Shin Hukumar Hisbah a Jahar Kano Ta Hana Pati da Daddare?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 21 ga watan Dismanban shekara ta 2020, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin sun a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da jaridar Kano Focus ta wallafa inda tace hukumar HISBAH ta jahar Kano ta hana party da daddare a fadin jahar Kano.

Labarin yayi ikirarin cewa babban kwamandan hukumar HISBAH, Sheikh Harun Ibn Sina ya bayyana hanin a wanin taron manema labarai da ya gudanar.

A cewar labarin, Sheikh Ibn Sina yace tarurrrukan pati na biki suna cin karo da lokutan sallah kuma hakan yana sanadiyyar rasa sallolin Magriba da Isha da mahalarta patin suke yi.

Har wayau  labarin ya rawaito hukumar HISBAH na cewa daga yanzu dukkanin tarurrukan biki zasu fara ne da safe sannan agama su zuwa karfe 4 na yamma.

Gaskiyar Magana:

Labarin da wata jaridar yanar gizo ta wallafa cewa hukumar HISBAH ta jahar Kano ta hana yin pati da dadddare karya ne! binciken CDD ya gano cewa hukumar HISBAH bata bayyana hanin ba duk kuwa da cewa jaridar ta rawaito.

A martanin sa game da labarin hana pati da daddaren da akace hukumar HISBAH tayi, babban kwaman dan hukumar, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina yace labarin labari ne na bogi dan hukumar babu inda tayi hanin.

Ibn Sina: “wannan labari ne na bogi, abinda ya faru shine, mun kaiwa hukumar yawon bude ido ziyara, toh a lokacin ziyarar, shugaban hukumar yace suna duba yiyuwar samar da dokar hana duk wani shagalin biki da ya wuce karfe 12 ba dare, bayan kamala jawabin sa sai nace hakan yana da kyau, amma abin takaici sai yan jarida suka ce nace HISBAH ta hana pati da daddare”.

“hukumar lura da al’amuran yawon bude ido ce ke kula da otal-otal, da guraren shakatawa da sauran su. Nima kamar yadda kaga labarin haka na ganshi”.

Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina yace hukumar HISBAH ba ta da hurumi ko ikon bada hani akan wannan al’amari.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa hukumar HISBAH ta jahar Kano ta hana pati da daddare a fadin jahar karya ne! Haka nan hukumar bata ce daga yanzu duk shagulgulan biki a fadin jahar ta Kano zasu fara daga safiya kuma a gama su karfe 4 na yamma ba.

CDD tana karfafawa mutane gwiwa game da tantance sahihancin labarai kafin yada su. Kuna iya aikowa CDD labarai na tantance muku sahihancin su ta hanyar aika gajeren sako ko ta WhatsApp akan wannan lamba: +2349062910568 ko ta shafin Twitter a: @CDDWestAfrica @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabarinBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa