Shin Majalisar Dattawa Taki Tantance Lauretta Onochie Dan Nada Ta a Matsayin Kwamishina a Hukumar Zabe Ta Kasa INEC?

Gaskiyar Magana: Labarin Yana Cike Da Rudani

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoban da muke ciki, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani azure yanar gizo mai wallafa labarai mai suna Wazobia Reporters ya wallafa inda yake ikirarin cewa majalisar dattawan Najeriya taki tantance Lauretta Onochie dan nada ta a matsayin kwamishina a hukumar zabe ta kasa INEC da Shugaba Muhammadu Buhari yake son yi.

Labarin ya kara da cewa majalisar dattawan ta nemi fadar shugaban kasa ta sake nazari akan yunkurin nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishina a hukumar zaben kasa INEC.

Labarin jingina madogararsa da wata jarida mai suna Nigerian Daily a matsayin inda ya samo labarin.

Gaskiyar Al’amari:

Bincken da CDD ta aiwatar ya gani cewa labarin dake cewa majalisar dattawan Najeriya taki tantance Lauretta Onochie dan zama kwamishina a hukumar zabe ta ksa INEC labari ne na bogi.

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoban da muke ciki, Shugaba Buhari ya zabi Onochie da wassu mutane uku wato Mohammed Sani daga jahar Katsina, da Kunle Ajayi daga jahar Ekiti da Saidu Ahmed daga jahar Jigawa da nada su a matsayin kwamishinonin zabe a hukumar zabe ta kasa INEC.

Binciken da CDD ta zurfafa game da batun ya gano cewa jaridar da Wazobia Reporters sukace sun samo labarin daga wajen su wato  Nigerian Daily basu buga wani labari makamancin wannan ba. Saboda haka labarin da Wazobia Reporters din suka buga labari ne na karya.

Idan Shugaban Kasa ya gabatar wa majalisar dattawa jadawalin mutanen da yake so ya nada a wassu mukamai, majalisar zata mika sunayen ga kwamitoci daban-daban dan gudanar da binciken kwa-kwaf akansu.

Bayan kamala bincike game da mutanen da Shugaban Kasa ke san nadawa a mukamai, kwamitoci zasu gabatar da rahoton su ga majalisar dattawan dan daukan mataki na gaba. Kuma kawo yanzu ba’a kamala wannan aiki na bincike ba kuma bada wata matsayarta game da batun tun bayan sanar da cewa Shugaban Kasa ya aiko sunayen mutanen da yake son nadawa a mukamin kwamishinoni a hukumar zaben a ranar Talata, 13 ga watan Oktoban da muke ciki.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa majalisar dattawa taki tantance Lauretta Onochie dan zamowa kwamishina a hukumar zabe ta kasa INEC karya ne.

Har yanzu majalisar dattawa bata dauki kowane irin mataki ba game da sunayen da Shugaban Kasa ya aika mata a ranar Talata, 13 ga watan Oktoban shekara ta 2020.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa