Shin Da Gaske Ne Za’a Gudanar Da Jarabawa Ta Hanyar Yanar Gizo Ga Wadanda Suka Shiga Tsarin N-Power Agro?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba wato (CDD) suka gano wani sako da ake bazawa ta manhajar WhatsApp inda ake sanar da wadanda suka nemi shiga tsarin N-Power Agro game da wata jarabawa da za’a gudanar musu ta yanar gizo.

Kamar yadda sakon ya bayyana, an aikawa dukkan wadan da sukayi nasarar shiga cikin tsarin na N-Power Agro. Sakon ya kara da karfafawa wadanda suka shiga cikin tsarin da su duba imel dinsu dan samun adireshin yanar gizon da zasuyi anfani dashi dan yin jarabawar.

Sakon wanda aka yadashi sosai ta manhajar WhatsApp yayiwa mutane jawabi kamar haka: “ku taimaka ku gayawa wadanda suka nemi shiga cikin tsarin N-Power Agro na Ma’aikatar Noma da Raya Karkara da su gaggauta duba imel dinsu dan samun bayani game da jarabawa da za’a yimusu kuma wannan jarabawa zata dauki tsawon minti 15 , ku yada wannan sako dan yakai ga wadan da abun ya shafa”.

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu tantance sahihancin labarai na CDD suka gudanar ya gano cewa babu wata sanarwa ko sako da gwamnatin tarayya ta bayar game da yiwa wadanda suka shiga cikin tsarin N-Power wata jarabawa ta hanyar yanar gizo. Hakanan shafin yanar gizo N-Power ko kafafen sada zumunta na N-Power duk basu bada wata sanarwa ko sako mai kama da haka ba.

Fake News Alert! 5 Steps to Verify Every Information on CDD Channel

A jawabi da ma’aikatar jinkai da bada dauki ta fitar a ranar 7 ga watan Yulin shekara ta 2020 ya nuna cewa babu wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta bayar game da tsarin na N-Power.

Dan fitar da gaskiyar lamari game da batun, shirin N-Power ya bada ba’asi dan magance jita-jitar da ake yadawa. Har wayau shirin N-Power yaja hankali jama’a da cewa su guji daukan duk wata sanarwa da bata fito daga amintattun kafafen sadarwa da shirin N-Power yake anfani dasu ba.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa za’a gudanar da jarabawa ta yanar gizo ga mutanen da suka shiga cikin shirn N-Power Agro karya ne.  Ma’aikatar jinkai da bada dauki ta gargadi mutane da cewa su guji daukan duk wani labari game da shirin N-Power da bai fito daga sahihiyar majiya ba.

CDD tana jan hankali jama’a da su rika tantance sahihancin labari kafin yadashi tare da daina kirkira ko yada labaran karya.

Kuna iya turowa CDD labaran da kuke da tantama akansu dan tantancewa ta wannan lambar: +2349062910568 ko shafin mu na twitter: @CCDWestAfrica, @CDDWestAfrica_H

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.