Shin Gwamnatin Tarayya ta Fitar da Jadawalin Sassauta Dokar Zama a Gida?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Wani sako da aka yada manhajar WhatsApp da ya bayyana gundarin jadawalin sassauta dokar zaman gida aka kuma yadashi sosai a dandalin Facebook and zaurukan yanar gizo yanar gizo yayi ikirarin cewa gwamnatin tarayya zata saukaka dokar zaman gidan a matakai daban-daban.

Sakon ya bayyana cewa za’a aiwatar da sassauta dokar zaman gidan ne a matakai biyar. Sakon ya kara da cewa kowane zango zai kasance ne tsawon makonni uku. Ga yadda jadawalin sassautar dokar zai kasance a cewar wannan sako:

  1. Zango na farko: 1 zuwa 18 ga watan Mayun shekara ta 2020
  2. Zango na biyu: 2 ga watan Yuni zuwa 8 ga Yunin shekara ta 2020
  3. Zango na uku: 3 zuwa 29 ga watan Yunin shekara ta 2020
  4. Zango na hudu: 4 zuwa 20 ga watan Yulin shekara ta 2020
  5. Zango na biyar: 5 zuwa 10 ga watan Agustan shekara ta 2020

Gaskiyar Magana:

Sakon wanda tun farko aka wallafa shi a manhajar WhatsApp an wallafa shi a wani shafin Facebook dake kasar Birtaniya  a ranar 4 ga watan Mayun shekara ta 2020 kuma kawo yanzu an yada wannan sako sau 58,000.

Wannan jadawali da sakon yake dauke dashi jadawali ne da ya shafi kasar Ireland amma ba Najeriya.

Tun farko gwamnatin kasar Ireland ta wallafa jadawalin bude saye da sayarwa a kasar ne a ranar 1 ga watan Mayun shekara ta 2020.

Sakon WhatsApp din ya bayyana cewa jadawalin zaiyi aiki ne a matakai biyar kuma za’a fara a tsakanin 18 ga watan Mayu zuwa 10 watan Agustan shekara ta 2020.

Wani bangaren sakon ya zayyana karara cewa sakon bai shafi Najeriya ba saboda kalmomin da akayi anfani dasi irinsu GAA, rugby, bowling, da bingo ba’a anfani dasu a Najeriya.

Binciken da CDD ta gudanar har wayau ya gano cewa kwamitin kar takwana na shugaban bai fitar kowane jadawali ba.

Kammalawa:

Sakon WhatsApp dake bayyana jadawalin sassauta dokar zama a gida acikin zango biyar bai shafi Najeriya ba, hasalima sakon a fito ne daga kasar Ireland. CDD na jan hankalin mutane da suyi watsi da sakon tare da daina yadashi.

Kuna iya turo wa CDD sakonni da labaran da kuke da shakku akansu dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2349062910568 ko ku tuntunbe mu a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica_H.

Leave a Comment

Your email address will not be published.