Shin Gwamnatin Tarayya Tana Bada Tallafin Naira 30,000 Ga Yan Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 14 ga watan Yunin shekara ta 2020 Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD ta gano wani sakon da ake yadawa a manhajar WhatsApp dake ikirarin cewa gwamnatin tarayya raba tallafin naira dubu talatin (N30,000) ga dukkan yan Najeriya a matsayin agajin rage radadin annobar cutar Corona.

Sakon yayi ikirarin cewa naira dubu talatin din tallafi ne dan ragewa yan Najeriya radadin annobar da cutar Corona ta haifar kuma mutane zasu tallafin kudin ne daga lokacin da suka cika wani fom da aka samar a yanar gizo.

Gaskiyar Magana:

Kamar ire-iren wadannan hanyoyin da yan danfara yaudaran mutane cewa gwamnati zata bada tallafi da suka gudana a baya, wannan ma daya ne daga cikin dinbi labarun bogi da yan danfara ke yadawa dan cutar mutane.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa wadanda suka kirkiri sakon sunyi ne da nufin tara bayanai masu muhimmanci kamar su lambar asusun ajiya na banki da sauran bayanai dan zambatan jama’a.

Tunda bular cutar Corona a Najeriya yan danfara keta baza ire-iren wadannan sakonni da cutan mutane. Sahihin tsarin tallafawa yan Najeriya shine wanda ma’aikatar jinkai tare da bada dauki a lokutan annoba ke aiwatarwa wanda kuma wannan tallafi ne da ake baiwa masu karamin karfi da bukatar taimako, wannan tallafi kuma naira dubu ashirin ne (N20,000) ake bayarwa ga dukkan mutum.

Kammalawa:

Babu wani tallafin kudi naira dubu talatin (N3,000) da gwamnatin tarayya ke rabawa yan Najeriya. Tsarin tallafin da gwamnatin tarayya ke aiwatar kawai shine wanda ake baiwa masu karamin karfi da bukatar taimako naira dubu ashirin (N20,000) da ma’aikatar jinkai tare da bada dauki a lokutan annoba take aiwatarwa kuma shi ba ta hanyar yanar gizo ake gudanar dashi ba.

CDD tana jan hankalin mutane da guji amincewa da wannan sako dama sauran ire-irensa tare da zurfafa binciken musamman akan labaran dake fitowa daga kafofin sada zumunta na zamani.

Leave a Comment

Your email address will not be published.