Shin Babban Bankin Kasa CBN Da Gwamnatin Tarayya Na Bada Tallafin N650,000 Ga Kowane Najeirya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Talata, 1 ga watan Disamban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wassu sakonni da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da suke bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hannun babban bankin kasa na CBN na bada tallafin kud da yawan su yakai N650,000 da N250,000 ga kowane ga yan Najeriya a matsayin tallafi.

Sakonnin sunce tallafi za’a bada shi ga mutanen dake shekaru 18 zuwa sama kuma ana bukatar su da cika wani fom a yanar gizo da sakon ke dauke dashi.

Daya sakon yace ana karfafawa yan Najeriya gwiwa da su cika fom ta hanyar wani adireshin yanar gizo da aka samar dan samun garabasar tallafin N250,000. Sakon ya kara da cewa za’a cigaba da bada tallafin har zuwa ranar 1 ga watan Disamban shekara ta 2020

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babu wani shirin bada tallafin kudi N650,000 da N250,000 da gwamnatin tarayya da babban bankin kasa CBN ke shrin baiwa yan Najeriya. Sakonnin da ake yadawa din aiki ne nay an damfara.

Har wayau CDD ta gano cewa bayan mutane sun shiga adireshin da akace shine na samun tallafin sai a bukaci su dakata su gayawa wassu mutanen game da bada tallafin da kuma gabatar da wassu bayanai da suka shafe su kafin a basu dama su ci gaba da rijistar.

Ajikin fom din yanar gizon day an danfarar suka samar anga hoton maganganun da mutanen da acewar wadda suka samar da fom din kalamai ne na wassu da suka cika fom din kuma suka samu gasmsuwa. Wannan alama ce day an danfara kanyi anfani da ita da cutan jama’a, ga hoton bayanan a kasa kamar yadda za’a iya gani.

A matakin karshe na yin rijistar ana bukatar masu cika fom din das u gayawa mutane 15 a shafin WhatsApp.

Ziyarar da masu tantance sahihancin labarai na CDD suka kai zuwa shafin yanar gizo na CBD sun gano cewa tsarin tallafi guda daya da bankin ke aiwatarwa shine na Nigerian Youth Investment Fund, wani shiri na ma’aikatar matasa da wasanni da hadin gwiwar NIRSAL.

Kammalawa:

Sakonnin da ake yadawa ta manhajar WhatsApp dake cewa babban bankin kasa na CBN da gwamnatin tarayya na bada tallafin N650,000 da N250,000 ga yan Najeriya karya ne. yan danfara ne suka tsara sakonnin dan cutar jama’a.

CDD na jan hankalin mutane da suyi taka-tsantsan game sakonnin da amince dasu.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa