Shin Masu Zanga-Zangar #EndSARS a Benin Sun Balla Tare Da Fitar Da Fursunoni?

Gaskiyar Magana: Karya Ne.

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban shekara ta 2020 fursononi da ake tsare dasu a gidan gyaran hali birnin Benin a jahar Edo suka tsere, tserewar tasu tazo ne a lokacin da ake tsaka da zanga-zangar #EndSARS.

Wani rahoto da Goldennews suka wallafa yayi ikirarin cewa masu zanga-zangar #EndSARS sune suka shiga wani gidan yari dake kan titin tafiya Sapele a birnin Benin kuma suka fitar da fursunonin da ake tsare dasu. Ajikin rahoton anga wani bidiyo mai tsawon dakika 39 inda dandazon mutane ke turmutsitsi yayin da murya wata mata ke cewa “fursunoni sun samu shaker iskar yanci”.

A wani rahoton kuma da Newsflash247 anjiyo murya na cewa masu zanga-zanga dake Kings Square a birnin Benin sun karya kofar gidan yari tare da fitar fursunoni .

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa da gaske ne fursunoni sun tsere daga gidan yarin da ake tsare dasu a birnin Benin.

Sai dai masu zanga-zangar #EndSARS sun barranta kansu da fitar da fursunonin inda sukace wassu bata-gari ne ked a alhakin balla gidan yarin tare da fitar da fursunonin. Acikin wani bidiyon anga bata-garin na dauke da makamai abinda masu zanga-zangar suka kira aikin wassu amma ba su ba.

Wani nazari da CDD ta aiwatar ya gano cewa ba’a lalata kofofi da makullan gidan yarin ba a lokacin da fursunonin suka tsere, wannan kuma wani al’amari ne dare daure kai da jefa alamomin tambaya a zukatan mutane.

Adaidai lokacin da ake ta jefa alamomin tambaya akan waye ya sake fursunonin sai gashi kuma anga fursunonin da jakakkunan su dama na’urar sauraron kida a kunne wato “headsets” suna gudu.

Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana guduwar fursunonin a shafin ta na Twitter inda tace: “cikin takaici muna tabbatar da cewa ankai hari ga ofisoshin yan sanda na Ugbekun da kasuwar Oba da Idogbo, wassu dake fakewa da zanga-zangar #EndSARS ne suka kai harin a birnin Benin dake jahar Edo yau Litinin, 19 ga Oktoba, 2020”.

Kammalawa:

Gaskiya ne fursononi sun tsere daga gidan yarin Benin dake jahar Edo. Amma masu zanga-zangar #EndSARS basu ne ke da alhakin sake fursunonin ba, wannan aikin na wassu bata-gari.

Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana guduwar fursunonin a shafin ta na Twitter inda tace: “cikin takaici muna tabbatar da cewa ankai hari ga ofisoshin yan sanda na Ugbekun da kasuwar Oba da Idogbo, wassu dake fakewa da zanga-zangar #EndSARS ne suka kai harin a birnin Benin dake jahar Edo yau Litinin, 19 ga Oktoba, 2020”.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa