Shin Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Amince Da Maganin Cutar Corona Da Kasar Madagascar Ta Samar?

Gaskiyar Magana: Karya Ne

Tushen Magana:

A ranar 27 ga watan Mayun shekara ta 2020, masu tantance sahihanicin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sun gano wani labari da wani shafin yanar gizo ya wallafa dake bayyana cewa hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta amince da sinarin da ka iya magance cutar Corona da ake ta cece-kuce akansa da kasar Madagascar ta samar.

Shafin yanar gizon ya wallafa labarin ta hanyar bayyana cewa labari ne da dumi-duminsa, ga abinda jigon labarin yace: “Hukumar lafiya ta duniya ta amince da maganin cutar Corona da kasar Madagascar ta samar”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babban daraktan Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus hukumar lafiyar ta duniya yayi magana ta hanyar wayar tarho da shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina.

A lokacin tattaunawar, Messrs Rajoelina da Tedros sun tattauna hanyoyin da kasar Madagascar din da hukumar lafiyar zasu fadada bincike akan sinadarin da Madagascan da samar dangane magance cutar Corona.

Gwaje-gwaje akan sinadari da ya shafi magani akan aiwatar dasu ne akan kebabbun marasa lafiya dan auna mizanin yiwuwar magance cutar da suke dauke da ita ko akasin haka.

Binciken da CDD ta zurfafa akan lamarin ya gano cewa hukumar lafiya ta duniyar wato WHO ta saka hannu ne kawai akan sidarar yarjejeniyar adana bayani dangane da kirkiran maganin da kuma tantance maganin daga mahangar lafiya a nahiyar Afirka.

Shugaban kasar Madagskan, Andry Rajoelina a wata magana da yayi a shafin Twitter, ya bayyana cewa kasar sa da hukumar lafiyar ta duniya sunyi tattaunawa mai cike da fa’ida.

Ya kara da cewa Tedro ya yabawa kasar sa dangane da kokarin ta wajen dakile cutar Corona.

A lokacin da shugaba Rajoelina da Dr. Tedro sukayi magana a waya basu tattauna batun amincewa da sinadarin magance Corona ba da ake jita-jitar cewa WHO ta amince dashi.

CDD ta gano cewa hukumar lafiya ta duniya bata amince da sinadarin da kasar Madagaskan ta samar ba

Kammalawa:

Hukumar lafiya ta duniya bata amince da sinadarin magance cutar Corona da kasar Madagascar ta samar ba. CDD tana jan hankalin mutane da su rika karanta gundarin labari musamman idan zaurukan yanar gizo ne suka wallafa shi saboda a lokuta da yawa sukan gina jigon labari mai jan hankali domin jawowa shafukan su maziyarta.

Kuna iya turo wa CDD sakonni da labaran da kuke da shakku akansu dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2349062910568 ko ku tuntunbe mu a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica_H.

Leave a Comment

Your email address will not be published.