bankin kasa na CBN cewa ya baiwa NCDC din kudade dan rabawa yan Najeriya ta hanyar asusun ajiyar su na banki.

Sakon ya shawarci yan Najeriya da su cigaba da zama a gida kuma su duba cancantar su dan samun tallafin kudi ta hanyar kiran lambar wayar da aka bayar acikin sakon.

Ga abinda sakon yake cewa: sanarwa ga dukkan jama’a, sakamakon dokar zaman gida da yan Najeriya ke cigaba da yi, gwamnatin tarayya ta bada umarni ga babban banki kasa na CBN da ya raba kudi ga yan kasa ta hanyar hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC  dan tallafa musu. Wannan rabon kudi zai gudana ne ta hanyar asusun ajiya na banki. 

Yan Najeriya dake da asusun ajiya na banki, da lambar kariya ta BVN da kuma katin cire kudi na ATM zasu samu wannan tallafi. Manufar tallafin shine samarwa yan Najeriya yanayi mai kyau yayin zaman gida. Zaku iya sanin ko kun cancanta ku samu wannan tallafin kudi ta hanyar kiran wannan 07043196929 lambar waya. Sakon ya karkare da cewa: “muna muku fatan nasara”.

Gaskiyar Magana:

Tun bayan samun bullar cutar Corona da kuma aiyana dokar zama a gida da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jahohi suka yi, yan danfara a matakai daban-daban suke ta danfaran yan Najeriya ta sigogi daban-daban.

Daya daga cikin hanyoyin da mazanbatan kebi itace yin ikirarin cewa gwamnatin tarayya na kira ga mutane cewa suyi rijista ko bada asusun ajiyar su na banki a wani shafin yanar gizo dan samun tallafin kudi. CDD ta jima tana tantance ire-iren wadannan labaran bogi da wayar da kan jama’a game dasu.

A lokacin da take maida martani game labarin bogin, NCDC tace tana sane da jita-jitar da ake yadawa cewa zata rabawa yan Najeriya kudi a wannan lokaci da ake cigaba da zama a gida.

NCDC ta gargadi yan Najeriya da suyi watsi da sakon inda ta bayyana shi a matsayin labarin bogi, NCDC taja hankalin mutane da su dakatar da yada sakon.

Sanarwar da NDCD ta fitar game da labarin bogin ta kara da cewa: “aikin NCDC sune jagoranta da ganowa tare da bada dauki ko kulawa ga cutuka masu yaduwa dama magance barazanar lafiya da za’a iya fuskanta”

Bincike da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin tarayya bata sakarwa NCDC kudi ta hanyar babban bankin kasa na CBN ba dan rabawa ga yan Najeriya.

Kammalawa:

NCDC ba ta raba kudaden tallafi ga yan Najeriya sakamakon zaman gida da suke cigaba da yi. Raba kudaden tallafi a lokutan annoba baya cikin ayyukan NCDC. CDD na jan hankalin jama da su rika tantance sakonni dama sanarwa musamman a manhajar WhatsApp kafin yadasu saboda ba dukkan abinda aka gani bane yake gaskiya.

Kuna iya turo wa CDD sakonni da labaran da kuke da shakku akansu dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2349062910568 ko ku tuntunbe mu a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica_H.

Leave a Comment

Your email address will not be published.