Shin Gwamnan Kano Ya Cire Kwamishinan Kananan Hukumomi?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 18 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai da bankado labaran karya na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gani wata takarda dake bayyana korar kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na jahar Kano wato Murtala Sule Garo. Takardar an yada ta sosai musamman a kafafen sada zumunta na zamani irinsu Facebook da WhatsApp da Twitter.

Takaradar wadda akayi ikirarin cewa ta fito ne daga ofishin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tana dauke da 18 ga watan Agusta a matsayin ranar da salami kwamishinan daga aiki tana dauke das aka hannu da akace na mai baiwa Gwamna Ganduje Shawara ne a fannin yada labarai wato Salihu Tank Yakasai.

Wani bangare na takardar yayi bayani kamara haka: “Mai girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje  ya sallami kwamishinan kananan hukumomi da la’amuran masarautu na jahar Kano Hon. Murtala Sule Garo daga matasyin sa na kwamishina. Wannan kora ta fara aiki ne daga yau 18ga watan Agustan shekara ta 2020. Ana umartan kwamishinan ya mika ragamar gudanar da al’amuran ma’aikatar da kwamishinan din-din-din na ma’aikatar”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babu wata sahihiyar sanarwa ko takarda da ta fito daga gwamnatin jahar Kano dake bayyana korar kwamishinan kananan hukumomin, Hon. Murtala Sule Garo.

Lokacin da aka tuntube shi game da cire kwamishinan kananan hukumomin, mai gwamnan Ganduje shawara akan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai yace labarin cire kwamishinan da abinda takardar take fada karya ne!

Salihu yace: “ban rattaba hannu akan sallamar kowane kwamishina da aiki ba, dan haka takardar da ake yadawa cewa an cire Murtala Sule Garo daga matsayin san a kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu takarda ce ta bogi”.

Tanko Yakasai ya kara da cewa takardar da ake yadawan tana dauke da kura-kurai masu tarin yawan gaskek kura-kuren sun hada: “takardar ba itace takardar ofishin gwamna ke anfani da ita ba, adireshin dake jikin takardar adireshin ofishin sakataren gwamnati ne ba na ofihsin gwamna ba, mukamin kwamishinan ma ba’a rubuta shi daidai ba, hakanan mukamina ma ba’a rubuta shi daidai ba”.

“ni mai baiwa gwamna shawara ne akan harkokin yada labarai ba mai taimakawa gwamna na musamman akan yada labarai ba”, in Salihu Tanko Yakasai.

Yakasai ya kara da cewa har yanzu Murtala Sule Garo ne kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu.

Kammalawa:

Takardar da ake yadawa musamman a kafafen yada labarai cewa an sauke kwamishinan kananan hukumomin da harkokin masarautu na jahar Kano, Hon. Murtala Sule Garo daga mukamin sa karya ne.

CDD na jan hanakalin mutane daga kirkira dama yada labarai na bogi. Har wayau CDD na shawartan jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Kuna iya aikowa CDD labarai dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2348062910568 ko ta shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.