Shin Gwamna Yahaya Bello Yace Cutar Corona Karya Ne Kuma Ana Anfani da Itane Kawai Dan Jefa Fargaba a Zukatan Mutane?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

A ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyra Bunkasa Demokadiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani shafin yanar gizo mai Observers Times wanda ya wallafa wani labari daya rawaito gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello yana cewa cutar Corona karya ce.

Shafin na Observer Times ya wallafa wani labari mai jigon: “Cutar Corona Karya ce, wassu mutane ke anfani da ita firgita mutane, kuma mutuwar Ajanah mutuwa ce ta karar kwana, inji Yahaya Bello”.

Acikin labarin har wayau anyi ikirarin cewa Yahaya Bello yace babu cutar Corona a jahar Kogi.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya nuna cewa cutar Corona gaskiya ne kuma tana cigaba da yaduwa a Najeriya.

Har wayau binciken CDD ya gano cewa, da yake jawabi a waje sadakar uku ta rasuwa babban jojin jaha Kogi, Mai Shari’a Ajanah, Gwamna Yahaya Bello yace Mai Shari’a Ajanah ya mutu ne mutuwa ta karar kwana amma ba wata jinya ba.

Babu wata shida da ta nuna cewa Yahaya Bello ya furta kalaman da ake dangantawa dashi, kodayake yace wassu mutane na anfani da wannan yanayi da ake ciki na annobar cutar Corona dan haifar zaman dar-dar.

“babu abinda yake kisa kamar fargaba, bai kamata mutane su rika daukan duk abinda sukaji ba, cutar Corona da aka samar da ita dan haifar da tsoro, hakanan munfarta ne rage yawan mutane da tsawon rayuwar su”, inji Gwamna Yahaya Bello.

Bello ya cigaba da cewa ko kwararru a fannin lafiya sun yarda ko a’a, cutar da aka samar da ita dan rage yawan al’umma kuma aka kakaba ta wa yan Najeriya ala tilas.

Yahaya Bello ya shawarci yan Najeriya da suyi watsi da rade-radin da akeyi cewa Babban Mai Shari’a na jahar Kogin ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona inda ya kara tabbatar da cewa babu mai cutar Corona a jahar sa ta Kogi.

Idan za’a iya tunawa dai tun bullar cutar Corona a ranar 27 ga watan Fabrairun wannan shekarar hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta cigaba da ganowa da tattara bayanan bullar cutar.

Hakanan za’a iya tunawa cewa fitattatun yan Najeriya sun kamu da wannan cuta irinsu Gwamna Nasir El-rufai na jahar Kaduna, da takwaransa Seyi Makinde na jahar Oyo dama marigayi Malam Abba Kyari wanda cutar ta hallaka.

Yana da kyau asani cewa kawo ranar 2 ga watan Yulin wannan shekarar, hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC  tana da kiyasin mutane 26,484 masu dauke da wannan cuta, daga cikin wannan adadi, 4 daga cikin su a jahar Kogi suke.

Hakanan kasashe irinsu Amurka da Brazil da Russia dama India suna ta fadi tashi ganin sun magance wannan cuta.

Kammalawa:

Binciken CDD ya tabbatar da cewa cutar Corona gaskiya ce. Zargin shafin yanar gizo na Observer Times yayi cewa Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi yace babu cutar Corona karya ne kuma jigon labarin yana da rikitarwa.

CDD tana jan hankalin mutane das u rika karanta gundarin labari musamman wadanda zaurukan yanar gizo suka wallafa, saboda ire-iren wadannan zaurukan yanar gizo sukan wallafa labarai da nufin jan hankalin mutane dama kara yawan mau ziyartan shafukan su.#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.