Shin Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Matasa Dubu Hamsin (50,000) Aiki?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu tanatnce sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da ake yadawa cewa hukumar samar da ayyukan yi ta kasa National Directorate of Employment (NDE) tana raba ayyuka da yawan su yakai 50,000 ga matasan Najeriya.

Wani sako mai alaka da wannan labari yace za’a rika baiwa matasa N10,000 a duk sati dan rage radadin da cutar Corona ta haifar.

Nan a kasa sanfurin sakonnnin ne cikin hoto:

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babu wani tsari na dauka matasa dubu hamsin aiki ko basu naira dubu goma duk sati dan rage musu radadin cutar Corona.

CDD ta gano cewayan danfara ne suka tsara labarin dan cutar mutane kuma tsara sakonnin ne ta hanyar yin lafazin day a shafi tallafin kudi da zai ja hankalin jama’a.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa za’a dauki matasa dubu hamsin (50,000) aiki da kuma basu tallafin naira dubu goma (N10,000) kowane sati dan rage musu radadin cutar Corona karya ne.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa