Shin Gwamnatin Jahar Oyo Ta Bayyana Cigaba Da Karatu Ga Daliban Aji Shida Da Aji Uku Na Makarantun Sakandaren Jahar?

Gaskiyar Magana: Eh, Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 15 ga watan Yunin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato (CDD) sun gano wani rahoto da aka wallafa a yanar gizo da yayi ikirarin cewa Jahar Oyo ta bayyana bude makarantu a jahar dan bada dama ga daliban aji shida wato SS3 and daliban aji uku wato JSS3 dan shirin jarabawa da zasuyi.

Labarin wanda aka wallafa shi da jigon labari kamar haka: “Jahar Oyo ta bude makarantu ga daliban SS3 da JSS3 a jahar” ya watsu sosai musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa jahar Oyo ta sassauta dokar hana zaman gida domin dakile cutar. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin shekara ta 2020 da Taiwo Adisa, sakataren yada labarai na Gwamna Seyi Makinde na jahar Oyo ya sanyawa hannu tace an dauki matakin ne bayan ganawa da shugaban kwamitin yaki da cutar Corona na jahar yayi da Gwamna Makinde.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, matsayar da aka cimma ta kunshi cigaba da karatu ga daliban aji shida na firamare, daliban aji shida na karamar sakandare (JSS3) da daliban aji shida na babbar sakandare (SS3) a ranar 29 ga watan Yunin da muke ciki.

Sanarwar ta kara da cewa ranar komawa aiki ga dukkan rukunin ma’aikata a sakatariyar jahar itace ranar 22 ga wannan watan yayin da za’a  wuraren ibada zasu gudanar da al’amuransu a tsarin kaso ashirin da biyar (25%) cikin dari (100%).

Adisa yace an yanke hukunci hana taron mutane fiye da ashirin da biyar (25) dan dakile yaduwar cutar Corona a jahar baki daya.

CDD  har wayau ta gano cewa daliban aji shida (SS3) dana JSS3 zasu koma makaranta ne a karshen watan da muke ciki wato Yuni dan cigaba da shirin rubuta jarabawa anan gaba.

Ka’idojin da jahar Oyon take so makarantu su jaddada sun hada da samar da wajen wanke hannu da kuma tabbatar da cewa dukkan dalibai sun saka takunkumin fuska.

Kammalawa:

Masu tantance sahihancin labarai na  CDD bayan gudanar da bincike sun gano cewa kawo ranar da aka ywallafa wannan tantancewa wato (16/06/2020) labarin bude makarantun gaskiya ne.

CDD tana shawartan mutane das u rika karanta gundarin labari musamman wanda zaurukan yanar gizo suka wallafa dan wassu zaurukan kan wallafa labarai masu jan hankali wadanda a wassu lokutan ba sahihan labarai bane.

Leave a Comment

Your email address will not be published.