Shin Da Gaske Ne Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Biyan Kowane Dan Najeriya Alawus Din N8500 A Duk Sati?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Maganar:

Wani sako dake cigaba da yaduwa a WhatsApp da Twitter yayi ikirarin cewa gwamnatin tarayya zata baiwa kowane dan Najeriya Naira Dubu Takwas Da Dari Biyar N8500 a kowane mako da nufi tallafin masa a lokacin da yan Najeriya cigaba bin umarnin zama a gida da magance Cutar Coronavirus.

Sakon ya bayyana cewa za’a fara bada wannan tallafi ga Yan Najeriya daga ranar Litinin 23 ga Watan Maris din 2020.

Sakon yana da kamanni da irin sakonnin daya yan danfara ke turawa mutane da bukatar su bada kudi dan sama musu wata dama ko aiki.

Sahihiyar Magana:

Ba tare da bata lokaci ba, masu tantance gaskiya da rashin gaskiyar labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba wato (CDD) suka bi shafin yanar gizon da akayi ikirarin cewa shafi ne da aka samar dashi dan samun tallafin gwamnatin tarayya akan cutar Coronavirus.

Har wayau wannan sako ya bukaci mutane dasu gabatar da bayyanan su ta hanyar yanar gizo kamar suna, adireshi, lambar waya, imel, lambar asusun ajiya na banki dan samun tallafin N8500 din. Bayan bada wadannan bayanai, sai wannan shafi na yanar gizo yakai mutum ga mataki na gabainda za’a bukaci mutum ya dora hoton sa. A yayinda mutum yake cika wannan fom din kafin matakin karshe za’a bukaci mutum ya sanar da akalla wassu mutane goma game da tallafin, wannan kuma wata alama ce a fili cewa ana bukatar wannan sakon marar tushe yakai ga mutane da yawa, kuma manufar haka shine tattara muhimman bayanan mutane.

CDD ta gano cewa duk ma’aikatun gwamnatin tarrayya suna da shafin yanar gizo wanda yake dauke da alamar cewa na  gwamnati ne kuma karshen su yakan dauki kalmomi kamar .gov.ng ko kuma  .gov amma shi wannan shafi baya dauke da daya daga cikin wadannan alamu da muka lissafa, hasali ma muhallinsa wani takaitattacen zaure ne da ake kira blogspot a turance, kuma shi wannan dandali Kanfanin Google ne yake samar dashi kyauta. Wannan yana nufin cewa kowa na iya bude irin wannan shafi ya kuma iya jefa bayanan mutane masu muhimmanci cikin hadari.

Leave a Comment

Your email address will not be published.