Shin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tace Ba’a Iya Daukar Cutar Corona Daga Masu Dauke da Cutar da Alamun Cutar Basu Bayyana Ajikinsu Ba?

Gaskiyar Magana: WHO Bata Fadi Haka Ba!

Tushen Magana:

A ranar Talata, 16 ga watan Yuni, shekara ta 2020, masu tantance sahihanci labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gani wani bidiyo da aka yada sosai a manhajar WhatsApp dake nuna cewa hukuamr lafiya ta duniya WHO tace ba’iya daukan cutar Corona ta hanyar mutanen da alamun cutar basu bayyana ajikinsu ba.

Acikin wani rubutaccen sako da ake yadawa tare da wani bidiyo mai tsawon dakika shida, masu yada bidiyo sunyi ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya WHO tace masu dauke da cutar Corona din da alamu basu bayyana a tattare dasu ba basa bukatar a killace su.

Sakon har wayau ya kara da cewa an kirkiri rudani ne da ya kallafawa mutabne saka takunkumin fuska tare da bada tazara a tsakanin su lokacin mu’amala wanda hakan yakai ga mutane bila-adadin rasa rasa ayyukansu.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa anyi anfani da wani gajeren bidiyo da Maria Van Kerkhove, babbar jami’ar hukumar lafiyar mai lura da annobar cutar Corona tayi jawabi akan cutar Coronar. Acikiin jawabin nata, Maria, tace: “bisa ga bayanan da muke dasu, daukan cutar Corona daga wadanda alamun cutar basu bayyana a jikinsu ba yakanyi wahala”.

Wadanda suka kirkiri labarin bogin game da lamarin sun alakanta zargin nasu ne da bayanin da Maria Van Kerkhove ta gabatar acikin bidiyon inda suka kara da cewa hukumar lafiyar ta yaudari mutane cewa suyi biyayya ga matakan dakilewa da dakatar da yaduwar cutar bayan ta kirkiri rudani a tsakanin mutane.

Biciken kwakwaf da CDD ta aiwatar ya gane cewa ba’a fahimci bayanin Maria Van Kerkhove bane kuma an gurbata shi dan cimma manufar rikita mutane.

A wani rahoto da statnews ta wallafa a ranar 9 ga watan Yuni, Maria Van Kerkhove ta yarda cewa an samu rashin fahimta game da abinda take nufi lokacin da tayi anfani da kalmar “yakanyi wahala” a dauki cutar daga wadanda alamun cutar basu bayyana ajikin suba.

Ta kara da cewa maganar tata ta dogara ne da sakamakon wani bincike da aka gudanar akan wadanda suka kamu da cutar Corona kuma alamun cutar basu bayyana ajikin su da kuma yawan mutanen da suka kamu sakamakon cudanya dasu.

Maria tace bata nufin cewa masu dauke da cutar da alamu basu bayyana ajikinsu da wuya suke iya yadata a duk fadin duniya saboda bincike baikai gano hakan ba.

Jami’ar hukumar lafiya ta duniyar gtace masu dauke da cutar Corona da alamomin cutar basu bayyana ajikinsu ban a iya yada cutar ko suna rashin lafiya ko basayi. Ta kara da cewa saka takunkumin hanci tare da bada tazara yayin mu’amala yana rage yaduwar cutar.

Kammalawa:

Hukumar lafiya ta duniya WHO bata ce masu dauke da cutar Corona da alamun cutar basu bayyana ajikin su ba basa iya yada cutar kuma basa bukatar killacewa. Har wayau WHO bat ace an yaudari mutane ba ta hanyar karfafa musu gwiwa dan saka takunkumin fuska tare da bada tazara yayin mu’amala.

CDD tana kira ga mutane da suyi watsi da sakon tare da daina yadashi. CDD na jan hankalin mutane das u rika tantance gaskiyar labarai kafin yadasu.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.