Shin Engr. Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) Yabar Kwankwasiyya?

Gaskiya Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 25 ga watan Oktoban shekara ta 2020, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wata jita-jita da aka yada a dandalin Facebook (wadda yanzu aka goge) na cewa dan takara gwamna a jam’iyyar PDP a jahar Kano a zaben 2019 kuma dan tsagin Kwankwasiyya, wato Engr. Abba Kabir Yusuf yabar Kwankwasiyya. Labarin wadda kuma aka yadashi a manhajar WhatsApp yace Abba ya fita daga Kwankwasiyya ne saboda hasashen da yakeyi cewa baza’a bashi tikitin tsayawa takara ba a zaben shekara ta 2023.

Abba Kabir Yusuf makusancin jagoran Kwankwasiyya ne wato Sen. Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon lokaci kuma ya rike mukamin kwamishina a tsohuwar gwamnatin Kwankwaso.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Abba yaji kishin-kishin din cewa jagoran Kwankwasiyya, Sen. Rabiu Kwankwaso zai bada takarar gwamnan Kano ne ga Dr. Abdullahi Baffa Bichi wadda shine tsohon babbabn sakataren hukumar TETFund.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar game da wannan labari ya gano labari ne na karya kuma maras tushe. Mabiya darikar Kwankwasiyya sun tabbatar wa CDD cewa babu kasnhin gaskiya acikin labarin kuma Abba Gida-Gida yana nan a Kwankwasiyya.

Mai magana da yawun dan takarar gwamnan, Sunusi Bature shima ya karya ta labarin inda yace Abba yana nan a Kwankwasiyya.

Bature yace: “ina son na tabbatar muku da cewa wannan labari ba gaskiya bane”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2019, Engr. Abba Kabir Yusuf yabar Kwankwasiyya karya ne!

Abba Gida-Gida yana nan a Kwankwasiyya.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa