Shin Matasa Sun Doki Dan Majalisar Tarayya a Jahar Kano Sakamakon Rashin Cika Alkawura?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 25 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wassu jaridu da majiyoyi suka wallafa a shafukan sun a yanar gizo cewa matasa sun doki dan majalisa mai wakiltar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe a garin Gulu yayin da yaje ziyarar aiki.

Majiyoyin da suka wallafa labarin sun hada da Sahara Reporters, Naturenex da Pinnaclereport. Majiyoyin sun wallafa wani hoto dake nuna dan majalisar cikin dafifin jama’a gumi yana keto masa.

Gaskiyar Magana:

Labarin da ake yadawa cewa matasa sun doki dan majalisar tarayya mai wakiltar Tofa da Dawakin Tofa da Rimin Gado, Engr. Tijjani Abdulkadir Jobe karya ne. Binciken da CDD ta gudanar ya cewa labarin labari ne na bogi.

Hon. Jobe yaje mazabarsa ne dan duba aikin hanya dake titin Rimin Gado zuwa Gulu da ya kawowa mazabar tasa.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa bayan ya gabatar da ziyarar duba hayar ya wuce zuwa garin san a Jobe inda dubban jama’a da suka taro dan yimasa maraba, ganin dafifin jama’ar da suka tarun, Engr. Jobe ya bukaci abar mutane su shigo gidan sa inda ya dinga raba musu kudi, dan majalisar yayi gumin ne yayin da yake cikin rana yana rabawa mutane kudi.

Wani da yaga abinda ya faru, Balarabe Yusuf Gajida ya tabbatarwa CDD cewa labarin dukan dan majalisar karya ne.

Gajida: “Na rantse babu wanda ya daki Hon. Jobe, mutane sun taru ne dan yin murna da zuwansa kuma komai farin ciki ya faru”.

Shima da yake maida martani game batun, mai taimakawa dan majalisar ta fuskar hulda da jama’a, Ibrahim Yaro ya karya ta labarin inda yace abun mamaki ne yadda jaridun suka wallafa labarin bogi.

Yaro yace: “wani magoyin bayan dan majalisar ne ya dauki hoton da akaga shi Hon. Jobe yana gumi ya wallafa a shafin san a Facebook inda ya yaba masa saboda taimakawa mutane, amma kwanaki bayan yin hakan sai wani dan adawa shima ya wallafa hoton inda ya caccaki dan majalisar, kwana daya bayan yin haka sai jaridar Sahara Reporters ta dauki wannan labari da hoton ta wallafa cewa an doki dan majalisar, wannan abun mamaki ne, yaya za’ayi jarida ta wallafa labari ba tare da bincika sahihancin sa ba?”

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa matasa sun doki dan majalisar tarayya mai wakiltar Tofa da Dawakin Tofa da Rimin Gado, Engr. Tijjani Abdulkadi Jobe sakamakon rashi cika alkawura karya ne!

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa