Shin Dauda Kahutu Rarara Ya Nemi Gudummawar N1,000 Daga Yan Najeriya Dan Yiwa Shugaba Buhari Waka?

Tantancewar CDD: Gaskiya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 10 ga watan Satunban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani labarai ake yayatawa musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Labarin wanda majiyoyi da shafuka dama daidaikun mutane suka wallafa shi ya bayyana cewa, Dauda Kahutu Rarara ya bude gidauniyar neman yan Najeriya masoya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari su bada tallafin naira dubu daya (N1000) dan bashi dama ya wake Shugaba Buharin.

Wata jarida da ake wallafawa a yanar gizo mai suna Kainuwa24 ta rawaito a shafin ta na Facebook cewa mawakin ya bukaci yan Najeriya da suyi masa karo-karon N1000 dai-dai dan ya gwangwaje su da wata sabuwar waka ta yaban Shugaba Buhari.

Har wayau gidan rediyon Express Radio dake Kano shima ya wallafa labarin neman tallafin yan Najeriyan da Rarara yayi dan yiwa Buhari waka. Kari akan haka shine wani labari mai taken Rarara ya daina yiwa Buhari waka da sashin Hausa na rediyon Faransa ya wallafa a shafin sa. Wannan jigon labari ya yadu sosai musamman a yanar gizo inda mutane keta cece-kuce cewa mawakin ya daina yiwa Buhari waka.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa sanannen mawakin, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya sanar neman gudummawar naira dubu dayan (N1,000) ne daga masoya Shugaba Buhari dan rera musu wata sabuwar waka inda zaiyi bayani akan ayyuka da nasarorin da Buharin ya cimma tare da aiwatarwa a jahohi daban-daban, kuma wadannan ayyuka yawansu yakai 192.

Wakar wanda aka yimata suna Kainuwa za’a saketa ne nan gaba.

Da yake yiwa CDD Karin bayani akan batun, sakataren Rarara Multimedia Company, Aminu Yusuf Afandaj yace: “Rarara yana son magoya bayan Shugaba Buhari su bada gudummawar naira dubu-dubu saboda ya samu damar rera waka ga Buharin. Rarara baya bukatar kowane mai rike da mukamin siyasa ko mai hamshakin mai kudi ya biya kudin wakar, abinda yake so shine yan Najeriya masu kaunar Buhari su biya kudin wakar”.

Afandaj ya cigabad cewa: “anfara karbar wannan tallafi daga masoya Buhari kuma wannan gidauniya zata cigaba har nan da sati uku masu zuwa”.

Dangane da cewa Rarara zai daina yiwa Buhari waka kamar yadda wassu kafafen yada labarai suka rawaito, Afandaj yace: “me zaisa Rarara ya bukaci yan Najeriya su bada gudummawar naira dubu da-dai idan dan yiwa Buhari  idan ya daina masa waka? Inaso na tabbatar wa jama’a cewa har yanzu Rarara yana yiwa Buhari waka kuma wakar sa ga Shugaba Buharin mai suna Kainuwa tana nan tafe”.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa Dauda Kahutu Rarara ya bukaci yan Najeriya su bashi naira dubu dai-dai dan yayiwa Shugaba Muhammadu Buhari waka gaskiya ne!

Sai dai wani labarin kuma da shima ake yadawa musamman a kafafen yada labarai cewa Rarara ya daina yiwa Buhari waka karya ne!

CDD tana jan hankalin mutane da su guji kirkira dama yada labaran bogi. Har wayau CDD na kiran jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Zaku iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu domin tantance muku sahihancin su. Kuna iya aikowa ta wannan lamba +2349062910568 ko ta adireshin mu na Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa