Shin Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Titin Zuwa Filin Jirgin Saman Abuja Ranar 4 Ga Maris, 2021?

Gaskiyar Al’amari: Akwai Rudani Cikin Labarin

Tushen Magana:

A ranar 5 ga watan Maris, shekara ta 2021wadan su kafafen sada zumunta na zamani sun wallafa wani bidiyo tare da yin ikirarin cewa: “matasan Najeriya sun toshe titin zuwa filin jirgin sama da ke garin Abuja, daidai gadar Dantata, sun kuma dakatar zirga-zirgar jiragen sama tare da tsayar da al’amura cak a garin na Abuja”.

Bdiyon an kara yada shi a manhajar WhatsApp da taken: “ zanga-zangar Lekki Toll Gate na maimaita kanta a garin Abuja. Ya Allah taimaki wannan kasar!”

Shafin yanar gizo na Nairaland ya kara wallafa bidiyon a dandalin tattaunawar sad a karin bayani kamar haka: “wasu matasa sun dauki doka a hannun sua babban birnin tarayya, wato Abuja aranar Alhamis inda suka dakatar dukkan al’amuran dare, wannan lamari ya faru a gadar Dantata da ke kan titin zuwa fili jirgin saman garin Abuja, dalilin daukar wannan mataki da matasan suka yi shine mummunan shugabanci da ke wanzuwa karkashin mulkin Shugaba Buhari”.

An nuna wani jerin gwanon ababen hawa inda wani mutum ke cewa matasa sun rufe gadar Dantata yayin da suke gudanar da zanga-zanga.

Gaskiyar Magana:

Binciken CDD ya gano cewa bidiyon da aka yada din watan sa biyar da dauka. Hasalima an dauki bidiyon ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 2020 lokacin gudanar da zanga-zangar #EndSARS da ke hankoron kawo karshen ikirarin cin zarafin mutane day an sanda keyi a Najeriya.

Hakika masu zanga-zanga sun toshe titin zuwa filin jirgin saman garin Abuja. Wannan hanya hanya ce da ake binta zuwa jihohin Niger da Kogi da Kaduna dama wasu yankunan babban birnin tarayyar. Jaridu irinsu Premium Times da Independent da Tribune duk sun rawaito wannan zanga-zanga.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa, lallai anyi zanga-zanga a garin Abuja a ranar 4 ga watan Maris din shekara ta 2021 wadda wasu mutane da ke neman Shugaba Buhari yayi murabus suka aiwatar. Masu zanga-zangar wadda mafiya yawan su matasa ne sun gudanar da ita ne a tsakiyar birnin tarayya amma ba gadar Dantata ba kamar yadda majiyoyi da yawa suka rawaito.

Rundunar yan sanda babban birnin tarayya ta yi tsokaci da bidiyon inda ta ce ba a yi zanga-zangar #EndSARS a Abuja ba a ranar 4 ga watan Maris din 2021.

Yan sandan fayyace batun inda suka ce bidiyon da ake yadwa din an dauke shine a lokacin zanga-zangar #EndSARS da ta gudana a shekarar da ta gabata.

“Labarin bogi, an janyo hankalin rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja game da bidiyon yin zanga-zangar #EndSARS a Abuja. Muna son tabbatar da cewa babu wata zanga-zanga da ta faru, wannan bidiyo da aka yada tsohon bidiyo da aka nada lokacin zanga-zangar #EndSARS da ta gudana a shekarar da ta gabata, inji hukumar yan sanda

Kammalawa:

Ikirarin da aka yi cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani cewa matasa sun toshe gadar Dantata da ke kan titin zuwa filin jrigin saman Abuja ranar Alhamis, 4 ga Maris, 2021 yana dauke da rudani. Bidiyon an dauke shi ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 2020 lokacin zanga-zangar #EndSARS.

CDD na jan hankalin jama’a da su guji yada duk abubuwan da ba su tantatnce sahihancin su ba.

Za ku iya turowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568 ko a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa