Shin Mata Sun Bukaci Shugaba Buhari Yayi Murabus Yayin Zanga-Zangar #EndSARS a Katsina?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

A ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sun gano wani bidiyo mai tsawon dakika 30 wanda wani zauren yanar gizo ya wallafa ya kuma yi ikirarin cewa mata a jahar Katsina sun shiga zanga-zangar #EndSARS suka kuma nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulkin Najeriya. Acikin bidiyon anga mata sanye da bakaken hijabai suna rawa suna waka suna kuma cewa Buhari munafiki ka sake mana Malam.

Kamar yadda shafin Twitter din ya bayyana wannan zanga-zanga ta faru ne a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar #EndSARS a garin Katsina. Shafin ya kara da cewa matan sunyi zanga-zangar ne dan neman Shugaba Buhari ya sauka tare da kawo karshen halin rashin tsaro da yankin arewancin Najeriya ke ciki.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa ikirarin da mawallafan bidiyon sukayi na cewa an dauki bidiyon ne lokacin zanga-zangar #EndSARS a Katsina karya ne.

Karin binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa, tun farko an wallafa bidiyon ne a shafin YouTube a ranar 12 ga watan Oktoban shekara ta 2020 kuma wani shafin talabijin mai suna African Best TV ne ya wallafa shi kuma kawo yanzu mutane 44,000 ne suka kale shi.

CDD ta kara gano cewa an nadi bidiyon ne a lokacin da kungiyar Yan’uwa Musulmai mabiya darikar Shi’a suka gudanar da zanga-zangar neman asako Malam Ibrahim Elzakzaky. Idan za’a iya tunawa dai an kama Elzakzaky ne a shekara ta 2015 inda ake cigaba da tsare shi kawo wannan lokaci.

Jigon labarin yayi banbanci da abinda matan dake cikin bidiyon ke fada. Anjiyo matan da suke sanye da bakaken kaya na cewa “buhari munafiki ka sake mana Malam”, yayin da shi kuma labarin ke cewa matan na zanga-zangar #EndSARS ne.

Kammalawa:

Bidiyon da ake yadawa cewa mata sunyi zanga-zangar #EndSARS a Katsina bidiyo ne na karya. Bidiyon an dauke shi ne a lokacin da mabiya darikar Shi’a sukayi zanga-zangar neman a asako Malam Ibrahim Elzakzaky wanda a kama a shekarar 2015.

CDD na kiar ga jama’a da su guji yada kirkira ko labaran karya.

#AgujiYadaLabaranKarya

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa