Shin Gwamna Zulum Ya Nada Aisha Bakari Gombi a Matsayin Mai Taimaka Masa ta Fannin Yaki Da Yan Boko Haram?

Tantancewar CDD: Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 19 ga watan Disamban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da majiyoyi da kafafen yada labarai da yawa suka wallafa, labarin yace, Gwamna Babagana Umara Zuum na Jahar Borno ya nada sananniyar yar farautar nan yar asalin jahar Adamawa, wato Aisha Bakari Gombi a matsayin mai taimaka masa ta musamman a fannin yaki day an kungiyar Boko Haram.

Majiyoyin da suka wallafa labarin sun hada da: Premium Times, AljazirahNews, JTV, The Niche NG da sauran wassu kafafen sana zumunta na zamani.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar game da nadin sananniyar yar farautar a matsayin mataimakiya ta musamman ga Gwamna Zulum gaskiya ne.

Takardar nadin Aishan da sakataren din-din-din game da harkar gudanarwa da al’amuran yau da kullum, Danjuma Ali ya sanyawa hannu tace Gwamna Zulum ya amince da nadin jarumar.

Wani sashi na takardar nadin Aishan yace: “an nada ki ne bisa cancanta da kwarewarki dama sadukarwarki ga ayyukan al’umma”.

“muna fata zaki nuna sadaukarwa da jajircewa wajen aiwatar da aikin ki tare da bada gudummawa ga gwamnati dan cimma manufofin ta”.

Da CDD ta tuntunbe ta game da nadin nata, Aisha Bakari Gombi ta tabbatar da cewa Gwamna Zulum ya bata mukamin mai taimaka masa a fanni yaki da Boko Haram.

Aisha tace: “eh hakane, Gwamna Zulum ya nada ni mataimakiya ta musamman a fannin yaki da yan kungiyar Boko Haram, nan gaba za’a saka ranar da zan karbi takardar kama aiki a hukumance”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nada sananniyar yar farautar nan, Aisha Bakari Gombi a matsayin mai taimaka masa a fannin yaki da yan Boko Haram gaskiya ne!

CDD tana karfafawa mutane gwiwa game da tantance sahihancin labarai kafin yada su. Kuna iya aikowa CDD labarai na tantance muku sahihancin su ta hanyar aika gajeren sako ko ta WhatsApp akan wannan lamba: +2349062910568 ko ta shafin Twitter a: @CDDWestAfrica @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabarinBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa