Shin Gwamnatin Tarayya Ta Bada Biliyan Dari Ga Kungiyar Miyetti Allah Da Nufin Magance Kashe-Kashe Da Garkuwa Da Mutane?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 24 ga watan Janairun shekara ta 2021, an yada wani bidiyo a shafin Twitter wadda ya janyo cece-kuce da tofa albarkacin baki daga mutane da yawa, bidiyon yayi zargin cewa gwamnatin tarayya bada kudi har naira miliyan dubu dari ga kungiyar Fulani makiyaya ta “Miyetti Allah” dan tsayar matsalar kasha-kashe das ace-sacen mutane da ke faruwa a fadin kasar nan.

Bidiyon wanda rahoto ne da gidan talabijin na Roots TV ya gabatar, mawallafin wata mujalla da ake bugawa a harshen Turanci mai suna “Ovation Magazine” Dele Momodu ya wallafi a shafin sa na Twitter a safiyar ranar Ladin da ta gabata.

Wani mai amfani da shafin Twitter wadda ke da tarin magoya baya, Kelvin Odanz (@MrOdanz) ya sake wallafa wannan bidiyon inda yayi masa take kamar haka: “gwamnatin Najeriya ta bada naira miliyan dubu dari ga makiyaya domin su daina aikata muggan laifuka. Naira miliyan dubu dari ga kungiyar da tayi garkuwa da mutane, ta kashe tare da tagayyara rayuwa. Lallai wannan al’amari yayi kyau”

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu bin diddigin labarai da bayanai dan gano sahihancin su na CDD suka gabatar ya gano cewa bidiyon da Dele Momodu da Mr. Kevin suka wallafa ba bidiyo ne na kwanan nan ba. Hasalima binciken ya gano cewa tun farko gidan talabijin na “Roots TV” ne ya fara wallafi a shafin san a YouTube a ranar 14 ga watan Mayun shekara ta 2019.

Fadar shugaban kasa a lokuta daban-daban ta karyata zargin cewa ta bada naira miliyan dubu dari ga kungiyar Fulani makiyaya dan tsayar da matsalar garkuwa da mutane dake faruwa a kasar nan. Wannan ba shine karon farko da ake yada wannan bidiyo da wannan zargi ba.

A ranar 10 ga watan Mayun shekara ta 2019, an yada irin wannan jita-jita da zargi a kafafen sada zumunta na zamani dama saura kafafen yada labarai da aka sani, wannan al’amari ya janyo a wancan lokaci gwamnatin tarayya ta hannun mai Magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu yayi bayani a gidan talabijin na Channels ranar 10 ga Mayu, 2019 inda ya karyata batu.

Shima da yake amsa tambayoyin manema labarai game da batun a watan Mayun shekara ta 2019, babban sipetan yan sanda na kasa, Mohammed Adamuyace gwamnatin tarayya bata baiwa makiyaya ko kungiyar su naira miliyan dubu dari ba. Rahaton da “Roots TV” wanda shine gidan talabijin din da ya wallafa labarin tun farko ya janyo cece-kucen za’a iya samun sa a dandalin YouTube

A martanin da ta mayar, kungiyar “Miyetti Allah” tace hakika ta neman gwamnatin tarayya ta bata naira miliyan dubu dari a shekarun baya amma ba a karkashin wannan gwamnati mai ci yanzu ta Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Sakataren kungiyar “Miyetti Allah”, Saleh Alhassan ya gayawa jaridar Punch a watan Mayun shekara ta 2019 cewa naira miliyan dubu dari din da kungiyar tasu ta nema ba wai da kowace manufa bane face dan ginawa makiyaya wuraren kiwo dan saukaka musu al’amuran su na kiwo.

Alhassan yace: “lallai wannan zargi na biyan naira biliyan dari ga kungiyar makiyaya mummunan zargi ne. Shin dama gwamnati na bada haka sakaka? Sun taba biyan kudi kamar haka. Ai maganar neman wannan kudi ta naira miliyan dubu dari ta kasance a teburin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan tun shekara ta 2014 a lokacin da yake neman warware rikicin makiyaya da manoma”.

Saleh ya kara da cewa wani bangare na wadaddan kudade gwamnanin jihohi sunyi amfani dashi a karkashin kwamitin da tsohon gwamnan jahar Benue Gabriel Suswam ya jagoranta, “ko a haka ma bana jin kaso mai yawa na kudin ya kai ga makiyaya”

Dalilan da suka janyo aka sake dawo da bidiyon a wannan lokaci

Yanzu ana ci gaba da cacar baka ta hanyar kafafen yada labarai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnan jahar Ondo wanda ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga Fulani su bar jahar ta Ondo. Gwamnan Ondo ya bada wa’adin kwanaki bakwai din ne ga Fulani subar wuraren kiwo da ke dazukan jahar Ondon dan magance matsalar garkuwa da mutane da tayi kamari da kuma ake zargin Fulanin da aikatawa kuma suna buya a cikin dazukan.

Yadda Maganar Miliyan Dubu Dari ta Samo Asali

A shekara ta 2014, gwamnatin tarayya karkashin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta kafa wani kwamiti akan wuraren kiwo a karkashin shugabancin tsohon gwamnan jahar Benue Gabriel Suswam.

Kwamitin ya bada shawarar cewa babban bankin kasa na CBN ya samar da wasu kudade dan taimakawa wajen kirkirar kananan wuraren kiwo na zamani a duk fadin kasa baki daya.

Suswam a lokaci da yake yiwa yan jaridar fadar shugaban kasa bayani a ranar 26 ga watan Oktoban shekara ta 2014 bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta kasa ya bayyana shirin gwamnatin tarayyar.

Haka nan, a watan Satumban shekara ta 2019, gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari ta kara karkade shirin tsohuwar gwamnatin lokacin da rikici tsakanin manoma da makiyaya yayi kamari a arewa ta tsakiya, wannan ya zo ne a lokacin gwamnatin ta karbi tsari na kyautata kiwo na kasa. Wannan shiri na gwamantin tarayya Gwamnan Ebonyi ne, David Umahi ya sanar shi ne ya sanar dashi jim kadan da kamala taron kasa akan tattalin arzikin kasa wanda ya gudana a Abuja.

A cewar Umahi a karkashin tsarin, gwamnatin tarayya za ta samar naira miliyan dubu dari wanda shine kaso 80  yayin da gwamnaotcin jahohi za su bada wurare ko kasa  da yanayi dama sauran kaso 20 dan aiwatar  tsarin da ake yiwa lakabi da “Ruga”.

Wannan shiri na gwamnatin tarayya ya gamu da tazgaro inda ya fuskanci mummunar tsana da kiyayya daga yan Najeriya a kafafen sada zumunta na zamani, wannan ya janyo daga baya gwamnatin ta dakatar da shirin.

Kammalawa:

Wani bidiyo da ake wallafawa tare da yadawa a kafafen sada zumunta na zamani inda ake zargin cewa gwamnatin tarayya ta bada naira miliyan dubu dari ga kungiyar makiyaya ta “Miyetti Allah” bidiyo na karya haka nan yana cike da rudani. Binciken CDD ya gano cewa bidiyon an dauke shi ne shekaru biyu da suka gabata, wannan kuma ya saba da ikirarin da masu wallafawa da yada shi ke yi cewa sabon bidyo ne.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa