Shin Hukumar Zabe Ta Kasa INEC Zata Koma Hannun Shugaban Rikon Kwarya?

Gaskiyar Magana: Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, wani zauren yanar gizo mai suna ejegist ya wallafa wani labari dake cewa shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu zai mika jagorancin hukumar ga hannun wani shugaban wanda zai riketa a matsayin rikon kwarya a ranar 9 ga watan Nuwanba.

Labarin wanda ya bayyana madogararsa ga jaridar Daily Trust yace Mahmood Yakubu zai mika shugabancin hukumar ne ga hannun daya daga cikin kwamishinonin hukumar na kasa.

Gaskiyar Magana:

Labarin da ake yadawa cewa Farfesa Mahmood Yakubu zai mika jagorancin hukumar zuwa ga hannun wani shugaban da zai riketa a matsayin rikon kwarya gaskiya ne.

Kwamishinan hukumar zabe ta kasa INEC, Barr. Festus Okoye ya bayyana wa CDD cewa Farfesa Mahmood Yakubu zai sauka ya mkia shugabancin ga wani har sai majalisar dattawa ta tantance shi dan cigaba da hukucin a karo na biyu.

Okye yace: “bisa doka shigabancin Farfesa Mahmood Yakubu zai kare a ranar Litinin , 9 ga watan Nuwanba, 2020. Yakubu zai mika hukumar ga hannun daya daga cikin kwamishinonin hukumar kafin majalisar dattawa ta tantance shi dan cigaba da jagoranci a karo na biyu”.

Kammalawa:

Labarin cewa shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu zai mika jagorancin hukumar ga hannun shugaban rikon kwarya gaskiya ne!

Farfesa Yakubu zai mika jagorancin hukumar zuwa ga hannun daya daga cikin kwamishinonin hukumar na kasa.

CDD na karfafawa jama’a gwiwa game da tantance game da tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa