Shin Kanfanonin Apple da Google Sun Samar Manhajar Da Zata Bi Diddigin Cutar Corona a Asirce a Wayoyin Mutane?

Tantancewar CDD: Labari ne na bogi!

Tushen Magana:

Mutane da yawa a Najeriya dake anfani da manyan wayoyi suna ta bayyana shakku da cece-kuce dangane wata magana dake yawo cewa daya daga cikin kanfanonin nan guda biyu, wato Apple ko Google ya jefa wata manhaja da zata rika bin diddigin bayanan da suka shafi cutar Corona ba tare da izinin masu wayoyin ba. Wannan magana tayi yawo sosai a kafafen sadaarwa na zamani irinsu WhatsApp da Facebook da Twitter. Kamar yadda bayanin dake kunshe acikin maganara ya bayyana, wannan manhaja an kirkire ta ne dan liken asiri ga mutane.

Gaskiyar Magana:

A baya-bayannan kanfanin Google ya kara wata fasaha akan jerin fasahohin da yake anfani dasu, fasahar wadda take da taken: “bayanai akan cutar Corona”, wannan jimla takan bayyana daga mutum ya shiga runbun takaitattun bayanai  a manhajar Google akan wayar sa ko wayarta da Android, yadda hoton shafin ke kasancewa kamar yadda wannan hoto na kasa ke nunawa.

Ba’a samar da sabon runbun takaitattun bayanan dan liken asiri ga mutane ba ko wani abu da ya shafi cutar Corona kamar yadda wassu sakonni da suka bayyana ta kafafen Facebook da Twitter dama WhatsApp suka yayata.

Kanfanin Android ko IOS suna anfani da tsari ne dake bada damar saka manhajoji da yawa akan waya ko na’ura daya. Kamar tsarin da yadda sauran manhajoji da tsare-tasren da suka kan wayoyi da na’urori, abinda kanfanin Apple da Gooogle sukayi shine sabunta tsare-tsaren su dan kyautata yadda wayoyin zasu yi anfani da kuma barin sauran manhajoji suyi aiki idan kowane mai waya ya dora akan wayar sa ko wayar ta.

Kamar yadda jadawalin kirikirar manhajar da kanfoanonin Apple da Google din ta zaiyana, mutane suna da zabin dora manhajar akan wayoyin su tare da damar amincewa ko rashin amincewa da dora manhajoji a wayoyinsu, kamar dai yadda dora sauran manhajoji yake daga runbun manhajoji na app store.

Sabon runbun bada sanarwa ko bayanai game da cutar Corona din bazai yi aiki a waya har sai ansaka shi a waya kuma kawo yanzu wannan tsari bazai yi aiki a waya ba saboda kirkirar manhajar bai kan kama ba, dan batun saka shi a waya ma bai taso ba.

Bayanan da masa tantance sahihancin labarai na CDD ke dasu kawo yanzu sun nuna cewa gwamnatin Najeriya bata sanar da samar da manhajar bin diddigin bullar cutar Corona ba.

Babban lura da sashin dake kula da jita-jita na cibiyar dakile yadiwar cutuka ta kasa NCDC, Abiola Egwuenu yace cibiyar bata da manhajar bin diddigi.

Egwuenu ta kara da cewa manhajar kawai da cibiyar ke anfani da ita itace ta gano bulla da alkintawa tare da bada sharfi akan annoba da aka yiwa lakabi da SORMAS a turance.

Egwuenu tace wannan manhaja da suke anfani da ita manhaja ce data shafi bangare lafiya dake anfani a wayoyin hannu wadda kuma take tallafawa wajen gano bullar annoba kai tsaye ta hanyar hange a fasahar zamani da dakuna gawje-gwajen lafiya.

Ta ci gaba da cewa bayanan da wannan mahaja ke tattarawa ana samun su ne ta hanyar jami’an gwamnati a matakin jaha da kananan hukumomi wadanda aka basu damar yin anfani da ita manhajar.

Kammalawa:

Kanfanonin Google da Apple basu sakawa wayoyin mutane wani tsari dazai rika tattara bayanai game cutar Corona ba. Abinda kawai sukayi shine fadada yadda jadawalin yadda tsarin su ke aiki dan bada dama ga manhaja tayi aiki wanda kuma hakan ke nufin kowane mutum na iya saukar da manhaja da kowa ne runbun manhajojin da yake anfani dashi.

Idan mutum ya saukar da manhaja wadda hukumomin lafiya suka samar, kamar a Najeriya hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC da ma’aikatar lafiya ta tarayya, za’a bukaci izininka ta fuskoki daban-daban dan baiwa manhajar damar yin aiki yadda ya kamata.

#AdainaYadaLabaranBogi

Leave a Comment

Your email address will not be published.