Shin Jami’a Bayero Ta Fitar Da Sanarwar Dakatar Da Dalibai Masu Son Shiga Jami’ar a Zangon Karatu Na Shekara ta 2020/2021?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Wata takarda dake dauke da gargadin dalibai masu neman shiga Jami’ar Bayero a zangoon karatu na shekara ta 2020/2021 wadda masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sukaci karo da ita ta bayyana cewa daliban suyi hankali dangane da shiga tantancewar dazata gudana ta yanar gizo, sanarwar ta kara da cewa Jami’ar Bayero bata gudanar da kowace irin tantancewa a wannan lokacin dan haka mutane su guji shiga tantancewar da ake yayatawa cewa tana gudana a yanar gizo. Sanarwar ta shafi masu neman shiga jami’ar ne a matakin aji daya da aji biyu wato DEda kuma UTME.

Wani bangare na sanarwar da ta bayyana a yanar gizo yace: “Jami’ar Bayero ta gano wata sanarwa  dake zagayawa  tana cewa anfara gudanar da tantance dalibai dan shiga zangon karatu na shekara ta 2020/2021, wannan sanarwa ba gaskiya bace”.

Sanarwar ta cigaba da cewa “Jami’ar Bayero zata sanar idan za’a fara tantancewar ta sahihan hanyoyi irinsu shafin yanar gizo na jami’ar da kasidar mako-mako da ake bugawa a jami’ar  da gidan rediyo da shafukan jaridu”

“Duk wanda ya biya kudi dan yin wannan tantancewa a kowane asusun ajiya na banki ya sani yayi hakane a bisa kasada”

Har wayau, wani ikirari da CDD ta gani a dandalin Twitter game da tantancewa dan neman shiga Jami’ar Bayeron yaga wani mai suna Godson wanda ya bada wannan 09062137223 lambar cewa a tuntubeshi game da tantance daliban.

Gaskiyar Magana:

Takardar da ake yadawa a dandalin sada zumunta na zamani dake ikirarin cewa Jami’ar Bayero ce ta fitar da ita kuma tana gargadin dalibai dangane da shiga tantancewa dan samun izinin karatu a zangon karatu na shekara ta 2020/2021 karya ne.

Ba kamar yadda sanarwar ta bayyana ba, Jami’ar Bayero ta sanar da fara tantance daliban dake neman shiga Jami’ar a zangon karatu na 2020/2021 a ranar 3 ga watan Agustan shekara ta 2020 kuma an wallafa sanarwar a jaridar Daily Trust.

Binciken CDD ya gano cewa kodayake an yada sanarwar sosai dandalin WhatsApp and Twitter, sanarwar karya ce!

Binciken da CDD din ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Bayero bata wallafa suna ko lambar wani mai Godson bad an a tuntubeshi game da tantancewar da ake gudanarwa a halin yanzu.

Da take jawabi game da sanarwar, darakta mai kula kula harkokin jarabawa da daukar dalibai ta Jami’ar Bayero, Hajiya Amina Umar tace BUK bata fitar da kowace sanarwa ba da take gargadin dalibai daga yin tantancewar yanar gizon.

Amina Umar ta kara da cewa: “sanarwar da ake yadawa musamman a yanar gizo dake cewa BUK bata fara gudanar da tantance dalibai masu neman izinin karatu a zangon karatu na shekara ta 2020/2021 ba karya ce”.

“domin samun gamsassun bayanai game da Jami’ar ko daukar dalibai ko gudanar da jarabawa, mutane su duba shafin yanar gizon jami’ar Bayeron”, inji Amina.

Amina Umar ta cigaba da cewa: “Jami’ar Bayero bata wakilta wani mutum ba ko ta bada lambar waya ba bugawa a nemi karin bayani kuma wani mutum da ya bada lambar wayarsa dan a tuntube shi game da tantancewar yanar gizon ba ma’aikacin jami’ar bane , idan dalibai na neman karin bayani akan kowane lamari sais u ziyarci shafin yanar gizon jami’ar”.

Kammalawa:

Jami’ar Bayero dake Kano bata fitar da sanarwar dake gargadin dalibai masu neman shiga Jami’ar a zangon karatu na shekara ta 2020/2021 game da shiga tantancewar yanar gizo ba.

Sanarwar dake yawo a yanar gizo cewa kada daliban su shiga tantancewar bata fito daga Jami’ar Bayeron ba. Hakanan mutumin da ya bada lambarsa ya shafin Twitter cewa a tuntubeshi game da tantancewar ba ma’aikacin Jami’ar bane.

CDD tana jan hankalin dalibai da sauran jama’a da suyi watsi da sanarwar tare da tantance duk labari ko sakon da sukaci karo dashi.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.