Shin Gwamnatin Tarayya Ta Maye Gurbin Katin Dan Kasa Da Wani Katin Na Daban?

Tantancewar CDD: Hakan Ba Gaskiya Bane! 

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan shekara ta 2020, kafafen yada labarai da yawa sun wallafa wani labari dake nuna cewa gwamnatin tarayya ta maye gurbin katin dan kasa da wani kati dake da alaka fasahar zamani. 

Daya daga cikin majoyoyin ya gina jigon labarin sa kamar haka: “gwamnatin tarayya ta canja katin dan kasa da wani katin dake da alaka da fasahar sadarwar zamani”. 

Labarin wanda jaridu irinsu Vanguard, the Sun, Legit.ng da Daily Trust suka wallafa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tayi watsi da katinan yan kasa da aka buga tare da canjasu da tsarin tantance mutane ta hanyar yin anfani da fasahar zamani. 

Labarai da rahotannin sun alakanta kansu da Ministan harkokin cikin gida kuma shugaban kwamitin alkintawa tare da tsara bayanan yan kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola. 

Gaskiyar Magana:

Gwamnatin tarayya bata bayyana cewa tayi watsi da katin dan kasa da ake anfani dashi yanzu ba. 

Wani jawabi da ya fito daga Ministan Harkokin cikin gida ya bayyana cewa kwamitin ya bada shawarar cewa hukumar dake bada katin dan kasa ta tattara bayanin dukkan yan Najeriya. 

Aregbesola ya kara da cewa dukkan ma’aikatun da hukumomin dake tattara bayanai su fara aiki tare da la’akari mallakar katin dan kasa a matsayin abubuwan da ake bukata kafin samun cin gajiyar ayyukan da sukeyi. 

Wani nazari da CDD ta aiwatar ya gano cewa babu inda Minista Aregbesola yace gwamnati tayi watsi da katunan aka riga aka buga. 

Aregbesola yace bayanan da za’a tattara za’a adanasu ne a ma’adanar tara bayanai ta kasa. 

Ministan ya bukaci dakatar da sabuwar rijistar da dukkan ma’aikatu da hukumomi keyi a kasarnan. 

Kwamitin ya bukaci dukkanin kanfanonin sadarwa da yin anfani da lambar tantance yan kasa yayin yimusu rijistar layukan wayoyin su. Wannan umarni ya bukaci fara anfani dashi daga ranar 30 ga watan Yuni shekara ta 2020. 

Domin kara tantance wannan labari, CDD ta tuntubi sakatariyar Ministan Harkokin Cikin Gidan, Mrs. Jane Osuji wadda ya bayyana cewa labarin da jaridun suka wallafa na dauke da rikitarwa. 

Osuji tace, ba haka zancen yake ba, Minista baiyi furucin da jaridun sukace yayi ba, “ban ma san yadda akayi jaridun suka wallafa wannan labari mai dauke jirkita abinda Ministan ya fada ba,” inji Mrs. Osuji. 

Kammalawa:

Ikirari da labaran da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya ta canja katin dan kasa da wani katin na daban labari ne mai rikitarwa da jaridun suka wallafa kuma Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola bai furta hakan ba. 

CDD na jan hankalin jama’a da su rika neman karin bayani akan dukkan abinda suke da shakku akansa daga wuraren da suka kamata. 

You can also forward suspicious messages for verification at +2349062910568 or contact us on twitter @CDDWestAfrica.

#StopFakeNews #StopDisinformation

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.