Shin Da Gaske Ne Idan Ka Saka Jarin Dubu Ashirin Da Biyar Take Zaka Samu Dubu Hamsin a Wani Tsari Na Yanar Gizo?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 17 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba sun hango wani sako dake yawo a dandalin Facebook  dake cewa idan mutum ya saka jarin naira dubu ashirin da biyar a wani tsari na yanar gizo take zai samu naira dubu hamsin.

Sakon yace tsari ne na saka jari dake baiwa mutane ribar kaso dari na abinda suka saka kuma ribar su zata same su a kasa da awa daya.

Sakon ya cigaba da cewa mutum zai iya saka hannun jari na duk yawan kudin da yake so kuma ya samu riba da kaso dari na abinda ya saka cikin minti arba’in da biyar.

Wani bangare na sakon yace: “yanzun nan na samu naira dubu hamsin bayan na saka hannun jarin naira dubu ashirin da biyar, wannan yasa nake ganin ya kamata na fadawa mutane dan su anfana, ga adireshin tsarin saka hannun jarin kamar haka: https://chat.whatsapp.com/Gnk0hbzwbd4GNdMAINjjQX  kuma iya kiran mai kula tsarin saka hannun jarin a wannan lamba dan samun karin bayani (09037026019)

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudabar ya gano cewa, tsarin saka hannun jarin tsari ne na yan danfara. Binciken har wayau ya gano cewa babu sahihan dalilai da suka nuna ingancin tsarin hakana lambar da aka bayar dan tuntubar masu gudanar da tsarin ta nuna cewa mai lambar sunan sa Anthony Joshua.

Binciken CDD ya kara gano cewa ana bukatar mutane su bada muhimman bayanai irinsu lambar asusun ajiya da lambar tsaro ta BVN, kuma wannan salo yan danfara ke anfani dashi dan tattara bayanan mutane da zanbatan su.

Da aka tuntubi mai kula da tsarin a manhajar WhatsApp yayi ta matsin lambar cewa a tura masa bayanan asusun ajiya na banki tare da karfafa gwiwa cewa a tura masa kudi.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa cewa idan mutum ya saka jari zai samu riba da kaso dari na abinda ya saka karya ne! Tsarin da a turance ake kira Winners Pay Investment tsari ne na yan danfara.

CDD tana jan hankalin jama’a da su rika taka tsan-tsan wajen yadda da dukkan abinda suka ga ana yadawa tare da zurfafa bincike kafin yarda kafin yadda da dukkan abinda zasu gani.

Ku kiramu akan lamba: +2349062910568 ko ku tuntube mu a shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa

Leave a Comment

Your email address will not be published.